
Wani Bincike ya gano Kaso 70 na ‘yan Najeriya na jin haushin Gwamnati da masu kudi
Binciken da wata kungiya me suna Edelman Trust Barometer dake bincike akan yanda mutane ke kallon Gwamnati, Kasuwanci, Kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen yada labarai ta yi ya nuna cewa kaso na mutane da yawa a Najeriya na jin haushin Gwamnati da masu kudi.
Kungiyar ta gudanar da wannan bincikene ta hanyar tambayar mutane ra'ayoyinsu kan ayyukan gwamnati da yanda ake gudanar da kasuwanci da sauransu.
Kaso 70 sun bayyana mata cewa suna ganin abinda masu kudi ke yi na taimakawa wajan kara jefa 'yan Najeriya cikin halin kaka nikayi, hakanan da yawa sun zargi masu kudin da rashin biyan haraji.
Kungiyar ta bayyana cewa, mutane da yawa kuma sun nuna rashin amincewa da gwamnati, da kafafen yada labarai da kuma Kungiyoyi masu zaman kansu.