fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Kiwon Lafiya

An dasa wa wani mutum zuciyar alade a Amurka

An dasa wa wani mutum zuciyar alade a Amurka

Kiwon Lafiya, Uncategorized
Likitoci a Amurka sun yi nasarar dasa wa wani mutum zuciyar alade, a irin wannan aiki da ke zaman na farko a duniya, inda mutumin yake murmurewa kwana uku bayan dashen. Likitoci sun bayyana aikin da cewa gagarumin ci gaba ne da kuma nasara, domin ana ganin a karshe zai kai ga ana amfani da hanyar wajen yin amfani da sassan dabbobi domin yi wa mutane dashe. Likitocin da suka jarraba wannan sa'a a asibitin Jami'ar Maryland sun ce zuciyar aladen wadda aka yi wa kwaskwarima ta yadda jikin dan adam zai iya karbarta, tana aiki a jikin mutumin kalau, bayan aikin na tsawon sama da sa'a bakwai. Rahotanni sun baiyana cewa likitocin sun kuma ce zuwa wasu sa'o'i 24 za a iya cire wata na'urar da aka hada wa mutumin da aka yi wa aikin David Bennett, mai shekara 57, da ke taimaka masa. Ai...
Shan maganin ƙarfin maza kan haifar da mutuwar fuju’a>>NAFDAC

Shan maganin ƙarfin maza kan haifar da mutuwar fuju’a>>NAFDAC

Kiwon Lafiya
Hukumar tsabtace Sahihancin Magunguna da Abinci ta Ƙasa, NAFDAC ta ce shan maganin ƙarfin maza kan haifar da mutuwar fuju'a, ma'ana, mutuwar gaggawa. Hukumar ta ƙara da cewa magungunan karfin maza kan haifar da cutar ɓarin jiki inda maza za su riƙa shan su domin su burge matan da su ke saduwa da su. Darakta-Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan gargaɗin a saƙon ta na Kirsimeti da sabuwar shekara. Adeyeye ta nuna rashin jin daɗin ta game da yadda magungunan karfin maza su ka cika kasuwannin magani a faɗin ƙasar nan. A cewar ta, yawancin irin magungunan ma ba su da rijistar NAFDAC ɗin. "Shigo da su a ke yi ta ɓarauniyar hanya. Inda su na da rijista, to masu shigo da shi da masu sayarwa ba za su riƙa yin abin da su ke yi a kasuwanni, ka tuna, kafafen sad...
Dawowar Coronavirus Da Duminsa: Gwamnatin tarayya tace daga yau yawan mutanen da zasu shiga masallaci kada ya wuce kaso 50 cikin 100 na yawan mutanen da masallacin zai dauka

Dawowar Coronavirus Da Duminsa: Gwamnatin tarayya tace daga yau yawan mutanen da zasu shiga masallaci kada ya wuce kaso 50 cikin 100 na yawan mutanen da masallacin zai dauka

Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta dawo da dokar kayyade yawan mutanen da zasu shiga masallaci saboda dawowar annobar Coronavirus gadan-gadan.   Gwamnatin tace duka wajan ibada na Najeriya,  mutanen da zasu shiga ciki, kada su wuce kaso 50 cikin 100 na yawan mutanen da wajan ibadar zai dauka.   Shugaban kwamitin dake kula da yaduwar cutar coronavirus,  Boss Mustapha ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai.   Yacw idan cutar ta ci gaba da yawaita, dole su saka karin dokoki masu tsauri.
Mun aikawa Kano Biliyan 5 ta yaki coronavirus>>Gwamnatin Tarayya

Mun aikawa Kano Biliyan 5 ta yaki coronavirus>>Gwamnatin Tarayya

Kiwon Lafiya
Kwamitin gwamnatin tarayya dake kula da yaki da cutar coronavirus ya bayyana cewa an sake aikawa jihohi kudade dan su yaki cutar coronavirus.   Shugaban kwamitin, Boss Mustapha ne ya bayyana haka a ganawa da manema labarai.   Yace an aikawa jihar Legas Biliyan 10 inda aka aikawa Kano Biliyan 5 sannan kuma an aikawa sauran jihohin Najeriya Biliyan 1 kowacce su yaki coronavirus.
Za’a Kwashe Shekaru 120 Kafin A Sami Wadatar Likitocin Da Ake Nema A Najeriya>>Ministan Ilimi

Za’a Kwashe Shekaru 120 Kafin A Sami Wadatar Likitocin Da Ake Nema A Najeriya>>Ministan Ilimi

Kiwon Lafiya
Minista Adamu Adamu ya bayyana hakan ne a wajen bikin rantsuwar fara karatun digiri karo na farko na jami’ar kimiyyar kiwon lafiya ta tarayya wato FUHSO, da aka gudanar a mazaunin jami’ar na wuccin gadi dake garin Otada na karamar hukumar Otukpo a jihar Binuwai. Adamu ya ce jami’ar ta FUHSO da ke jihar Binuwai za ta cike gibin da ake samu na bukatar likitoci a Najeriya. Ministan wanda ya sami wakilcin babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta tarayya, Sunny Echono, ya ce idan aka yi la'akari da adadin likitocin da ake yayewa a Najeriya a halin yanzu, kasar za ta kwashe kimanin shekaru 120 kafin ta samu adadin likitocin da take bukata a fannin kiwon lafiyarta, amma kuma sai idan likitocin da ke aiki a kasar sun ci gaba da aiki ba tare da fita kasashen waje aiki ba. Haka kuma, Adamu...
Gwamnati tace dole kowane ma’aikaci yayi rigakagin Coronavirus

Gwamnati tace dole kowane ma’aikaci yayi rigakagin Coronavirus

Kiwon Lafiya
Gwamnatin Najeriya za ta hana duk wani ma'aikacin gwamnati da ba a yiwa rigakafin korona ba shiga ofis daga ranar 1 ga watan Disamba. Sakataren Gwamnatin kasar wanda shi ke jagorantar kwamitin Shugaban kasa kan yaki da Korona Boss Mustapha ne ya bada sanarwar, a wani zama da kwamitin yayi a Abuja yau Laraba. Jaridar Daily Trust ta ambato wani bangare na sanarwar na cewa " daga ranar 1 ga watan Disambar 2021, gwamnatin tarayya za ta bukaci ma'aikatanta su nuna shaidar cewa an yi musu allurar rigakafi ko kuma sakamakon da ke nuna cewa ba su dauke da cutar wanda bai wuce awa 72 ba kafin su shiga ofis." A cewar Sakataren Gwamnatin, kididdigar gwaji ta sama da makonni hudu da suka wuce ta nuna cewa yayin da bazuwar cutar ke raguwa a wasu jihohi, tana karuwa ne a wasu jihohin. A wata mai k...
Hotuna: Likitocin da Sanata Aliyu Wamakko ya dauko daga Saudi Arabia sun iso Sakkwato domin yiwa jama’a aikin zuciya kyauta

Hotuna: Likitocin da Sanata Aliyu Wamakko ya dauko daga Saudi Arabia sun iso Sakkwato domin yiwa jama’a aikin zuciya kyauta

Kiwon Lafiya
Likitocin da Sanatan Sakkwato ta tsakiya, Aliyu Magatakarda Wamakko ya gayyato daga kasar Saudi Arabia sun iso a Jihar Sakkwato domin yiwa jama'ar Jihar aikin fida ga masu ciwon zuciya kyauta. Tuni ayarin Likitocin 24 suka isa Asibitin Koyawarwa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato. Likitocin zasu kwashe tsawon mako daya domin yin aikin kyauta ga al'ummar Sakkwato a karkashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko A yau ne ake sa ran Likitocin zasu fara yin wannan aikin ga marasa lafiyan.
Maganin kaikan gaba da kurajen gaba na mata da maza

Maganin kaikan gaba da kurajen gaba na mata da maza

Kiwon Lafiya
Ga mata masu fama da kaikan gaba, ga dama ta yanda za'a iya magance matsalar cikin sauki.   A gida zaki hada maganin da kanki ba tare da kin sayi maganin ba. Kusan kowa zata iya hada wannan magani wanda kuma da yardar Allah za'a samu biyan bukata.   Ga yanda za'a hada maganin kamar haka: MAGANIN 'KAI'KAYIN GABA NA MATA DA 'KURAJE uwar gida zaki sama ruwan zafi ki zuba gishiri kiringa kama ruwa dashi.sannan zaki sami bagaruwa zaki tafasa sannan kiringa kama ruwa da lta wato ruwan yazama akwai dumi alokacin da zakiyi.bayan wannan zaki samu saiwar(bini da zugu)sai kuma saiwar(marke) sai(jar kanwa)ki hada kitafasa ki dinga sha to ln sha allahu zaki samu saukin ciwan mara da kuma kaikayin gaba dama sauran cututtukan da suka damu mata inda ta bangaran nanne kamar yadd...
Matasa biyar sun mutu yayin da suke dauko gawar dan uwansu da ya mutu a sanadiyyar cutar kwalara daga Legas zuwa Sokoto

Matasa biyar sun mutu yayin da suke dauko gawar dan uwansu da ya mutu a sanadiyyar cutar kwalara daga Legas zuwa Sokoto

Kiwon Lafiya
Wasu matasa biyar sun mutu yayin da suke kai gawar dan uwansu wanda ya mutu sakamakon cutar kwalara a jihar Legas zuwa Sokoto. Mamatan yan ci rani ne dake zau ne a jihar Legas inda suke neman abincin su. Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, suna zaune ne a Ojota, yankin da aka ce ya fi fama da cutar kwalara a jihar Legas. Wata majiya ta bayyana cewa; Bayan rasuwar abokin nasu, sun yanke shawarar kawo gawarsa garinsu, Sanyinna a karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto don binne shi. Sun kuma tattauna da wata motar bas dake zuwa Sakkwato kuma a kan hanyarsu mutane biyar sun kamu da cutar kuma sun mutu kafin isowar su. Wasu fasinjoji guda biyar a halin yanzu suna karbar magani a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko ta Sanyinna. Ba a bar motar ta shiga cikin garin ba. Ardon Sanyinna...