Friday, December 13
Shadow

Kwalliya

Wacece mace mai kyau

Auratayya, Budurci, Gaban mace, Jima'i, Kwalliya, Sha'awa, Soyayya
Shi kyau kala biyune Dana zahiri Dana badini. Kyan Zahiri shine Wanda ake gani da ido, watau fuska me kyau, dogon hanci, fari, da sauransu. Mace me Kyan zahiri za'a iya ganinta fara, doguwa, me matsakaitan mazaunai da matsakaitan nonuwa me fararen idanu, da fararen hakora sannan ta iya wanka. Saidai shi Kyan zahiri yana dusashewa musamman Idan girma ya fara kama mace, shiyasa ake son mace ta hada kyau biyu watau na zahiri dana badini. A lokuta da dama, mace zata iya samun kyan badini amma bata dana zahiri, to idan so samune, mace ta hada duka biyun, amma idan ya zama mutum zaba zai yi tsakanin mace me kyan badini bata dana zahiri da kuma me kyan zahiri bata dana badini, to a shawarce mutum ya dauki mace me kyan badini bata dana zahiri yafi. Shi kuma kyan badini, yawanci ba'a...

Hadin man gyaran fata

Kwalliya
Asamu ganyan magarya man zaitun man habbatussaudaAna daka ganyan magarya a zuba cikin man zaitun da man habbatussaudaAnasha shafawa sau 2 a rana shi ma yana gyaranJiki yana kashe cututtukan fataInsha allah. Sabulun gyaran fata,salaushinta dakuma maganin tabo Kisamu sabulun salo,wato ghana soap,kisami madara,leman tsami dakuma kurkur da haska amarya,kisamu sabulun broonze bashida tsada ana saidashi a stores haka saikuyi kokari kunemi sabulun caramel shima duk acikin kayan hadine to kisamu kihada sabulun duka ki daddakasu kokuma ki yanyankasu siri siri saiki gwamutsasu sannan saikikawo kurkur daidai misali ki juye kisamu haska amarya daidai misali shima ki juye.haska amarya da kurkur agidagen gyaran jiki ake samunshi saikihadeshi asabulun kibuge sannan wasu sunasa nescafe do...

Yadda ake hada sabaya

Kwalliya
AMFANIN SABAYA A JIKIN YA"MACE Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Zai Taimaka Wajen Dawo da Halittan Da Allah Yai Mata Jikinta Nonon Bazai Zube Ba. Na Biyu Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Jikinta Zaiyi Laushi Kamar Kwalabiya Na Uku Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Da zarar ta Haihu Irin Ramar Da Mata Keyi Baza Tayi Ba Kuma Ruwan Nononta Zai Qara Yawa Sannan Bazai Lalace Ba Kuma Yaron Data Haifa Allah Zai Kareshi Daga Dangin Cututtuka Sannan Hatta Magidanci Idan Yasha Yana Qara Masa Lafiya Da Kuma Kuzari a Jikinsa Hatta Wajen Kusantar Iyalinsa ABUBUWAN DA AKE BUKATA WAJEN HADA SABAYA SUNE KAMAR HAKA: *Al Kama 1Mudu *Danyen Shinkafa 1Mudu *Waken Suya 1Mudu *Ridi ½Mudu *Hulba ½Mudu *Gyada Mai Bargo/Kamfala *Madara *Zuma YA ZA'A HADASU SHINE: Ridi Da Gy...

Gyaran Gashi

Gyaran Gashi, Kwalliya
Akwai hanyoyi da yawa na gyaran gashi wanda ba ma sai kin sayi mai ba idan kinso. A wannan rubutu, zamu kawo muku abubuwan gyara gashi daban-daban wanda za'a iya hadawa a gida: Man Zaitun: Ana samun man zaitun wanda ba'a hadashi da komai ba, a rika amfani dashi wajan gyaran gashi, man zaitun yana taimakawa sosai wajan kara yawan gashi, hanashi karyewa, sa gashi ya rika sheki da sauransu. Idan gashin kanki ya lalace, ko yana yawan bushewa ko yana kaikai, man zaitun na magance wadannan matsaloli. Ana shafa man zaitun akai, bayan mintuna 30 sai a wanke ko kuma idan anzo kwanciya sai a shafashi, da safe a wanke da ruwan dumi. Man Kwakwa: Bayan Man zaitun, ana kuma amfani da Man Kwakwa wanda ba'a gaurashi da komai ba wajan gyaran Gashi. Shima ana shafashi zuwa mintuna 30 sai a wa...

Maganin pimples da black spot

Gyaran Fuska, Kwalliya
Ana samun maganin pimple da black spot a gida ba tare da amfani da maganin asibiti ba. Hanyoyin magance pimples da black spot sun hada da: Amfani da Aloe Vera: Ana samun ruwa ko man Aloe Vera wanda ba'a hadashi da komai ba a shafa a fuska wanda yana maganin pimples da black spot sosai. Idan ba'a samu na kemis ba, ana iya hadawa a gida ta hanyar yanko ganyen Aloe vera a fere koren bayan a tatso ruwan a rika shafawa a fuska. A lura idan fuska ta nuna alamar reaction, sai a daina amfani dashi a tuntubi likita, idan kuma bata yi ba, sai a ci gaba har fuska ta dawo daidai. Ana iya karanta karin bayani kan amfanin Aloe vera wanda muka rubuta Ana kuma amfani da Man Zaitun wajan magance matsalar pimples da black spot: Ana amfani da man zaitun kai tsaye a shafa a fuska ba tare da ...

Gyaran fuska da man kwakwa

Amfanin Kwakwa, Gyaran Fuska, Kwalliya
Man kwakwa na da amfani da yawa a fuska, yana sa fuska ta yi laushi, yana maganin ciwo yayi saurin warkewa, yana kuma taimakawa wajan rage kumburi. A wannan rubutun, zamu kawo muku amfanin man kwakwa wajan gyaran fuska. Wani bincike ya tabbatar da man kwakwa na taimakawa sosai wajan maganin kurajen fuska da kuma yana a matsayin rigakafi dake hana kurajen fitowa mutum a fuska. Hakanan man kwakwa na taimakawa wajan kawar da alamun tsufa a fuska. Ana shafa man kwakwa a fuska ko jiki kamar yanda akw shafa sauran mai. Hakanan ana cinshi da abinci.

Gyaran fuska da man zaitun

Gyaran Fuska, Kwalliya
Man zaitun na da matukar amfani sosai,a wani bincike da masana suka yi wanda aka gwada akan bera, ya nuna cewa man zaitun din na kashe kaifin Kansa ko cutar daji. A wannan rubutu zamu yi bayanin amfanin man zaitun wajan gyaran fuska. Babban amfanin Man zaitun ga fuska shine yana kawar da alamun tsufa dake fuskar mutu. Wannan ya tabbata, masana sun yi amannar man zaitun yana kawar da alamun tsufa da suka hada da duhun fuska da tattarewarta sosai idan ana amfani dashi aka-akai. Man Zaitun yana matukar amfani sosai wajan kawar da matsalar fuska,musamman kurajen fuska. Hakanan yana maganin duhun da fuska ke yi idan an dade a rana. Ana iya amfani da man zaitun shi kadai ba tare da hadashi da wani abuba a fuska.

Gyaran fuska da madara

Gyaran Fuska, Kwalliya
Wani bincike ya tabbatar da ana amfani da madara a matsayin Cleanser a fuska dan kawar da kurajen fuska, duhun fuska, da matacciyar fatar fuska. Binciken ya bayyana cewa, madarar tana kuma hana bakaken abubuwa bayyana a fuska da kuma bude kofofin gashin fuska. Ana iya amfani da auduga ko kyalle me kyau a goga madarar a fuska. Ana amfani da madara wajan kara hasken fata, kuma akwai mayukan kara hasken fata da yawa da aka hadasu da madara. Saidai babu wani bincike na bangaren masana lafiya daya tabbatar da madara na kara hasken fata. Hakan na nufin za'a iya gwadawa a gani, idan yayi reaction sai a daina, idan kuma bai yi ba, za'a iya yin sati 4 ana gwadawa ana idan fata zata yi haske. Bayan dadewa a rana, ana iya amfani da Madara a shafa a fuska dan kawar da duhun fuska da ra...

Maganin kurajen fuska

Gyaran Fuska, Kwalliya
Akwai hanyoyi da yawa da ake magance matsalar kurajen fuska. A cikin wannan rubutu, zamu yi bayani kan yanda ake magance kurajen fuska ta hanyoyi daban-daban. Saidai kamin mu fara, a sani cewa, idan ana da kurajen fuska, kada a rika wasa dasu da hannu ko sosawa, ko da suna kaikai kuwa. Hakan zai kara dagula matsalar ne maimakon ya magance ta, kai cuta ma zata iya shiga, dan haka a kiyaye. Hanyoyin da za'a iya amfani dasu a matsayin maganin kurajen fuska sun hada da: Ana Amfani da kankara ko ruwan Sanyi: Idan aka dora kankara ko ruwan sanyi akan kurajen fuska, suna daina kaikayi da kumburi kusan nan take. Ana iya samun kankarar a nade a tsumma me tsafta a rika dorawa a jikin kurajen, ko kuma a samu ledar ruwa me sanyi a rika dorawa. Idan an dora a rika barinshi yana kai mintu...

Maganin goge tabo a fuska

Gyaran Fuska, Kwalliya
Tabon fuska matsalace dake damun mata da yawa, kuma akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan goge shi. Ga wasu daga cikin hanyoyin da ake amfani dasu wajan goge tabon fuska kamar haka: Amfani da Aloe Vera: Ana amfani da mai ko ruwan Aloe Vera wajan goge tabon fuska kuma yana aiki sosai, ana iya sayen man Aloe Vera a shagon saida mai wanda ba'a hadashi da komai ba, a duba roba ko kwalin man a tabbatar ba'a hadashi da giya ba ko wasu abubuwa na daban ba, kamin a siya, mafi kyawun hanyar samun mai ko ruwa Aloe Vera shine a hadashi a gida. Ana samun ganyen Aloe Vera a kankare koren ganyen dake jikinshi a matso ruwan a rika shafawa a fuska dan maganin tabon fuska, mun yi cikakken bayani kan yanda ake amfani da Aloe Vera wajan gyaran fuska Hakanan ana amfani da Zuma wajan cire ...