Blinken a Masar don inganta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Masar domin samun goyon bayan yankin ga yarjejeniyar zaman lafiyar Gaza da shugaba Joe Biden ya gabatar kwanan nan.
Wannan ziyarar dai ita ce ziyara ta takwas da Blinken ya kai yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan ɓarkewar rikicin Gaza.
Blinken zai gana da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi kafin ya tattauna da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a yau Litinin.
Masu shiga tsakani a yankin ciki har da Qatar, sun shafe watanni da dama suna ƙoƙarin sasantawa tsakanin Isra'ila da Hamas.
Netanyahu ya ci gaba da jajircewa wajen ƙin amincewa da duk wani tsagaita bude wuta har sai an wargaza sojojin Hamas da kuma sako duk waɗanda aka yi garkuwa da su.
A karshen makon da ya gabata, sojojin Isra'ila sun kuɓutar da wasu mutane hu...