Friday, January 23
Shadow

Duk Labarai

Yanzu-Yanzu: NLC zata ci gaba da yajin aiki gobe bayan zaman sulhu da Gwamnati ya gaza cimma matsaya

Yanzu-Yanzu: NLC zata ci gaba da yajin aiki gobe bayan zaman sulhu da Gwamnati ya gaza cimma matsaya

Siyasa
Rahoton da muke samu na cewa, Kungiyar Kwadago ta NLC zata ci gaba da yajin aikin da ta dauri aniya gobe, Litinin bayan zaman sulhu da gwamnati ya ci tura. A yau lahadi ne dai aka zauna tsakanin wakilan gwamnatin tarayya daga majalisar tarayya da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC dan cimma matsaya kan mafi karancin Albashi, saidai an kare zaman ba tare da cimma matsaya ba. Da misalin karfe 5:50 PM ne dai aka fara zaman inda aka kareshi da misalin karfe 8:45 PM. Kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio bayan taron, ya gayawa manema labarai cewa gwamnati ta roki kungiyoyin kwadagon kan su janye yajin aikin nasu amma suka kiya. Akpabio yace idan aka yi yajin aiki, abubuwa da yawa hadda asibitoci a kasarnan zasu tsaya cik. Duk da haka dai ya sake rokon kungiyoyin kwadagon da ...
‘Gwamnati za ta ci gaba da biyan ma’aikata ƙarin albashin wucin gadi’

‘Gwamnati za ta ci gaba da biyan ma’aikata ƙarin albashin wucin gadi’

Siyasa
Gwmanatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da bai wa ma'aikatan ƙasar ƙarin albashin wucin gadi - da ta fara biya wata shida ta suka gabata - har zuwa lokacin da za a kammala cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar. Cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai ranar Asabar a Abuja, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce wa'adin mafi ƙarancin albashi da aka yi a shekarar 2019 ya ƙare ne ranar, 8 ga watan Afrilun 2024. Sai dai ministan bai bayyana adadin kuɗin da gwamnatin ke biya a matsayin albashin wucin gadin ba, to a baya gwamnatin ta ce za ta riƙa biyan ma'aikatan ƙarin naira 35,000 a kan albashinsu kowane wata har na tsawon wata shida. A ranar juma'a ne dai ƙungiyoyin ƙwadogon ƙasar suka ce za su tsunduma yajin aiki daga gobe Litinin, kasancewar wa'adin ranar 31...

NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na naira biliyan 2.1 a Legas da Fatakwal

Tsaro
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce jami'anta sun samu nasarar kama muggan ƙwayoyin da kuɗinsu ya kai kimanin naira biliyan 2.1 a biranen Legas da Fatakwal Cikin sanarwar nasarar mako-mako da hukumar ke fitarwa ta ce a ranar Juma'a 31 ga watan Mayu, jami'anta tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas suka kama wasu manyan jakankuna maƙare ƙulli 320 na tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 164.50 da aka yi safararta daga Canada. Hukumar ta ce ta kama mutumin da take zargi da safarar tabar - da aka yi ƙiyasin kuɗinta ya kai naira miliyan 960, - mai suna an kama Ughenu Nnaife Francis, wanda ya shaida wa jami'an hukumar cewa naira miliyan shida aka biya shi domin shigar da kayan Najeriya. NDLEA ta ...
NAFDAC ta yi gargaɗi kan amfani da sinadarin Sniper don taskance abinci

NAFDAC ta yi gargaɗi kan amfani da sinadarin Sniper don taskance abinci

Duk Labarai
Hukumar Kula da Inganci da Abinci ta Najeriya, NAFDAC ta gargaɗin 'yan ƙasar dangane da amfani da wani sinadarin adana abinci da ake kira Sniper. Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa shafinta na intanet ta ce tana ankarar da jama'a game da illar amfani da sinadarin wajen kare abinci daga lalacewa. Hukumar ta ce tun a shekarar 2019 aka haramta sayarwa da amfani da sinadarin da ke cikin ƙananan ƙwalabe. Yayin da aka sahalewa sayar da manyan kwabale musamman ga amintattun masu samar da magungunan ƙwari ga manoma. A baya-bayan nan ne dai wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta a ƙasar ya nuna yadda wasu ke amfani da sinadarin wajen adana nau'o'in abinci, kamar kifi da wake da wasunsu. Yayin da take mayar da martani kan bidiyon shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye...
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun kashe Naira Biliyan 8.64 wajan tafiye-tafiye kadai a cikin watanni 3 da suka gabata

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun kashe Naira Biliyan 8.64 wajan tafiye-tafiye kadai a cikin watanni 3 da suka gabata

Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun kashe Naira Biliyan 8.64 wajan tafiye-tafiye a cikin watanni 3 kacal da suka gabata. An gano hakanne ta hanyar Amfani da wata manhaja me suna Govspend da ake amfani da ita wajan bibiyar kudaden da gwamnati ke kashewa. Hakanan an gano cewa an kashe Naira Biliyan 12.59 wajan kula da jiragen da suka yi amfani dasu wajan yin wadannan tafiye-tafiye.
Mutane na cikin wahala da Yunwa a Najeriya>>Obasanjo

Mutane na cikin wahala da Yunwa a Najeriya>>Obasanjo

Siyasa
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, mutane na cikin wahala da yunwa a Najeriya. Ya bayyana hakane a legas wajan wani taro da aka gayyaceshi. Obasanjo yace matsalar tsaro ce ta daidaita kasarnan sannan ya koka da matsalar rashin shugabanci na gari. Yayi kira ga shuwagabannin kasar da su tashi tsaye wajan inganta rayuwar mutane. Yace akwai bukatar canja Shuwagabanni wanda zasu kawo ci gaba irin wanda ake bukata.

Yadda ake fara soyayya

Duk Labarai
A addinance, idan ka ga yarinya, Budurwa kana so, zaka fara zuwa wajan mahaifinta ne ka nemi izini. Idan kuma ba zaka iya zuwa ba kai tsaye, zaka iya aika magabatanka a nemar maka izini idan ba'a bayar da ita ba. Idan ka samu aka maka iso to aiki ya ganka. Anan ne kai kuma aiki ya rage gareka ka samu hanyar da zaka yi nasara soyayyarka ta shiga zuciyarta. Abubuwan da zaka rika yi dan jan hankalinta: Ka rika yin kwalliya sosai idan zaka je wajenta. Ka rika saka turare. Ka wanke baki. Ka rika bata labarin abinda bata sani ba. Ka rika mata kyauta. Ka rika kokarin sata dariya. Ka mayar da ita abokiyarka, ka rika neman shawarar ta. Wannan zai sa ka shiga zuciyarta sosai kuma itama ta ji tana sonka.
Kalli Hoto: Tsohuwar ‘yar kwallon Najeriya da Tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad ya dauki nauyinta zuwa kasar Amurka aka mata aiki ta koma Namiji na neman taimakon Naira Miliyan 69.7 dan a mata karin aikin da zata rika haihuwa

Kalli Hoto: Tsohuwar ‘yar kwallon Najeriya da Tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad ya dauki nauyinta zuwa kasar Amurka aka mata aiki ta koma Namiji na neman taimakon Naira Miliyan 69.7 dan a mata karin aikin da zata rika haihuwa

Duk Labarai
Tsohuwar 'yar kwallon Najeriya, Iyabo Abade wadda yanzu Namiji ce da sunan James Johnson na neman taimakon Naira Miliyan 69.7 dan ta samu ta rika haihuwa. Iyabo ta bugawa Najeriya was a tsakanin 1997 da 2000. Kuma a shekarar 2004 ne aka canja mata halitta a kasar Amurka ta koma Namiji. Tsohon ministan babban birnin tarayya a wancan lokacin, Malam Nasiru El-Rufai ne ya dauki nauyin aikin da aka mata. Saidai kamin kace wani abu, Ita dai Iyabo an haifeta ne a matsayin mata maza, watau tana da azzakari da farji irin na mata. Dan hakane ta zabi daya ko kuma aka duba wanda yafi karkata aka gano Namiji ne kuma aka mata aiki ta koma cikakken Namiji. Saidai tana bukatar a kara mata aiki dan ta samu ta rika haihuwa.