Monday, December 23
Shadow

Duk Labarai

Babu Alamar Abubuwa zasu yi sauki a gwamnatin Tinubu>>Inji Archbishop Nwaobia

Babu Alamar Abubuwa zasu yi sauki a gwamnatin Tinubu>>Inji Archbishop Nwaobia

labaran tinubu ayau, Siyasa
Wani babban malamin Kiristanci Archbishop Nwaobia ya bayyana cewa babu alamar lamura zasu gyaru a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. A hirar da wakilin jaridar sunnewsonline suka yi dashi, ya bayyana cewa faduwar darajar Naira akan Dalar Amurka matsala ce babba wadda ta jefa 'yan Najeriya da yawa cikin halin wahala. Yace kuma gwamnatin Tinubu ta kasa samo hanyar warware wannan matsala. Ya kara da cewa, Sam Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bata da alkibla dan ta kasa dasa tushen ci gaban Najeriya.
Kalli Hotuna: Gidan Mataimakin Shugaban kasar Najeriya ya fi na mataimakin shugaban kasar Amurka kyau

Kalli Hotuna: Gidan Mataimakin Shugaban kasar Najeriya ya fi na mataimakin shugaban kasar Amurka kyau

Duk Labarai
Gidan mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima Wani abin mamaki da ya dauki hankulan 'yan Najeriya shine ganin yanda gidan mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim ya fi na mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris kyau. Gidan na Mataimakin shugaban kasar Najeriya an ginashi ne akan Naira Biliyan 21 duk da cewa akwai wani gidan mataimakin shugaban kasar, a yanzu mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima gidaje biyu gareshi. A yayin da ita kuma mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris gida daya gareta. Gidan mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris. Bayan kashe Naira Biliyan 21 wajan gina sabon gidan na mataimakin shugaban kasar Najeriya da gwamnatin Tinubu ta yi ta kuma kashe Naira Biliyan 2.5 wajan gyara tsohon gidan mataimakin s...
Kalli Hotuna, Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa an kashshe mata sojoji 8 a Gazza

Kalli Hotuna, Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa an kashshe mata sojoji 8 a Gazza

Duk Labarai, Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa, an kashe mata sojoji 8 a Gazza a ci gaba da yakin da take yi da Israela. Kasat ta bayyana sunayensu kamar haka: Sergeant Ez Yeshaya Grover 20Sergeant Or Blomowitz 20Stanislav Kostarev 21Itay Amar 19Eliyahu Moshe 21Eylon Wiss 49Eytan Koplovich 28Wassim Mahmud 23
Bayan da Hadiza Gabon tasa aka kamashi, Rahama Sadau ta sa an sako Zaharaddeen Sani daga wajan ‘yansanda

Bayan da Hadiza Gabon tasa aka kamashi, Rahama Sadau ta sa an sako Zaharaddeen Sani daga wajan ‘yansanda

Duk Labarai, Hadiza Gabon, Kannywood, Rahama Sadau, Zaharaddeen Sani
Rahotanni sun bayyana cewa, Rahama Sadau ta sa an saki Zaharaddeen Sani daga wajan 'yansanda bayan da Hadiza Gabon tun a farko tasa aka kamashi. Yanzu haka dai rahotanni sun ce Zaharaddeen Sani na gida. Tun farko dai Hadiza Gabon ce tace matan da basu shiga fin ba kada su shiga, inda Zaharaddeen ya mata martani me zafi. Da alama, Hadiza Bata ji dadin martanin Abokin sana'arta ba inda tasa aka kamashi.

Maganin bugawar zuciya da sauri

Ciwon Zuciya, Duk Labarai
Bugawar zuciya da sauri na iya faruwa a kowane lokaci kuma abune wanda ke zuwa ya wuce, akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan Maganin bugawar zuciya da sauri. Ga abubuwan dake kawo bugawar zuciya da sauri kamar haka: Motsa jiki. Kishirwa me tsanani. Rashin Lafiya. Shiga halin takura. Me ciki na iya fuskantar hakan. Shaye-shayen miyagun kwayoyi. Shan taba Wasu daga cikin maganin bugawar zuciya da sauri sune: Tashin Hankali:Tayar da hankali na sa bugawar zuciya da sauri, dan haka neman maganin kwanciyar hankali da samun nustuwa zai taimaka magance wannan matsalar. Hanya ta gaba wajan magance matsalar bugawar zuciya da sauri itace a kwanta a kan gadon baya ko kuma ace rigingine sai a rika yin kamar ana tari, a dan rike numfashi sai a sakeshi. Ana k...

Maganin ciwon zuciya na Gargajiya

Ciwon Zuciya, Duk Labarai
Ciwon zuciya wanda yayi tsanani yana bukatar kulawar kwararren likita, saidai idan bai yi tsanani ba, ana iya amfani da magungunan gargajiya wajan maganceta Irin ciwon zuciyar da ake magancewa a gida shine wanda baya faruwa a kullun, watau na dan lokacine, sai kuma damuwa, da daurewar gabobi, sai da yawan gyatsa. Wasu lokutan akwai wahala wajan gane ko banbance kalar ciwon zuciyar da ya kamata a magance a gida da wanda ya kamata aje Asibiti. Idan aka ji wadannan alamu na kasa to a je Asibiti: Ciwin kirji idan ya yi tsanani yana daurewa, yayi nauyi ko yana nusar mutum. Idan mutum ya ji kamar zuciyarsa zata buga. Idan aka ji alamar numfashi na neman daukewa. Idan ba'a ji wadannan alamu na sama ba to za'a iya gwada maganin gargajiya na gida kamar haka: Ana iya samun ts...
Kalli Hoto:An kamata saboda turawa karamar yarinya me shekaru 12 icce cikin al’aura saboda zargin sata

Kalli Hoto:An kamata saboda turawa karamar yarinya me shekaru 12 icce cikin al’aura saboda zargin sata

Duk Labarai
An kama wannan matar me suna Temitope Adetanju 'Yar Kimanin shekaru 25 saboda turawa karamar yarinya me shekaru 12 icce cikin farjinta. An zargi yarinyar ne da satar Biskit na Naira 200 da Milo na 150 sai kayan marmari na Naira 300. Rahoton yace an azabtar da yarinyar sosai saboda wannan zargi. Lamarin ya farune a Isewo, Obada Oko, dake karamar hukumar Ewekoro na jihar Ogun. Kakakin 'yansandan jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace wadda ake zargin ta amsa laifinta amma suna ci gaba da bincike.
Kuma Dai: Kungiyar Kwadago, NLC tace zata iya amincewa idan gwamnati ta biya kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Kuma Dai: Kungiyar Kwadago, NLC tace zata iya amincewa idan gwamnati ta biya kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Siyasa
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa bata nace akan sai gwamnatin tarayya ta biya naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) ba a matsayin mafi karancin Albashi ba. Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa dashi. Yace a shirye suke su amince da kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin (250,00) a matsayin mafi karancin Albashin. Gwamnatin tarayya dai bata bayyana matsayar ta ba kan mafi karancin albashin ba.