Kaikayin Azzakari
Kaikayin Azzakari na daya daga cikin matsalolin da maza kan yi fama dasu, a wannan bayanin, zamu fadi abubuwan dake kawoshi da kuma maganinshi.
Abubuwan dake kawo kaikayin Azzakari sune:
Infection: Idan ya zamana kana fama da infection akan azzakarinka ko a cikinsa, zaka rika iya yin fama da kaikayin Azzakari.
Ciwon fata ko bushewar fata: Idan ya zamana kana fama da yawan bushewar ko wata cuta a jikin fatarka, zaka iya yin fama da kaikayin Azzakari.
Cutukan da ake dauka a wajan jima'i: Idan ya zamana ka kamu da daya daga cikin cutukan da ake dauka a wajan jima'i zaka iya yin fama da kaikayin Azzakari.
Sabulu da Ake amfani dashi: Kalar sabulun da ake amfani dashi wajan wanka zai iya kawo kaikayin Azzakari.
Aske Gashin Gaba: Aske gashin gaba na daya daga cikin abubuwan dake...