Monday, December 15
Shadow
Shugaba Tinubu ya suke Gawuna daga shugaban Kwamitin gudanarwa na jami’ar Bayero dake Kano

Shugaba Tinubu ya suke Gawuna daga shugaban Kwamitin gudanarwa na jami’ar Bayero dake Kano

Duk Labarai
Shuagaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada AVM Sadiq Ismail Kaita a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwa na jami'ar Bayero dake Kano. Kaita ya maye Dr. Nasiru Yusuf Gawunane a wannan mukami. Gawuna kuma shine shugaban hukumar kula da gidaje ta kasa. A sanarwar da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar Yace an cire gawuna daga shugabancin kwamitin gudanarwa na BUK ne dan ya mayar da hankali kan shugabancin hukumar kula da gidaje ta kasa Gawuna dai na hannun damar tsohon shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne.
Kungiyar kare hakkin musulmai ta Najeriya, MURIC ta nemi Gwamnati ta gina kotunan shari’ar Musulunci a kowace jiha

Kungiyar kare hakkin musulmai ta Najeriya, MURIC ta nemi Gwamnati ta gina kotunan shari’ar Musulunci a kowace jiha

Duk Labarai
Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Musulmai a Najeriya, MURIC ta bukaci Gwamnatin tarayya ta gina Kotunan shari'ar Musulunci a kowace jiha dake kasarnan. Kungiyar tace dokar da ake amfani da ita babu adalci a ciki kuma akwai wasu sassa na kasarnan da babu kotunan Shari'a shiyasa take gabatar da wannan bukata. Kungiyar tace dan hakane take bukatar gwamnatin tarayya kamar yanda aka gina manyan kotunan gwamnatin tarayya a kowace jiha to itama kotun shari'ar Musulunci a ginata a kowace jihar. Shugaban kungiyar, Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Karya ministan Lafiya yake, bamu janye yajin aiki ba>>Inji Kungiyar malaman Jinya(Nurse) na Najeriya

Karya ministan Lafiya yake, bamu janye yajin aiki ba>>Inji Kungiyar malaman Jinya(Nurse) na Najeriya

Duk Labarai
Kungiyar malaman jinya(Nurse) da Ungozoma (NANNM-FHI) sun bayyana cewa, basu janye yajin aikin da suka shiga ba na kwanaki 7. Kungiyar ta nesanta kanta da kalaman Ministan lafiya, Prof. Muhammad Pate wanda a dazu bayan kammala zaman tattaunawa dasu yace sun amince su janye yajin aikin. Me magana da yawun kungiyar, Omomo Tibiebi ne ya bayyana haka inda yacw yajin aikin da suka fara tun ranar Laraba har yanzu basu janye ba. Yace ba ministan ne ya ke yajin aikin ba, dan haka bashi da hurumin janye yajin aikin. Yace sai a ranar Asabar ne zasu zauna dan tattauna batun da duba irin alkawarin da gwamnatin ta musu ko abune da zasu iya amincewa dashi ko kuwa a'a.
Karanta Jadawalin shekarun Gwamnonin Najeriya, Ko Gwamnan jiharku shekarunsa nawa?

Karanta Jadawalin shekarun Gwamnonin Najeriya, Ko Gwamnan jiharku shekarunsa nawa?

Duk Labarai
Wannan Jadawalin shekarun Gwamnonin Najeriya ne: Bala Muhammed (Bauchi): 66 years Douye Diri (Bayelsa): 66 years Hope Uzodinma (Imo): 66 years Charles Soludo (Anambra): 65 years Bassey Otu (Cross River): 65 years Abdulrahman Abdulrasaq (Kwara): 65 years Abdullahi Sule (Nasarawa): 65 years Dapo Abiodun (Ogun): 65 years Ademola Adeleke (Osun): 65 years Muhammad Yahaya (Gombe): 63 years Sheriff Oborevwori (Delta): 62 years Umar Namadi (Jigawa): 62 years Abba Kabir Yusuf (Kano): 62 years Umo Eno (Akwa Ibom): 61 years Alex Otti (Abia): 60 years Babajide Sanwo-Olu (Lagos): 60 years Lucky Aiyedatiwa (Ondo): 60 years Caleb Mutfwang (Plateau): 60 years Nasir Idris (Kebbi): 59 years Dauda Lawal (Zamfara): 59 years Hyacinth Alia (Ben...
Da Duminsa: Kasar Amurka ta Laftawa Najeriya sabon Haraji

Da Duminsa: Kasar Amurka ta Laftawa Najeriya sabon Haraji

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka ta Laftawa Najeriya sabon harajin kaso 15 cikin 100. Hakan na zuwane bayan da kwanaki 90 da kasar ta Amurka ta ware dan tattaunawar huldar kasuwanci da Najeriya ta kusanto. A watan Afrilu kasar Amurka ta kakabawa Najeriya harajin kasuwanci na kaso 14 cikin 100. Saidai a wannan sabuwar sanarwar an sabunta tare da kara kaso 1 inda ya koma kaso 15 cikin 100. Lamarin dai ba Najeriya kadai ya shafa ba hadda sauran kasashen Duniya da dama.
Kalli Bidiyon: Gwamnan Adamawa ya baiwa me horas da ‘yan wasa na Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya Kyautar gida me dakuna 3 da Naira Miliyan 50

Kalli Bidiyon: Gwamnan Adamawa ya baiwa me horas da ‘yan wasa na Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya Kyautar gida me dakuna 3 da Naira Miliyan 50

Duk Labarai
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya baiwa Kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Justin Madugu kyautar gida da Naira Miliyan 50. Ya bashi kyautar ne a gidan gwamnatin jihar Adamawa. Ya bashi kyautar saboda kokarin da yayi na kai 'yan matan suka lashe kofin Afrika na mata wanda suka buga wasan karshe da kasar Morocco. Suma dai 'yan matan kowacce gwamnatin tarayya ta basu kyautar Naira Miliyan 152 da kuma gidaje. Sannan gwamnoni sun basu kyautar Naira Miliyan 10 kowacce. https://twitter.com/thecableng/status/1951307863176905132?t=5AnXPDT8jRDv8S2xlBvkog&s=19
Kalli Bidiyo: Su Bala Lau ‘yan Tawayene, Sheikh Sani Yahya Jingir shine shugaban Izala na gaskiya>>Inji Sheikh Musa Salihu Alburham

Kalli Bidiyo: Su Bala Lau ‘yan Tawayene, Sheikh Sani Yahya Jingir shine shugaban Izala na gaskiya>>Inji Sheikh Musa Salihu Alburham

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama Sheikh Misa Salihu Alburham ya bayyana cewa, Sheikh Sani Yahya Jingir shine shugaban Izala na gaskiya. Inda ya kara da cewa, Su Sheikh Bala Lau 'yan Tawayene. Ya bayyana hakane a wani faifan Bidiyon sa sa ya watsu sosai a kafafen sadarwa. https://www.tiktok.com/@darul_burhan_majlis/video/7532275234850852102?_t=ZS-8yWF1N9LLGL&_r=1
Da Duminsa: Malaman Jinya(Nurse) sun janye yajin aikin da suke

Da Duminsa: Malaman Jinya(Nurse) sun janye yajin aikin da suke

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, yajin aikin da malaman Jinya na Asibiti, watau Nurse suka shiga a karkashin kungiyarsu me suna (NANNM) ya zo karshe. Ministan Lafiya, Professor Ali Pate ne ya bayyana hakan bayan ganawa da wakilan malaman jihar, Nurse a ranar Juma'a. Saidai wakilan malaman jinyar sun ki cewa uffan bayan kammala zaman. A baya dai malaman jinyar sun shiga yajin aikin kwanaki 7 na gargadi.