Yadda ake gane cikin tagwaye
Babbar hanyar da ake gane cikin tagwaye shine ta yin gwaji.
Saidai akwai alamomi na al'ada wanda ake amfani dasu wajan gane cikin tagwaye bisa yanda aka saba gani a wajen masu haihuwarsu:
Wadannan alamu na cikin gwaye sune kamar haka:
Wadannan alamomi da zaku karanta sukan farune a kwanakin farko-farko na daukar ciki.
Za'a ji motsin ciki da wuri.
Za'a ji motsin ciki a bangarori daban-daban na cikin.
Cikin zai yi girma fiye da yanda aka saba gani a sauran cikkunan da ake dauka.
Nauyin jikin me cikin zai karu sosai.
A wajan gwaji, na'ura zata nuna zuciyoyi biyu na bugawa.
Wadannan sune alamomin dake nuna mace na dauke da Tagwaye, saidai kamar yanda muka fada a farko, babbar hanyar gane Tagwaue itace a yi gwaji.
Mace zata iya rika jin wadannan alamomi a jikinta i...