An wayi gari da ambaliyar ruwa da ba'a taba ganin irinsa ba a cikin garin Maiduguri. Ruwa ya shafe gidajen mutane a halin da ake ciki yanzu haka.
Ubangiji Allah ka basu mafita na alheri.
Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta buƙaci hukumomin ƙasar su gaggauta sakin shugabanta ba tare da wani sharaɗi ba.
Da safiyar ranar Litinin ne hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kama Mista Ajaero a filin jirgin saman Abuja, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Birtaniya domin halartar taron ƙungiyar kwadago TUC, ta Birtnaiya
Cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ƙungiyar, Benson Upah ya fitar, ya ce ta sanya rassanta na jihohi da manyan ƙungiyoyin da ke ƙawance da ita cikin shirin ko-ta-kwana, kan lamarin da ta kira mai ''tayar da hankali''.
“Ƙungiyarmu ba za ta zuba ido tana ganin ana tozarta shugabanni da mambobinta ba, don haka muke buƙatar a gaggauta sakin Kwamared Ajaero, ba tare da gindaya kowane irin sharaɗi ba'', kamar yadda sanarwar ta ...
Jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan kalaman da sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 ya yi wanda ya yi iƙirarin cewa jam’iyyar PDP ba ta da wani tasiri a siyasar Najeriya, inda ya ce jam’iyyar ta mutu.
A ranar Asabar ne dai Sanata Kwankwaso yayin buɗe ofishin jam'iyyar NNPP na jihar Katsina, jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam'iyyar PDP da APC mai mulki da jefa kanta cikin abin da ya kira ''halaka''.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa Debo Ologunagba ya fitar a ranar Lahadi, PDP ta bayyana Kwankwaso a matsayin "mara muhimmanci a siyasar Najeriya" tare da zargin sa da son kai.
Ologunagba, ya soki kalaman Kwankwaso, inda ya nuna cewa jam’iyyar NNPP a karkashin shugabancin Kwankwaso na ƙoƙarin gina kanta ne a ...
Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai na baya-bayan nan da ke nuna cewa jami'anta sun yi murabus daga aikinsu ne saboda cin hanci da rashawa, da rashin ɗa’a, da kuma rashin walwala.
A makon nan ne dai wasu kafofin watsa labaran Najeriya suka yi ta naƙalto wani rahoto da ke nuna yadda sojoji fiye da guda 1000 suka yi murabus bisa zarge-zargen rashin jin daɗin aiki da rashawa da cin hanci "da ya yi wa aikin katutu".
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana waɗannan iƙirari a matsayin karya da kuma yunƙurin ɓata mata suna da gangan.
A cewar rundunar, rahotannin an yi su ne domin haifar da saɓani da kuma ɓata tarbiyar jami’anta.
Sanarwar ta kara da cewa: "Batun cewa sojoji na yin murabus daga muƙamansu saboda rashin jin dadin rayuwa, da cin...
Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero.
Kungiyar ta NLC ta bayyana a shafin sada zumuntarta na X cewa an kama shugaban nasu ne a yau, Litinin da safe a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Ƙungiyar ta NLC ta ce "har yanzu ana ci gaba da cin zarafin ma'aikatan Najeriya yayin da shugabanmu Joe Ajaero ya shiga hannun jami'an DSS da safiyar yau."
"Jami'an sun kama shi ne akan hanyarsa ta zuwa taron ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Birtaniya."
NLC ta ce yanzu haka ana tsare da shugaban a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro NSA.
A baya dai, shugaban NLC ɗin ya mutunta gayyatar da ƴansanda suka yi masa kan zarginsa da hannu a tallafawa ayyukian ta'addanci, da kuma cin amanar ƙasa
Jagoran jam'iyyar NNPP, mai mulkin jihar kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana takaicinsa kan yadda ya ce gwamnatin tarayya ta raba kayan tallafin shinkafa ga Jihohi 35 duk ta hannun Gwamnonin su, amma ban da Jihar Kano.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Jagoran Kwankwasiyyar ya yi zargin cewa gwamnatin tarayyar ta miƙa kason jihar Kano hannun jiga-jigan jam'iyyar APC, wanda a cewarsa hakan ya saɓa wa dimikraɗiyya.
''Wannan babban cin fuska ne ga dimokradiyya da kuma tsarin mulkin ƙasar mu. Wannan mataki dai nuna ɓangaranci ne da ya wuce gona da iri,'' in ji jagoran jam'iyyar NNPP.
Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasar ya gagguata dakatar da abin da ya kira karan-tsaye wa tsarin dimikraɗiyyar ƙasar.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar NNPP ya kuma nun...
Shugaban 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane, Bello Turji ya nemi mutanen garin Moriki dake jihar Zamfara su biyashi Naira Miliyan 50 a matsayin diyya.
Saidai an yi tattaunawa mutanen sun yadda zasu biyashi Naira Miliyan 30.
Wadannan kudade suna a matsayin diyyar shanun Bello Turji ne da sabon shugaban sojoji na harin Morikin yayi inda Bellon yace idan ba'a biyashi ba zai kai hari garin.
Shahararren dan jarida, Bulama Bukarti ne ya bayyana hakan inda yace shugaban sojojin ya nemi mutane kada su biya kudin amma basu saurareshi ba dan sun san Bello Turji zai iya kai musu hari.
Kowane gida suna biyan Naira 10,000 sai kuma wanda bashi da aure yana biyan Naira dubu 2.
Rahotanni na ta kara fitowa kan dalilin ajiye aikin me magana da yawun shugaban kasa,Ajuri Ngelale.
A ranar Asabar ne dai Ajuri ya ajiye aikin nasa inda ya bayyana dalilan rashin lafiyar danginsa a matsayin abinda yasa ya ajiye aikin.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa fada ne ko rashin jituwa tsakanin Ajuri da wasu na kusa da shugaban kasar yasa ya ajiye aikin.
Hakanan a wani sabon Rahoto na kafar FIJ, suma sun bayyana cewa, rashin jituwa ne tsakanin Ajuri da dayan kakakin shugaban Bayo Onanuga inda kowa kw ganin shine babba a tsakanin su.
Majiyar tace an yi yunkurij sasantasu amma Ajuri yaki yadda a yi musu sulhu wanda haka tasa daga baya aka koreshi daga aiki.
Saidai bayan da aka koreshi daga aikin,ya yi rokon a taimaka masa yayi ritaya da kansa dan idan akace an kore...