Daga Bello Abubakar Babaji
A ranar Litinin ne Hukumar kula da harkokin Zuba hannun-jari ta Ƙasa, NSIA ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta tara Naira biliyan 60 a ɓangaren cire tallafin taki a ƙarƙashin shirin taki na shugaban ƙasa (PFI) cikin shekaru takwas.
Hukumar, wadda tayi nazari kan ayyukan PFI, ta ce hakan wani yunƙuri ne bunƙasa masana’antar takin Nijeriya inda aka samar da masarrafa guda 84 a shiyyoyi shida na Nijeriya.
Ci gaban ya kuma tara Dala miliyan 200 daga hada-hadar cinikayyar ƙasashen wajen wanda hakan ya taimaka wajen samar da ayyuka 100,000.
Hakan nan, shirin PFI ya jagoranci raba buhunan taki mai inganci miliyan 90 ga manoma a Nijeriya.
Darakta Manaja na NSIA, Aminu Umar Sadiq ya yi ƙarin haske game da nasarorin da aka samu ta hanyar shirin waɗanda suk...
Daga Dan Bala
A farkon shekarar 2021 an samu yawaitar jita-jita cewar wai jirage na zuwa su kawowa ƴan bìđìģa màķàmai su kuma ɗauki gwal a asirce (ba wannan ba ne karo na farko da ake samun irin wannan jita-jitar).
Malam Abdulaziz Abdulaziz a matsayin sa na ɗan jarida mai bincike, ya yi tafiya zuwa Zamfara don binciken gani da ido ya kuma kuma tattauna da masana harkokin sauka da tashin jiragen sama (tare da taimakon Mal Hussaini Jibrin).
Binciken ya tabbatar da wannan zancen ƙanzon kurege ne kawai, ya kuma ƙaryata maganar cewa jirgi zai iya shigowa Najeriya ba tare da an gan shi ba.
Na yi sharing wannan labarin ne don na ga ana neman dawo da wannan maganar marar tushe tare da harma ana cewa radar mai ganin jirage sararin samaniya Najeriya ta lalace shekaru biyar da suka wuce!
...
Gwamna Abba ya Gabatar Da Sabon Kasafin Kuɗi Domin Biyan Sabon Albashin Ma'aikata N70,000.
Gwamnatin jihar Kano ta gabatar da ƙarin kasafin kuɗi ga majalisar dokokin jihar. Za kuma a yi amfani da wani bangare na ƙarin kasafin kuɗin ne wajen biyan sabon mafi ƙarancin albashin da aka cimma yarjejeniya a kan sa tsakanin ƙungiyar ƙwadago da gwamnatin Najeriya.
Me zaku ce?
Johan Rupert na ƙasar Afirka ta Kudu ya tsallake Dangote a jerin, inda ya zama mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka
Majiyar mu ta A Yau rahoton da Bloomberg ta fitar na jerin masu kuɗi ya nuna, tattalin arzikin Rupert ya kai Dala Biliyan $14.3 bn, a yayin da Dangote ke da Dala Biliyan $13.4 bn.
Me zaku ce?
A farkon watan Satumba ne shugaba Bola Tinubu zai fara wata ziyara zuwa kasar Sin, da nufin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya da samar da ababen more rayuwa.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa game da ziyarar a ranar Talata.
A cewarsa, shugaban zai kai ziyara zuwa kamfanin Huawei Technologies, da kuma Kamfanin harhada jiragen kasa na CRCC domin kammala aikin titin Ibadan zuwa Abuja na babban layin dogo na Legas zuwa Kano.
Da yake jaddada mahimmancin tafiyar shugaba Tinubu ga ‘yan Nijeriya, Ngelale ya bayyana cewa, jerin ziyarar da shugaban zai yi a birnin Beijing zai haifar da fa’ida cikin gaggawa ga tattalin arzikin Nijeriya da al’ummar kasar baki da...
DA ƊUMI-ƊUMI: Za mu kubutar da dukkanin ƴan Najeriyar da ke hannun masu gârkụwą da mutane, inji shugaban ƴansanda na ƙasa IGP Egbetokun
Wane fata zaku yi musu?
Babban Hafsan Sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya ce rundunar soji ba za ta taɓa amsa kiraye-kirayeɲ da matasan Najeriya da wasu masu ruwa da tsaki da jiga-jigai ke yi mata ba na kawo cikas ga mulkin dimokradiyya a Najeriya ba
Menene ra'ayinku?
RANAR HAUSA TA DUNIYA: Kawo Mana Karin Magana Daya Da Hausa Wadda Ta Fi Burge Ku!
….wannan hotunan matashi Abdulbaki Jari kenan, wanda ya kirkiro Ranar Hausa ta Duniya.
Wace fata za ku yi masa?