Hoto: An daure wannan mutumin saboda ya cire kwaroron roba yayin da yake jima’i da wata mata da suka amince cewa zai yi amfani da kwaroron roba amma ya yaudareta ya cire bata sani ba
An daure Guy Mukendi me shekaru 39 tsawon shekaru 4 da wata 3 saboda cire kwaroron roba yayin jima'i ba tare sa sanin matar da yake jima'i da ita ba.
Shi da matar dai sun amince su yi jima'i amma da sharadin zai saka kwaroron roba.
Saidai ya yaudareta ya cire, anan ne ita kuma ta kaishi kara.
A dokar kasar Ingila, idan mutum ya cire kwaroron roba ba tare da amincewar matar da yake jima'i da ita ba to kamar ya mata fyade ne.
Mutumin dai ya bata hakuri inda yace dalilinsa shine ya dade bai yi jima'i ba amma duk da haka taki hakura inda ta yi amfani ma da sakon hakurin da ya aika mata a matsayin shedar cewa ya cire kwaroron robar.
Mutumin dai ya ki amsa laifinsa amma hujjojin da aka samu akansa sun tabbatar da ya aikata abinda ake zarginsa da aikatawa dan haka aka yanke masa hu...