Tuesday, May 12
Shadow

Duk Labarai

Mu muka koya maka siyasa har ka zama abinda ka zama yanzu>>PDP ta mayarwa Kwankwaso martani kan sukar da ya mata

Mu muka koya maka siyasa har ka zama abinda ka zama yanzu>>PDP ta mayarwa Kwankwaso martani kan sukar da ya mata

Duk Labarai
Shugaban riko na Jam'iyyar PDP, Umar Damagum ya bayyana cewa, sune suka gogar da tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso har ya zama abinda ya zama yanzu. Damagun ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da BBChausa. Yace koda duka jam'iyyun hamayya zasu hade ba zasu yi nasarar kwace mulki daga hannun APC ba tare da PDP ba. Kwankwaso a baya ya soki Jam'iyyar PDP inda ya bayyana irin rashin kyautawar da suka masa data sa ya fice daga cikin Jam'iyyar. Saidai Damagun yace duk da kalubalen da Jam'iyyar ta PDP ke fuskanta amma har yanzu tana nan da kwarjininta.
Kalli Bidiyon Zainab, Diyar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero na gararamba a titin Legas karfe dayan dare

Kalli Bidiyon Zainab, Diyar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero na gararamba a titin Legas karfe dayan dare

Duk Labarai
Wannan Zainab ce wadda kusan duk masu bibiyar kafafen sada zumunta sun santa. Diyace a wajen marigayi, sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero wadda rayuwarta ke cikin damuwa da rashin tabbas. A sabon bidiyon da ta yi ta bayyana cewa gata karfe dayan dare a Birnin Legas tare da mahaifiyarta da kaninta wanda kuma akanta suka dogara. Tace mahaifinta ya barta ba ilimi ba wani abu da zata iya dogaro dashi, bata da aikin yi. Tace ta gaji bata san yadda zata yi ba, babu wanda ke taimakonta. A baya dai Gwamnatocin Ganduje dana Abba Gida-Gida sun taimaka mata. A wannan karin, Hadimin tsohon shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad yayi kiran da a sake taimakawa Zainab, musamman Gwamnatin jihar Kano. Kalli Bidiyon anan
Za’a kashe Naira Biliyan 4 dan ginawa shugaba Tinubu wajan saukar jirgin sama a Legas

Za’a kashe Naira Biliyan 4 dan ginawa shugaba Tinubu wajan saukar jirgin sama a Legas

Duk Labarai
Ma'aikatar ayyuka ta ware Naira Biliyan 4 dan kashesu wajan ginawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu filin da zai rika sauka da karamin jirginsa. Tuni ma'aikatar ta saka wannan aiki na gina filin saukar jirgin a cikin kasafin kudinta na shekarar 2025. Wasu dai sun soki hakan da cewa bata kudin 'yan kasa ne musamman ganin yanda 'yan Najeriya da dama ke cikin halin ji 'yasu inda ake ganin da an saka kudin a wani fanni da sun taimaka sosai.
Asibitin koyarwa na Jami’ar ABU zai fara yin aikin dashen Koda a shekarar 2025

Asibitin koyarwa na Jami’ar ABU zai fara yin aikin dashen Koda a shekarar 2025

Duk Labarai
Asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello Zaria dake jihar Kaduna zai fara aikin dashen koda ga marasa lafiya. Hakan zai kawowa mutane sauki matuka wajan yin dashen kodar. Daraktan kula da lafiya na jami'ar, Prof. Ahmed Umdagas ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Lahadi, yace tsakanin nan da watan Maris ne za'a fara aikin dashen kodar. Yace mafi yawan kayan aikin da ake bukata suna kasa kuma ma'aikatansu an horas dasu kan yanda zasu gudanar da aikin. Ya kuma bayyana cewa suna kokarin kawo kayan aikin kula da masu cutar daji watau Cancer.
Mun bar gidan kakan mu ba gyarane saboda bamu saci kudi ba, ba zamu iya kula da gidan ba>>Inji Jikan Tsohon Shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari

Mun bar gidan kakan mu ba gyarane saboda bamu saci kudi ba, ba zamu iya kula da gidan ba>>Inji Jikan Tsohon Shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari

Duk Labarai
Jika a wajan tsohon shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari, Bello Shagari ya bayyana cewa sun kasa kula da gidan kakansu, tsohon shugaban kasar ne saboda basu saci kudi ba kuma dalilin haka yasa ba zasu iya kula da gidan ba. Ya bayyana hakane a matsayin martani ga wani dake tambayarsa me yasa suka kasa kula da gidan kakan nasu. Alhaji Shehu Shagari na daya daga cikin tsaffin shuwagabannin da akewa kallon mutanen kirki saboda basu yi sata ba.
Rundunar ‘yansanda a Katsina ta ce ta kashe ‘yanfashi 40 a 2024

Rundunar ‘yansanda a Katsina ta ce ta kashe ‘yanfashi 40 a 2024

Duk Labarai
Kwamashinan 'yansanda na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, Aliyu Musa, ya ce rundunarsu ta kashe 'yanfashin daji 40 daga farko zuwa ƙarshen shekarar 2024. Da yake magana yayin wani taron manema labarai na ƙarshen shekara a birnin Katsina ranar Litinin, kwamashinan ya ce sun kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su 319, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Kazalika a cewarsa, sun kama aƙalla mutum 916 a wannan tsakanin. "Mun samu nasarar ɗaiɗaita gungun miyagu da dama, mun ƙwato makamai, mun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, sannan mun yi nasarar gurfanar da wasu da dama a gaban kotu," in ji shi.