Monday, November 23
Shadow
Kalli Bidiyo yanda Katon Maciji ya hadiye wata mata me suna Farida da ranta

Kalli Bidiyo yanda Katon Maciji ya hadiye wata mata me suna Farida da ranta

Abin Mamaki
Wani maciji a kasar Indonesia ya hadiye wata mata me suna Farida da ranta. Matar dai an yi tsammanin ta bace ne inda aka bazama nemanta. https://www.tiktok.com/@trending_viewz/video/7378214616637246762?_t=8n2JmKVzcQP&_r=1 Saidai jama'a sun ganota a cikin wani katoton maciji bayan da aka yanka macijin. Lamarin ya farune a kauyen Kalempang dake yankin South Sulawesi na kasar ranar Alhamis, saidai an ganota ne a cikin macijin ranar Juma'a. Farida dai 'yar kimanin shekaru 45 ce kuma tana da yara 4. Mijinta me suna Noni ya bayyana takaicin abinda ya faru inda yayi nadamar barinta ta fita ita kadai. Yace da suna tare da macijin be isa ya hadiyeta ba.
Bidiyo: Kasa karanta sabon taken Najeriya da ‘yan Kwallon Najeriya suka yi ya jawo cece-kuce

Bidiyo: Kasa karanta sabon taken Najeriya da ‘yan Kwallon Najeriya suka yi ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Bidiyon 'yan kwallon Najeriya a filin wasan da suka buga wasa da kasar Africa ta kudu ya jawo cece-kuce. Bidiyon ya nuna 'yan kwallon na Najeriya sun ki rera sabon taken ko kuma ince sun kasa rerashi. Saidai za'a iya cewa, har yanzu mutane da yawa basu kai ga iya taken ba. https://www.youtube.com/watch?v=9IGhoqFJoFM Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya bayyana cewa, canja taken na daya daga cikin muhimman ayyukan da yake son yi a Najeriya.
Hotuna: Wannan Budurwar ta Mutu a dakin saurayinta bayan da ta kai masa ziyara

Hotuna: Wannan Budurwar ta Mutu a dakin saurayinta bayan da ta kai masa ziyara

Soyayya
Wata budurwa me suna Ginika Judith Okoro ta mutu a dakin saurayinta bayan da ta kai masa ziyara. Budurwar wadda malamar Jinya ce shekarunta 22 da haihuwa. Lamarin ya farune a Ezeogba dake Awaka ta karamar hukumar Owerri North a jihar Imo. Iyayen budurwar tuni suka nemi hukumomi da su shiga lamarin dan binciko dalilin mutuwar diyar tasu. Mahaifiyar budurwar, Caroline Nneji ta koka inda tace ita kadai ce diyarta.

Ana kara mafi karancin Albashi zuwa Naira dubu dari da biyar(105,000) zan mayar da crate din kwaina Naira dubu goma(10,000)>>Inji Wannan me kiwon kajin

Kasuwanci
Wani me kiwon kaji ya bayyana cewa, Ana kara mafi karancin Albashi zuwa Naira Dubu dari da biyar(105,000) shima zai mayar da crate din kwansa Naira Dubu goma(10,000). Ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter. https://twitter.com/BashorunGa_/status/1798770654571086102?t=m-LuPzJhHyNp7Q9xbyI_mA&s=19 Saidai da yawa sun masa chaa inda suke cewa bai kyauta ba. Saidai ya bayyana musu shima ma'aikacin gwammatine amma a gyara kasa yanda farashin kayan masarufi zai yi sauki, yafi a kara albashi.
Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa

Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa

Siyasa, Tarihi
Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa. A ranar 8 ga watan Yuni 1998 Allah Ya yi wa tsohan shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, Janar Sani Abacha rasuwa; Yau shekara ashirin da shidda da ke nan. Da Wadanne Irin Ayyukan Alheri Ku Ke Tunawa Da Shi? Allah Ya Jikansa Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa
Real Madrid ta fi kowace kungiya kyau a Duniya>>Inji Messi

Real Madrid ta fi kowace kungiya kyau a Duniya>>Inji Messi

Kwallon Kafa, labaran messi na yau, Wasanni
Tauraron dan kwallon MLS kuma tsohon dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya bayyana cewa, Kungiyar Real Madrid ta fi kowace kungiya Kyau a Duniya. Ya bayyana hakane yayin hirar da aka yi dashi da wata kafa me suna Infobae. Ya bayyana cewa idan sakamako me kyau ake magana, Real Madrid ce kungiyar data fi kowace amma idan kuma iya wasane, ya fi son Guardiola inda yace duk kungiyar da Guardiola ya horas zaka ganda ta yi fice. Yace dan haka iya wasa sai Manchester City amma kuma sakamako sai Real Madrid. Kuma wannan ra'ayi na Messi bai zo da mamaki ba ganin cewa, Real Madrid ce ta lashe kofin zakarun nahiyar turai.