
Sha’aban Sharada ya sauya sheƙa zuwa APC
YANZU-YANZU: Sha'aban Sharada ya sauya sheƙa zuwa APC
Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar ADP a zaben 2023, Sha'aban Sharada ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar zuwa APC.
A wani faifen bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Sharada, tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kano Municipal, ya sanar da komawa APC din ne a wata liyafa da ya haɗa ga magoya bayan sa a gidan sa da ke Kano.
Ya ce ya auna ya ga cewa "da sabon gini gwanda yaɓe", bayan ya maida al'amuran ss ga Allah kan Ya yi masa zaɓi na alheri.
DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa a kwanakin bayan an hango Sharada tare da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje a Abuja, lamarin da tun a lokacin ake kallon kamar yunkurin komawa jam'iyyar ta sa ya ke yi.
A lokacin da ya ke taka...