Gwamnati za ta fara kama yaran da ke yawo a titunan jihar Kano
Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai yi aiki kwashe yaran da ke gararamba a titunan birnin.
Hukumomi sun ce ɗaukar matakin ya zama wajibi kasancewar barin yara ƙanana suna yawo a tituna babbar barazana ce ga tsaro da kuma ci gaba al'umma.
Kwamitin zai kuma bai wa gwamnati shawarar kan yadda za a mayar da yaran garuruwan da suka fito.
Kwamitin ƙarkashin shugabancin kwamandan hukumar Hisba, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa zai bi diddigi tare da zaƙulo yaran da suke yawo a kwararo da tituna suna kwana a kasuwanni da ƙarƙashin gada a sassan birnin Kano domin samar musu da kyakkyawar makoma da kuma maslahar al’umma.
"Yaran da za mu fara kamawa sune waɗanda suke kamar an zubar da su yawo kan titi, waɗanda ba su da wata makoma, mafi y...