Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

YANZU NACI KARO DA WANNAN AIKIN ALKHAIRIN DA JARUMI ADAM A ZANGO YAYI A FACEBOOK. ALLAH YA SAKA MASA DA ALKHAIRI

YANZU NACI KARO DA WANNAN AIKIN ALKHAIRIN DA JARUMI ADAM A ZANGO YAYI A FACEBOOK. ALLAH YA SAKA MASA DA ALKHAIRI

Duk Labarai
YANZU NACI KARO DA WANNAN AIKIN ALKHAIRIN DA JARUMI ADAM A ZANGO YAYI A FACEBOOK. ALLAH YA SAKA MASA DA ALKHAIRI. Idan ubangiji yanason ya albarkace ka sau biyu a lokaci ɗaya, sai ya saukar maka da ruwan sama, sannan ya bijiro maka da Adam A Zango , a matsayin maigida. Wata Ɗalibata ta nemi taimako daga gareni saboda tanada wata damuwa hakan yasa naji tausayinta, Na sanar da maigida Adam a zango Halin da take ciki sai gashi ya turo da 100k abata Adam Zango , ya kyautata mata batare da yasan wacece ba Allah yaƙara baka duk wani arziƙi da ɗaukaka da duk wata ni'ima wadda ka roƙa da wadda baka roƙa ba dan Alfarmar soyayyar da ke tsakanin Manzon Allah [Saw] da Nana faɗima. Amin Allah ubangiji ya cigaba da jan ragamar rayuwarka da harkokinka har zuwa inda baka taɓa zato ba… A...
Hotuna: ‘Yan Bindiga sun kashe babban soja da bai dade da yin aure ba da sauran sojoji 3 a Sokoto

Hotuna: ‘Yan Bindiga sun kashe babban soja da bai dade da yin aure ba da sauran sojoji 3 a Sokoto

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Sokoto sun ce 'yan Bindiga sun kashe babban soja me mukamin Captain tare da wasu sojoji 3. Sojan me suna Ibrahim Yibranii Yohana an kasheshi ne da sauran abokan aikinsa 3 a karamar hukumar Gudu ta jihar Sokoto din. Maharan sun yiwa sojojin kwantan baunane a kan titin Kukurau-Bangi inda kuma suka jikkata sojoji 2 da kona motoci 2 na sojojin.

Ga Bashi daga Gwamnatin Tarayya: Zaka iya neman daga Naira Miliyan 3 zuwa 20

Duk Labarai
Karin Bayani kan bashin da gwamnati tace zata bayar na NYIF. Wakilin hutudole yanzu haka yana bibiyar hira ta musamman da ake gudanarwa da jami'an gwamnati dake kula da wannan tsari na bayar da bashin NYIF. Sunce akwai bashi akwai kuma tallafi wanda ba bashi bane. Sannan sunce daga Naira Miliyan 5 har zuwa Naira Miliyan 20 mutum zai iya nema. Kuma wannan lamari za'a ci gaba da barinshi a bude har zuwa wani lokaci tukuna. Rahoto ya samemu daga majiya me karfi cewa 'yan kudu sun nunka 'yan Arewa sosai wajan neman wannan tallafi da bashi. Jama'a kada a yi wasa dan an nema a baya ba'a samu ba, kada ace ba za'a yi wannan ba, ana sa ran cewa saboda gwamnati bata son a yi zàngà-zàngà zata gaggauta bayar da wannan bashi da tallafi, dan haka a nema a cike. A duba kasa mun ajiye...
Ga Babbar dama ta samun Kudi da Cryptocurrency

Ga Babbar dama ta samun Kudi da Cryptocurrency

Duk Labarai
Da Duminsa: $Dogs sun saki Sabon Update: Sun bayyana cewa daga ranar 14 ga watan Augusta ba za'a kara samun damar tara $dogs din ba. Sannan sunce a wannan ranane zasu bayyana ranar da $dogs zai shiga kasuwa da kuma dukkan sauran bayanan da akw bukata. Sannan sunce ba'a fara sayar da Dogs ba sai bayan TGE. Wanda suka fara a dage cikin kwanaki 3 dinnan da suka rage a kara tara dogs, wanda kuma basu fara ba. Ga link: https://t.me/dogshouse_bot/join?startapp=KcTG8pUqR7StN2se8IJyMg Bayaninmu na farko akan Dogs: Dukkan Alamu sun nuna cewa za'a samu Alheri sosai da $dogs. Nan da kwana 4 zasu bayar da abin mamaki, ko da baka fara Dogs ba idan ka bayar da himma zaka iya tara dogs guda dubu 20 zuwa dubu 30 wanda idan ya shiga kasuwa a farashin da ake tsammani zaka iya samun dala...
Gwamnatin Jihar Kano ta saka dokar hana zirga-zirga na tsawon awanni 24

Gwamnatin Jihar Kano ta saka dokar hana zirga-zirga na tsawon awanni 24

Duk Labarai
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya ayyana dokar a taron manema labarai da ke gudana a gidan gwamnati a halin yanzu. Ya ce an saka dokar ne domin a dakile sace-sace da fashe-fashen kayan gwamnati da na al'umma da wasu ɓatagari ke yi a ƙarƙashin zanga-zanga. Ya ce wasu ƴan siyasa ne da ba sa don ci gaban Kano ke daukar nauyin yan daba wadanda su ka dake da zanga-zanga su ka fara kai hare-hare. Ya kuma umarci jami'an tsaro da su gaggauta fara aiwatar da dokar nan take.