A karo na biyu an sake samun Alhaji dan Najeriya ya tsinci makudan kudade har Yuro €1,750 ya mayarwa mesu
A karo na biyu an sake samun Alhaji dan Najeriya da ya tsinci kudade masu yawa a kasar Saudiyya ya mayar dasu.
Mutumin me suna Muhammad Na’Allah ya fito ne daga karamar hukumar Gumi ta jihar Zamfara kamar yanda hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta bayyanar.
Ya tsinci kudaden ne a Harami wanda suka kai €1,750 kuma ya kaiwa hukumar ta NAHCON dan a mayarwa mesu.
Shugaban hukumar, Malam Jalal Ahmad Arabi ya jinjinawa mahajjacin inda ya bayyana cewa lallai aikin hajjinsa ya koyar dashi darasi me kyau,sannan sunansa na'Allah ba suna bane kawai na'Allahn ne.
A baya ma dai wani Alhaji daga jihar Jigawa, Abba Sa’ad Limawa shima ya tsinci Naira Miliyan 1.6 kuma ya mayarwa meshi kayansa inda ya bayyana cewa, tsoron Allah ne yasashi yin hakan.