Sanata Okey Ezea daga jihar Enugu ya rigamu gidan gaskiya.
Sanata Natasha Akpoti da Sanata Orji Uzor Kalu ne suka tabbatar da hakan.
Sanata Kalu a ganawa da manema labarai a Abuja yace ya samu labarin mutuwar Sanata Okey Ezea da gigici inda yace abokin aiki ne kuma dan uwa.
Yace sukan je ma coci tare.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai bar ƙasar a yau Laraba domin halartar taron G20 da taro tsakanin kungiyar Tarayyar Turai da ta Tarayyar Afirka.
Shugaban zai soma ziyarar ne a Johannesburg,babban birnin ƙasar Afrika ta kudu, inda zai halarci karo na ashirin na taron shugabannin ƙasashe ashirin masu ƙarfin tattalin arziƙi wato G20 a ranakun 22 da 23 ga watan Nuwamba.
Daga nan zai tafi birnin Luanda da ke Angola domin halartar taron kungiyar Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka karo na 7 a ranakun 24 da 25 ga watan Nuwamban 2025.
Waɗannan bayanai na ƙunshe ne a cikin sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar a babban birnin ƙasar Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.
Ana kuma sa ran Shugaba Tinubu zai yi wasu gana...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar da mutuwar jami'in sojan ƙasar Birgediya Janar Musa Uba, wanda mayaƙan ƙungiyar Iswap suka kashe a jihar Borno.
An fara fargabar mutuwar Janar Uba ne bayan ƙungiyar ta yi iƙirarin kashe shi, da kuma fitar da wani bidiyo.
Wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar ta ce a ƙarshen makon da ya gabata ne 'yanbindigar suka yi wa dakarunta kwanton ɓauna, waɗanda janar ɗin ke jagoranta.
Zuwa yanzu rundunar ba ta ce komai ba game da bidiyon da ke yawo a intanet.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Shugaba Tinubu ya ce mutuwar janar ɗin "ta kaɗa" shi.
"A matsayina na babban kwamandan tsaro na ƙasa, na ji takaici da mutuwar sojojinmu a bakin aiki. Allah ya bai wa iyalan Bi...
Wata kungiya me suna The Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria ta 'yan Najeriya wadda suka kafa a kasar Amirka tace ta yi na'am da Amurka ta saka Najeriya cikin kasashen da zata rika sakawa ido.
Kumgiyar tace tana kira ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump da ya gaggauta kawo Kharin da yace zai kawo Najeriya.
Kungiyar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ta bakin shugabanta, Comrade Frederick Odorige inda tace tana goyon karfafa tsaro da Dimokradiyya a Najeriya.
Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa, kaso 90 na musulman Najeriya Sunni ne.
Ya bayyana hakane a martanin da yakewa 'Yar siyasar kasar Canada, Goldie Ghamari inda tace Najeriya na hada kai da kasar Iran dan Khasye Kiristoci.
Yace abinda ma bata sani ba shine kaso 90 na musulman Najeriya Sunni ne.
Yace 'yan kasar waje suna amfani da rarrabuwar mu ne wajan cimma burinsu inda yace sai mun hada kai.
https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1990889063834861572?t=RKCwoiSicU5RhxOM7Q_0VA&s=19
Tauraruwar fina-finan Hausa, Fatima Hussain ta fito ta bayyana takaici kan garkuwa da dalibai mata 25 da aka yi a jihar Kebbi.
Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace idan ba'a so a yi karatu ne a kulle makarantun mana.
Tace duka yaushe aka sace dalibai mata amma gashi an sake yi.
Tace daliban na da kananan shekaru.
https://www.tiktok.com/@fateeemahussain/video/7574376952191028500?_t=ZS-91WmE2naJV3&_r=1
Rahotanni da Duminsa sun bayyana cewa 'yan Bìndìgà a Daji sun afkawa sojojin da aka aika su kubutar da dalibai 'yan mata da aka yi garkuwa dasu a jihar Kebbi.
A Bidiyon wanda kafar Sahara Reporters ta wallafa, an ga sojojin kwakkwance cikin Jiyni wasu an Harbesu a kafa wasu a sassa daban-daban na jikinsu.
Dalibai mata 25 ne dai 'yan Bìndìgàr suka yi garkuwa dasu inda wasu biyu suka kubuta.
Danna nan dan kallon Bidiyon
https://twitter.com/SaharaReporters/status/1991074295015997845?t=50Y5DUr-jQN8s0-V8zdaXQ&s=19
Sanata Abdul Ningi ya bayyana takaici kan matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya.
Yace kwanaki kadan da Khashye Brigadier General gashi an sace daliban makaranta yace dan haka ya kamata ayi wani abu.
Yace a daina cewa wannan bangaren ne ke yiwa wancan bangare ko kuma wannan addinine kewa wancan addini, inda yace a hada kai a magance matsalar.
Kalli Bidiyon hirar anan
https://twitter.com/ChuksEricE/status/1990836849506500627?t=7pF3ObU4kFRKrjbke33xGQ&s=19
Rahotanni na fitowa cewa hukumar 'yansandan Farin kaya ta DSS yi gargadin cewa ana shirin kai wa makarantar 'yan mata ta MAGA dake jihar Kebbi hari.
Gwamman jihar Kebbi, Mohammed Nasir Idris ya tabbatar da cewa DSS sun sanar dasu game da gargadin kuma suka bayar da shawarar a gudanar da taron tsaro kan lamarin.
Gwamnan yace sun gudanar da taro akan tsaro aka kai jami'an tsaro makarantar dan su tsare daliban amma sai suka buge da daukar hotuna da dalibai 'yan mata 'yan makarantar.
Gwamnan yace mintuna 30 kamin a kai harin, jami'an tsaron dake baiwa makarantar kariya sun janye suka kama gabansu.
Gwamnan ya kai ziyara makarantar ranar Litinin da misalin karfe 6:45 na safe kamar yanda kafar Pointblacknews.com ya ruwaito.
Kafar tace wani jami'in tsaro ya bayyana mata cewa, gwamna...
Tsohuwar Firaiministar kasar Canada, Goldie Ghamari ta bayyana cewa, sun gano Najeriya na aiki da kasar Iran a munafurce.
Sannan ta zargi Gwamnatin Tarayya da hannu a matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya.
Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita da dan jaridar kasar Ingila, Piers Morgan da ministan harkokin kasashen waje na Najeriya, Yusuf Tuggar Maitama.
Tace A tsarin Najeriya ya kamata idan shugaban kasa ya zama musulmi, mataimakinsa ya zama kirista hakanan idan shugaban kasa kiristane, mataimakinsa zai zama Musulmi.
Tace amma a gwamnatin tinubu babu wakilcin kiristoci inda ta zargi cewa ana muzgunawa Kiristoci.