
Kashim Shettima yayi magana bayan rahoton cewa an hanashi shiga fadar shugaban kasa ya yadu
Ba wanda ya hana ni shiga fadar shugaban kasa - Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana rahotannin da ke yawo cewa an hana shi shiga fadar shugaban kasa a matsayin karya maras tushe.
Daily Trust ta rawaito cewa a daren jiya Juma’a ne wasu rahotanni su ka fito daga wata kafar labarai ta yanar gizo suna cewa an hana Mataimakin Shugaban Kasa shiga fadar shugaban kasa ta hannun wasu jami’an tsaro, tare da cewa an killace shi a gidansa har sai shugaban kasa ya dawo daga tafiyarsa ta kasashen waje.
Amma cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, Mista Stanley Nkwocha, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, ya ce: “A 'yan kwanakin nan, an shirya kuma an tsara yada labaran karya da gangan akan...