Saturday, December 21
Shadow

Amfanin dabino ga budurwa ga mata

Amfanin Dabino
Dabino na da matukar amfani ga matan aure da 'yan mata. Ga amfanin Dabino ga Matan Aure da 'yan mata kamar haka: Cin Dabino yana taimakawa mace ta haihu cikin sauki a gida ba tare da zuwa a sibiti ba. Cin Dabino yana taimakawa wajan gyaran gashi da hana karyewa da faduwar gashin. Ina matan da kiba ta musu yawa, suke son komawa jikinsu ya daidaita? Cin dabino yana taimakawa wajan rage kiba da daidaita jikin mata. Ina mata dake son fuska ta rika sheki ta daina tattarewa da nuna alamun tsufa? Dabino na timakawa wajan kyawun fatar jiki data fuska. Dabino na karawa mace ni'ima da samun gamsuwa yayin jima'i. Yawanci mata masu ciki suna sane da cewa a lokacin laulayin ciki sukan yi fama da ciwon basir, dabino na taimakawa wajan magance wannan matsala. Dabino na taimakawa m...

Amfanin dabino ga maza

Amfanin Dabino
Cin Dabino na da matukar Amfani sosai ga kowane jinsi amma anan zamu yi maganane akan amfanin cin Dabino ga maza: Abu na farko shine, Dabinon na magance matsalar Free Radicals wanda abubuwane dake sanya saurin tsufa, duk me cin dabino akai-akai zai ga yijikinsa baya irin tattarewar tsufa sosai sannan baya yawan kamuwa da cutuka barkatai. Hakanan yana zama garkuwa daga kamuwa da cutar daji watau Cancer da kuma cutar ciwon zuciya me tsanani. Cin dabido yana karawa kwakwalwa lafiya da kaifin basira sosai. Hakanan cin dabino yana karawa namiji karbin mazakuta da iya gamsar da iyali a gado. Yana taimakawa wajan narkewar abinci a ciki hakanan yana taimakawa wajan rage kiba, jikin mutum ya daidaitu. Cin Dabino yana karawa namiji yawa da kuma ingancin ruwan maniyyi. Yana taima...

Kanunfari yana maganin infection

Amfanin Kanunfari
Eh! Kanunfari yana maganin infection. Bincike ya tabbatar da cewa, man Kanunfari na dauke da sunadaran Antibacterial, Antifungal, Insecticidal, da kuma Antioxidant. Dan haka masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, Kanunfari yana taimakawa wajan rage ciwon lokacin al'adar mata hakanan kuma yana maganin Infection. Kanunfari, musamman manshi yana maganin infection na al'aura ko farjin mata, matsaloli irinsu kaikan gaban mace, zafin gaban mace ko fitar da ruwa. Ana iya samun man Kanunfari a kasuwa ko kuma ana iya hadashi a gida. Yanda ake hada man Kanunfari a gida shine, ana samun Kanunfarin a daka a zuba a wata roba ko kwalba, sannan sai a samu man zaitun, kwa-kwa ko wani a zuba a ciki. Sai a kulle wannan kwalba ko roba zuwa sati daya. Bayannan sai a samu rariya a ta...
Hoto: An kamasu sun yiwa matar aure da kawayenta fyade

Hoto: An kamasu sun yiwa matar aure da kawayenta fyade

Tsaro
Hukumar 'yansanda sun kama wadannan 'yan fashin a Abagana dake karamar hukumar Njikoka jihar Anambra. Rahoto yace mutanen sanannun masu yiwa mata fyadene. Sun shiga gidan wata mata inda suka sameta ita da kawayenta suka musu fyade sannan suka sa daya daga ciki ta tura musu kudi. Kakakin 'Yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargin sun amsa laifukansu. Sannan za'a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Kanunfari da zuma

Amfanin Kanunfari
Hadin Kanunfari da zuma na da matukar amfani a jikin dan Adam daya daga ciki shine idan akwai matsalar ciwon makoro. Shan wannan hadi yana taimakawa sosai wajan magance matsalar makogoro. Hakanan wannan hadi yana da matukar amfani ga masu fama da mura da tari, musamman lokacin sanyi. Hakanan wannan hadi na karawa garkuwar jikin mutum karfi sosai. Wannan hadi kuma yana taimakawa wajan magance matsalar warin baki da sauran matsalolin cikin bakin.

Amfanin kanunfari da madara

Amfanin Kanunfari
Amfanin hadin Kanunfari da madara na da yawa sosai. Daya daga ciki shine yana taimakawa sosai wajan magance matsalar warin baki ko kuma hana narkewar abinci ko a ce bata ciki. Wannan hadi kuma na Kanunfari da Madara yana kawar da Kasala. Hakan kuma yana taimakawa wajan daukar ciki. Ga wanda basu da karfin jima'i, yana taimakawa sosai wajan karawa namiji kuzari. Yana kara karfin Garkuwar jiki. Yana kuma karawa kashin mutum karfi sosai. Yana kashe Bacteria. Yana maganin kansa, watau ciwon daji, musamman na mama ga mata. Yana kuma taimakawa karfin ido wajan gani. Ga mai fama da sarkewar Numfashi, ko numfashi sama-sama, Kanunfari da Madara na taimakawa wajan magance wannan matsala. Yana kuma karawa namiji yawan maniyyi da karfin fitar ruwan maniyyin.