Monday, December 15
Shadow
Dubu 13 Gwamnan jihar Kebbi ke biyan malaman makarantar Firamare a matsayin Albashi>>Inji Dan Bello

Dubu 13 Gwamnan jihar Kebbi ke biyan malaman makarantar Firamare a matsayin Albashi>>Inji Dan Bello

Duk Labarai
Shahararren me yiwa 'yan siyasa Tone-tone, Dan Bello ya bayyana cewa, Naira 13,500 gwamnan jihar Kebbi ke biyan ma'aikata a matsayin mafi karancin Albashi. Yace hakan na zuwane a yayin da gwamnan zai kashe Naira Biliyan 1.3 a matsayin kudin sayen firjin. Naira 70,000 ne dai mafi karancin Albashi a Najeriya. https://twitter.com/BelloGaladanchi/status/1966876330127155307?t=m8xKKQI9CTnxwv27RY0L3g&s=19
Farashin kayan Abinci ya fadi kasa sosai>>Inji Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu

Farashin kayan Abinci ya fadi kasa sosai>>Inji Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Farashin kayan abinci ya fadi kasa sosai biyo bayan matakan da ta dauka. Ministan Noma, Senator Abubakar Kyari ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi dashi a Arise TV. Yace sun shigo da shinkafa ne dan karya farashinta ba dan saka Manoma asara ba, yace kuma shigo da shinkafar daga kasashen waje na wucin gadi ne. Yace Najeriya na da gibin kaso 15 cikin 100 na shinkafar da ake bukata, kuma itace suka shigo da ita dan cike wannan gibi.
Bidiyon yanda wani mutum me suna Yunusa Ahmadu Yusuf, ya rigamu gidan gaskiya bayan shiga dakin otal da wata me suna Ruth a Abuja

Bidiyon yanda wani mutum me suna Yunusa Ahmadu Yusuf, ya rigamu gidan gaskiya bayan shiga dakin otal da wata me suna Ruth a Abuja

Duk Labarai
Wani mutum me suna Yunusa Ahmadu Yusuf ya rigamu gidan gaskiya bayan shiga dakin Otal da wata mata me suna Ruth. Lamarin ya farune a Karu-Jikwoyi, Abuja inda mutumin me shekaru 47 ya mutu. Rahotanni sun ce tun bayah da ya shiga daki da matar bai ci komai ba sai giya yake ta kwankwada. Matar ta fita ta sayo masa lemun kara karfin kwanji inda bayan ya sha ne ya suma, daga nan ne kuma rai yayi halinsa. Tuni an fara binciken dalilin mutuwarsa. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1966940919791301113?t=dEzEalSqKYaSMXghKfQCRA&s=19
Kalli Bidiyo: Shinkafar da aka dafa a Tukunya mafi girma a Duniya ta yi yawa, saida aka rika bin mutane ana basu a bakin titi

Kalli Bidiyo: Shinkafar da aka dafa a Tukunya mafi girma a Duniya ta yi yawa, saida aka rika bin mutane ana basu a bakin titi

Duk Labarai
Hilda Baci data dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya a Legas ta rika bin mutane bakin titi tana raba musu shinkafar. Hakan ya biyo bayan yawan da shinkafar ta yi duk da mutane kusan dubu 20 da rahotanni suka ce sun yi rijista dan zuwa wajan cin shinkafar https://twitter.com/Teeniiola/status/1966916664051855714?t=PWgg0PIZ2xD8JAaqtMobTg&s=19 A baya dai an ga Bidiyon Hilda Baci na rokon mutane cewa su je su ci shinkafar dan ba yadda zata yi da ita, ta mata yawa.
Kalli Bidiyon: Shinkafar da aka bamu bata dahu ba, kuma ba nama, Inji daya daga cikin wadanda suka halarci wajan dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya a Legas

Kalli Bidiyon: Shinkafar da aka bamu bata dahu ba, kuma ba nama, Inji daya daga cikin wadanda suka halarci wajan dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya a Legas

Duk Labarai
Daya daga cikin wadanda suka halarci wajan dafa shinkafar Hilda Baci wadda aka dafa a tukunya mafi girma a Duniya a Legas, yace shinkafar bata dahu ba. Yace shinkafar ta yi dadi amma bata dahu ba sannan babu nama a ciki. https://twitter.com/Teeniiola/status/1966910035990372469?t=FrqBV6waJxMTTuvIPzMLGQ&s=19
Bidiyon Namiji nawa Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Fiddausi Yahya Kwalliya ya jawo cece-kuce inda mutane ke tambayar wai dama namiji ne ke musu kwalliya?

Bidiyon Namiji nawa Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Fiddausi Yahya Kwalliya ya jawo cece-kuce inda mutane ke tambayar wai dama namiji ne ke musu kwalliya?

Duk Labarai
Anga Tauraruwar fina-finan Hausa, Nana Fiddausi Yahya namiji na mata kwalliya a wajan daukar fim. Hakan yasa mutane ke mamakin dama wai namiji ne kewa taurarin fina-finan Hausa mata Kwalliya? Lamarin dai ya jawo muhawara sosai. https://www.tiktok.com/@halima.essah/video/7547794939048889618?_t=ZS-8zh7L7i4ui8&_r=1
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa Hilda Baci wadda ta dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa Hilda Baci wadda ta dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa Hilda Baci wadda ta dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya. Shugaban kasar yayi wannan jinjinane ta bakin ministan yada labarai, Mohammed Idris, inda yace abinda Hilda ta yi ya jawowa Najeriya suna a Idon Duniya kuma yace 'yan kasa na al'fahari da ita. Shugaban yace, matasa su yi koyi da irin abinda Hilda ta yi inda ya sha alwashin cewa gwamnati zata tallafawa irin wannan kokari nan gaba. Hilda Baci dai ta yi wannan abu ne dan shiga kundin Tarihin Duniya hakanan a shekarar 2023 ma ta yi girki na lokaci mafi tsawo a Duniya.
Kalli Bidiyon Yanda Hilda Baci ke raba shinkafar data dafa a tukunya mafi girma a Duniya

Kalli Bidiyon Yanda Hilda Baci ke raba shinkafar data dafa a tukunya mafi girma a Duniya

Duk Labarai
Hilda Baci wadda ta dafa shinkafa a Tukunya Mafi girma a Duniya tuni ta fara rabon wannan shinkafa. https://www.tiktok.com/@hildabaci/video/7549444036134800648?_t=ZS-8zh3TmZ2rDt&_r=1 https://www.tiktok.com/@hildabaci/video/7549479359577328903?_t=ZS-8zh2SVCoSUC&_r=1 Saidai duk da rabon da take yi, shinkafar ta yi saura inda take rokon mutane dasu je su ci.