Tuesday, December 16
Shadow
Kalli Bidiyo: ‘Yar Najeriya Hilda Baci ta fara girka Tukunyar shinkafa mafi girma a Duniya dan shiga kundin tarihin Duniya

Kalli Bidiyo: ‘Yar Najeriya Hilda Baci ta fara girka Tukunyar shinkafa mafi girma a Duniya dan shiga kundin tarihin Duniya

Duk Labarai
'Yar Najeriya, Hilda Baci ta fara girka tukunyar Shinkafa mafi girma a Duniya dan ta shiga kudin tarihin Duniya. Tana girkinne a Victoria Island Legas inda mutane da 'yan Jarida suka taru dan ganewa idanunsu yanda zata kasance. https://www.tiktok.com/@hildabaci/video/7549073070871301383?_t=ZS-8zfgU56bXtZ&_r=1 https://www.tiktok.com/@hildabaci/video/7548725143418211591?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7548725143418211591&source=h5_m&timestamp=1757698680&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=...
Likitoci sun fara yajin aiki a faɗin Najeriya

Likitoci sun fara yajin aiki a faɗin Najeriya

Duk Labarai
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwararewa ta sanar da fara yajin aikin gargadi na kwana biyar daga yau, bisa ga matsayar da aka cimma a majalisar zartarwar ƙungiyar. Ƙungiyar ta bukaci dukkan mambobinta a cibiyoyi daban-daban su bi wannan umarni ba tare da kaucewa ba. A cewar kungiyar, matakin yajin aikin ya zama dole ne domin matsa lamba ga gwamnati kan buƙatunsu na inganta walwala da kyautata yanayin aiki, tare da tabbatar da ingantacciyar tsarin kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya. Sun ce makasudin yajin ba wai cutar da al’umma ba ne, sai dai domin tabbatar da nagartar harkar lafiya a kasa. Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin mambobinta a wannan lokaci, inda ta ce nasarar wannan mataki zai dogara ne akan yadda kowa zai tsaya tsayin daka wajen aiwatar da yajin aikin. ...
Kwanannan za’a daina dauke wuta kwata-kwata a Najeriya>>Inji Gwamnatin Tarayya

Kwanannan za’a daina dauke wuta kwata-kwata a Najeriya>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Kwanannan za'a daina dauke wutar Lantarki kwatakwata a kasar. Hakan ya fito ne daga bakin ministan wuta, Adebayo Adelabu a wata ganawa da manema labarai a Abuja. Ya bayyana cewa, gwamnati na kokari kan hakan kuma tuni suka fara ganin sakamako me kyau. 'Yan Najeriya sun dade suna kukan rashin tsayayyar wutar lantarki.
Matatar Dangote za ta fara rarraba mai kai-tsaye bayan rage farashinsa

Matatar Dangote za ta fara rarraba mai kai-tsaye bayan rage farashinsa

Duk Labarai
Matatar man fetur ta Dangote ta sanar cewa za ta fara rarraba man kai-tsaye zuwa tashoshi a duk faɗin Najeriya daga ranar Litinin, 15 ga Satumba. Kazalika, kamfanin ya rage farashin man fetur ga masu gidajen mai zuwa N820 kan lita ɗaya, inda gidajen man jihohin Legas da sauran jihohin yammacin Najeriya za su sayar da shi kan N841. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin na fitar a shafinsa na X. Sai kuma Abuja da Rivers da Delta da Edo da Kwara za su sayar kan N851. Ta ce daga baya shirin zai karaɗe sauran jihohin ƙasar. Kamfanin ya ce an yi wannan tsarin ne domin rage farashin rarraba man da kuma sauƙaƙa farashin a tashoshi, da kuma rage matsin tattalin arziki. Haka nan, ana sa ran tsarin zai amfani ƙananan masana’antu sama da miliyan 42 ta hanyar rage farashin...
Albashin 100,000 da kudin abinci na 5,000 kullun da ake baiwa sojoji yayi kadan>>Inji Sanata Ali Ndume

Albashin 100,000 da kudin abinci na 5,000 kullun da ake baiwa sojoji yayi kadan>>Inji Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa, Albashin Naira 100,000 da kuma kudin abinci na Naira 5,000 da ake baiwa sojoji kullun yayi kadan. Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai inda yace hakan ba zai karfafa sojoji su gudanar da ayyukansu yanda ya kamata ba. Sanata Ali Ndume na martanine kan wasu dake kiran a sauke shuwagabannin sojojin. Yace matsalar ta karancin kudi ce.
Kotu ta aikawa bangaren su David Mark sammace akan shugabancin jam’iyyar ADC

Kotu ta aikawa bangaren su David Mark sammace akan shugabancin jam’iyyar ADC

Duk Labarai
Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta aikawa shugaban jam'iyyar ADC na riko, David Mark takardar sammace inda tace ya je ya kare kansa akan shugabancin jam'iyyar. Motun ta bukaci David Mark da sakataren riko na jam'iyyar ADC, Rauf Aregbesola su je su gaya mata dalilan da zasu hana a tsigesu daga shugabancin jam'iyyar. Hakan na zuwane bayan da Nafiu Gombe ya gabatar da kara a kotun inda yake cewa shine halastaccen shugaban jam'iyyar ADC ba David Mark ba. Ya kuma bukaci kotun data tsige David Mark daga shugabancin jam'iyyar ADC. Saidai kotun bata amsa bukatarsa ba inda tace maimakon tsige David Mark, tana bukatar ya bayyana a gabanta kamin 15 ga watan Satumba dan ya bata hujjojin da zasu sa kada a tsigeshi daga shugabancin jam'iyyar ADC.
Malamai sun sauke Qur’ani a Kano dan nasarar Shugaba Tinubu a 2027 da kuma takarar Gwamna ta Sanata Barau Jibrin

Malamai sun sauke Qur’ani a Kano dan nasarar Shugaba Tinubu a 2027 da kuma takarar Gwamna ta Sanata Barau Jibrin

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kano na cewa an gudanar da addu' da yankan Dabbobi sannan an sauke Qur'ani saboda neman Allah ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sanata Barau Jibrin Maliya nasara a 2027. Rahoton yace an yi wanan taronne a gidan Baballiya dake Kurna karamar hukumar Fagge dake Kano. Kuma mutane daga kowacce karamar hukumar a jihar sun samu halarta. Bayan kammala saukar Qur'anin, an gabatar da addu'a ga Shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sanata Barau Maliya kan Allah ya basu nasara. Sannan kuma malaman sun yi Addu'ar Allah ya bada zaman lafiya, ci gaban tattalin arziki a Najeriya baki daya.