Monday, January 13
Shadow

Kara Kiba

Maganin karin duwawu na shafawa

Kara Kiba
Idan kina Bukatar Hips Sannan kuma Mazaunan ki suyi Sutu sutu, Domin Hakan yana Kayatar da Maza. ⇚ Madarar Shanu ⇚ Zuma ⇚ Dan kalin Turawa ⇚ Coconba ⇚ Kayan Marmari. ki samu dankalin turawa ki dafashi ya dahu sosai, idan yasha iski Hadashi da Cocoban dinki sai ki Marka deshi, ki dinga Sha da madarar shanu da Zuma kadan, Zaki Sha na tsawon wata 1. Sannan ki dinga yawan Shan Mayan Marmari.

Maganin hips cikin kwana uku

Kara Kiba
Mata da yawa suna bukatar suga hips dinsu ya ciko tun basuyi aureba saboda yanda yake daukar hankalin da namiji to ballantana amarya Wanda ita tafi cancanta data samu hips domin daukar hankalin oga. kuma yana kara saka namiji yaji ya gamsu da matarsa Kafin kiyi amfani da maganin karin hips Abinda ya kamata kifara sani shine yaya yanayin jikinki yake? Ya dace ki kara hips? Abinda nake nufi shine akwai mace Wanda taketa kiba ita wannan batada matsakar wannan koda yake ana samu wacce kibarta tafi yawa ta sama. Akwai kuma mace wacce take batada kiba amma tanada breast(nono) sosai to irin wadannan zaka samesu basuda wadataccenhips irinsu sune ya kamata surinka kokarin amfanida maganin karin hips amma mace wacce batada nono sosai tun tana budurwa ana samunta da hips itama wannan babu ru...

Maganin kiba da duwawu

Kara Kiba
Karin girman duwawu abune da mata da yawa ke son samu amma ba kowace macece ke samun magani sahihi ba. A wannan bayani zamu bayyana muku sahihan hanyoyi na kara girman duwawu da zaki ga mazaunanki sun yi bulbul. Magani na farko shine ana samun hada Hulba da Man zaitun a rika sha sau 4 a rana, hakan yakan sa mace jikinta yayi bulbul ciki hadda duwawunta. Ana samun Man Hulba da Castro Oil a hada a rika shafawa akan duwawun, insha Allah zaki ga jikinki ya kara girma sosai. Hakanan ana son a rika cin wake, Dankalin Turawa, Fasuliyya da dai sauransu.

Karin kiba da hulba

Kara Kiba
*MAGANIN ƘARIN ƘIBA WANDA BASHI DA ILLAH BAYANI YADDA ZAA KARA KIBA GA MAI BUKATAR WANNAN.•(1)- Domin Karin kiba Za'a samo Zabib,da hulba, Za'a wanke Zabib din sannan azuba shi acikin ruwa Kofi biyu, sai shi yayi awa (16)Sannan Amur tsike shi atace bayan yahade sai kuma azuba hulba cokali (2) idan ruwan yayi kasa Sai akara wani daga nan sai asanya a freeze arufe amma banda marfin Wanda zai rufe kwanon ko robar gamgam. Idan yakara kamar awa (6)Sai atace za'arika shan karamin kofin shayin larabawa ,ko buzaye.•Sai dai yakan sanya kara cin abinci,to ana bukatar arika cin abinci mai kya Wanda yake gina jiki.•(2)-hanya ta biyu:•(1)- Ya yan hulba(2)- alkama(3)- waken suya(4)- gyada(5)- garin dabino(6)- garin farar shinkafa(7)- madara(8)- zumasaiki maida su gari suyi laushi saiki rika diba coka...

Danyen kwai yana kara kiba

Kara Kiba
A kimiyyar Lafiya, danyen Kwai baya kara kiba, maimakon amfani,shan danyen kwai zai iya haifar da matsalar lafiya. Wani abu da ba kowa ya sani ba shine, dafaffen kwai wanda aka tafasa,yafi danyen kwai yawan sinadaran protein. Abinda aka sani game da cin kwai dan kara lafiyar jiki shine a rika cin guda daya ko biyu a kullun. Shan danyen kwai yana da hadarin sanya cutar amai da gudawa, Zazzabi da ciwon gabobi. Dan haka idan neman kiba ake wajan shan danyen kwai a dena. Akwai kayan abinci da yawa da ake amfani dasu dan samun kiba ta hanyar lafiya maimakon shan danyen kwai me hadari. Kayan abinci irin su madarar ruwa, kankana, Ayaba, Madarar Waken Suya, Madarar Kwakwa duk suna sanya a yi kiba, dan karanta cikakken bayani kan abincin dake sanya kiba a karanta Abincin dake rag...

Kunun kara kiba

Kara Kiba
Ana hada kunun karin kiba dan sha a samun kiba musamman ga wadanda suke da rama wadda ta wuce kima. Ga yanda ake hada Kunun kara kiba kamar haka: Ana samun madarar waken suya kofi 1, sai a hadata da ruwan mangwaro da aka matse, sai a samu ayaba daya a saka a markada. A sha sau daya a rana ko kuma gwargwadon yanda ake son yin kiba, cikin sati guda za'a ga mamaki. Ana kuma iya hada Apple, Dabino, Kwakwa, Ayaba, Madara ta ruwa, madara ta gari, Abarba, citta. A yi blending a rika sha akai-akai.

Hanyoyin kara kiba

Kara Kiba
Kara kiba musamman me tsabta ba wadda zata wuce kima ba na da kyau. Saboda rama wadda ta wuce kima na iya zama matsala wadda zata sa ka rasa abubuwan kariya na jiki da zasu iya kaiwa ga raguwar karfin jiki ta yanda zaka rika karyewa cikin sauki. Ga hanyoyin da za'a kara kiba cikin sauki: A kara yawan abincin da ake ci, a rika cin abinci kadan-kadan a lokuta daban-daban a rana. A rika shan madara, madara na taimakawa sosai wajan karin kiba me tsafta. A rika cin kifi da kwai da wake. A rika shan yegot, A ci chakulate a sha ice cream daidai gwarwado. Rika motsa jiki. A rika cin soyayyen dankalin Hausa dana Turawa da kwai. A rika cin naman kaza. A rika cin bindin rago, ko na sa. A rika cin doya, Madarar Kwakwa. Kar a sha ruwa kamin a ci abinci, saboda hakan...