2024Sojojin Najeriya sun musanta zarge-zargen da Amnesty International ta yi musu
Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton da Amnesty International ta fitar na zargin jami’anta da tsare tare da cin zarafin mata da yara da dama da suka tsere daga hannun ‘yan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.
Mai magana da yawun rundunar Edward Buba ta bakin mataimakinsa kan yaɗa labarai, Group Kaftin Ibrahim Ali Bukar, ya shaida wa BBC cewa "ba za su damu da irin waɗannan kalamai na son kai da aka yi da niyyar rage kwarin gwiwar sojojin fafutuka don tabbatar da tsaro ba"
Ya kara da cewa sojojin za su yi haɗin gwiwa mai inganci da Amnesty International idan akwai bukatar yin hakan kuma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kawar da ta'addanci da tabbatar da tsaro.
Wannan martanin ya zo ne kwana guda bayan da Amnesty International ta zargi gwamnati da gazawa wajen bai wa ...