Thursday, January 16
Shadow
ILMI KOGI: Nan Gaba Mutane Za Su Iýà Bacewa Kamar Àĺjàñù, Inji Shêikh Imam Habibi

ILMI KOGI: Nan Gaba Mutane Za Su Iýà Bacewa Kamar Àĺjàñù, Inji Shêikh Imam Habibi

Duk Labarai
Shugabaɲ Kungiyar Malamai Masana Ilimin Taurári na Nájeriya, Shéikh Imam Habibi Abdallah Assufiyyu ya bayyana cewa "mun gano céwa kowanne ɗan Adam yana ɗauke da wata lambar sirri wacce Ubaɲgiji ya halicce shi da ita, da mutane za su iya tantance nasu da kowa zai iya bacéwa kamar yadda jinsin aljannu ke bacewa, kuma da kowa zai iya magana da dan uwansa ba tare da kiran waya ba ko haduwa ta zahiri a ko'ina suke a doran kasa " Shehin Malamin ya kara da cewa "da yiwuwar hakan zai fara kasancewa a shekaru masu zuwa". Me za ku ce?
Saboda matsalar tsaro: Gwamnatin tarayya ta umarci ministan tsaro da shuwagabannin sojoji su koma Sokoto da zama

Saboda matsalar tsaro: Gwamnatin tarayya ta umarci ministan tsaro da shuwagabannin sojoji su koma Sokoto da zama

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta umarci shuwagabannin sojoji da su koma jihar Sokoto da zama. Hakan na zuwa ne yayin da matsalar tsaro musamman ta garkuwa da mutane ke kara kamari a yankin arewa maso yamma. Sanarwar hakan na kunshene a cikin bayanan da sakataren yada labarai, Henshaw Ogubike ya fitar. Yace wannan kokari ne na kawar da matsalar ta'addanci da garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro da ake fama dasu a yankin. Gwamnatin ta bayyana takaici da matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a yankin na Arewa maso yamma inda tace wannan mataki alamu ne na daukar matsalar da muhimmanci da gwamantin ta yi.
Sojoji Śun Ķashe ‘Ýan Ța’àďda 1,166, Yayin Da Suka Kama 1,096, Inji Hedikwatar Tsaro

Sojoji Śun Ķashe ‘Ýan Ța’àďda 1,166, Yayin Da Suka Kama 1,096, Inji Hedikwatar Tsaro

Duk Labarai
Daga Bello Abubakar Babaji Hedkwatar tsaro (DHQ) tace jami’anta sun kashe ƴan ta’adda guda 1,166 tare da tsare wasu 1,096 acikin kwana 29 a faɗin Nijeriya. Daraktan watsa labarai na ofishin, Manjo-Janar Edward Buba ya faɗi hakan a Abuja, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai kan ayyukan jami’an tsaro, a ranar Alhamis. Ya ce, jami’an sun yi nasarar ceto mutane 721 da aka yi garkuwa da su. Sannan, sun kuma ƙwato makamai 391 da wasu nau’ukan bindigu da kayan yaƙi da adadinsu ya kai 15,234 acikin wata guda. Ya ƙara da cewa, sun yi nasarar kamo manyan ƴan ta’addan da kwamandodinsu a yayin gudanar da ayyukansu cikin watan. Waɗanda aka kama a yankin Arewa-maso-Gabas sun haɗa da; Munir Arika, Sani Dilla (aka Ɗan Hausawan Jibilarram), Ameer Modu, Ɗan Fulani Fari Fari, Bakour...
Masana’antar Kannywood Ta Samu Ƙaruwar Galleliyar Sabuwar Jaruma Daga Jihar Bauchi

Masana’antar Kannywood Ta Samu Ƙaruwar Galleliyar Sabuwar Jaruma Daga Jihar Bauchi

Duk Labarai
Jarumar mai suna Sadiya Abdulƙadir wacce aka fi sani da (Sareena) sabuwar Jaruma ce duk da cewa ta ɗan kwana biyu a masana'antar ta Kannywood ana damawa da ita a fagen shirya fina-finan Hausa wadda ƴar asalin Jihar Bauchi ce ƙaramar hukumar Azare. Fim na farko da ta fara yi tun bayan shigowarta masana'antar fim ne mai dogon zango mai suna (Aliya) wanda ake haska shi a (Youtube Channel) na Ali Jita, wato (Ali Jita Multimedia). Yanzu haka dai Jarumar ta faso gada-gadan da zafinta domin cigaba da aikinta na faɗakarwa cikin fina-finan Hausa domin inganta tarbiyyar al'umma. Photo Credit: Dk Photography Wane fata zaku yi mata ?