Tuesday, January 21
Shadow

Gajerun sakonnin soyayya

Kalaman Soyayya, Soyayya
Ga Gajerun sakonnin soyayya masu rasha jiki kamar haka: Duk yadda zuciyata ke tafasa da na ganki sai inji ta yi sanyi. Kece karin kumallo na, ko da na ci abinci in banji muryarki ba yunwa bata sakina. Taba waya akwai dadi amma ni hira dake yafi min dadi. Ko a indiya sai an bincika kamin a samu me kyau irin naki. Bansan akwai mata masu kama da larabawa ba a kasar mu sai da na hadu dake. Bincikena ya kare ban gano mace me kwarjini irin naki ba. Kanshinki na kai ni Duniyar da ban tantance ba. Nasan 'Ya'yanmu zasu zama kyawawa saboda mun dace da juna. Na yi babbar sa'a idan na sameki a matsayin mata, dan kuwa 'ya'yana zasu samu tarbiyya. Hankalinki da nutsuwarki na kara sawa in soki. Kina da kamun kai, kina da girmama mutane, kin iya kalaman soyayya, Allah yawa...

Addu’ar neman gafara ga mamaci

Addu'a
Idan za'a saka mutum a kabari, ana cewa, "Bismillahi, wa ala sunnati Rasulillah" Bayan an kammala binne mamaci, Annabi, Sallalalahu Alaihi Wasallam na cewa ku nemawa dan uwanku gafara. Kuma ku mai addu'ar samun nutsuwa, domin yanzu haka ana mai tambayoyi. Dan haka nemawa wanda ya rasu gafara da tabbatuwar harshensa akan gaskiya yayin tambayar kabari, Sunnah ce. Dan karin bayani, Saurari wannan bidiyon: Allah ya jikan wanda suka rigamu gidan gaskiya. Katanta: Yadda ake sallar gawaKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa: A shafin twitter zaku same mu a @hutudole A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Alamomin ciwon koda da abincin mai ciwon koda

Magunguna
Aikin Koda a jikin dan Adam shine tace datti da ruwan da bai da kyau daga cikin jini, a yayin da ta daina aiki, datti zai taru a jikin mutum. Abubuwan dake kawo cutar koda suna da yawa, amma akwai sauran ciwuka dake kawo cutar, kamar ciwon suga, hawan jini da sauran ciwuka dake dadewa a jikin dan adam. Ciwon koda na saka lalacewar jijiyoyi, da Raguwar karfin kashi, da kuma saka rama. Idan cutar ta yi muni, hantarka ta daina aiki kwata-kwata, saidai a koma inji ya rika wanke maka koda. Ire-ire da kuma Abubuwan dake kawo cutar Koda. Cutar Koda me tsanani: Wannan itace cutar koda da hawan jini yake haddasawa wadda kuma itace aka fi fama da ita. Takan dade a jikin mutum kuma za'a ga kullun lamarin kara munana yake. Hawan jini ta haddasa turawa koda jini da yawa wanda ha...

Addu’ar samun mijin aure da gaggawa

Addu'a
Ga me neman matar aure ko mijin aure, akwai addu'o'i da malamai na sunnah suka kawo wanda ke taimakawa wajan kawo nesa kusa. Addu'a ta farko itace Rabbana Atina Fidduniya hassana wafil Akirati Hassana, wakinna Azabannar. Wannan addu'a ta game kowace irin bukata mutum ke nema a Duniya da Lahira, kuma kusan duk musulmi ya santa amma wani yana ganin kamar ta yi kadan. Malaman Sunnah sun tabbatar da naci da yakini da sakankancewa ana wannan addu'a na kawo biyan bukata. Sai kuma Addu'a ta biyu. Itace "La'ilaha illallahul Azimul halim, La'ilaha illallahul hakimul Karim, La'ilahaillalah, Subhanallah, Rabbissamawatissaba'i wa rabbularshilazim, Alhamdulillahi rabbil alamin" Itama wannan addu'a idan aka haddace ta ana yinta akai-akai tana kawo nesa kusa. Akwai kuma addu'ar la'il...

Addu’ar samun kudi

Addu'a
Kana neman kudi dan aure, gina gida, sayen mota, gina babban gida daya fi wanda kake ciki, sayen kayan sawa, farantawa iyayenka, da dai sauransu? To ga addu'ar samun kudi daga bakin da baya karya, farin jakada, cikamakin annabawa da manzanni, Annabi Muhammadu, Sallallahu Alaihi Wasallam. Wannan addu'a an kawo ta a sunani Tirmizi, da Musnad na Imamu Ahmad. Addu'ar itace "Allahummagfirli Zambi Wawassi'ili fi daari, wa barikli fi rizqi Fassarar addu'ar itace ya Allah ka yafemin zunubaina, ka sa min nutsuwa a gidana, inji na wadata dashi, ka saka min albarka a Dukiyata. Allah ya Arzutamu Duniya da Lahira.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa: A shafin twitter zaku same mu a @hutudole A shafin Facebook zaku samemu a @hutudole...

Alamomin ciwon ulcer

Magunguna
Menene cutar Ulcer? Cutar ulcer ko gyambon ciki, kamar yanda aka fi saninta da Hausa, ciwone dake samuwa a cikin dan adam ko kuma a cikin hanjinsa. Allah ya halicci wata kariya a cikin dan Adam. Kariyarce idan ta samu matsala, sai wasu sinadarai da jikin mutum ke samarwa na sarrafa abinci su ji mada ciwo a ciki ko a hancinsa. Ana iya maganin cutar ulcer cikin sauki. Amma idan aka barta ba tare da kulawa ba, tanawa mutum illa sosai. Abubuwan dake kawo cutar ulcer Abubuwan dake kawo cutar ulcer sun hada da: Cutar da Bakateriya ke sawa. Yawan shan magungunan Aspirin, ibuprofen, da naproxen. A likitance, abinci baya saka ulcer. Alamomin ciwon Ulcer Alamar ciwon ulcer ya danganta da tsananin ciwon. Mafi shaharar alamar ciwon ulcer itace jin zafi a tsakanin kirji ...

Matan shehu ibrahim inyass nawane

Tarihi
Kana da tambayar matan shehu ibrahim inyass nawane? Mafi ingancin amsa itace, matan Shehu Ibrahim Inyass 4 ne. Akwai wasu ikirare-ikirare dake yawo cewa ya auri mata sama da 4 amma mafi ingancin bayani shine matansa 4 ne. Daga ciki kuwa akwai 'yar Najeriya, Sayyada Bilqis wadda 'yar jihar Kogi ce. Akwai kuma sayyada Fatimatou, sai kuma Sayyada Afiyatou, Akwai kuma Sayyida A'isha wadda rahotanni suka bayyana cewa, itace babba a cikin matan nasa. Hakanan wasu rahotanni sun bayyana cewa 'ya'yansa 75, kuma ya rasu yana da shekaru 75, hakanan ya wallafa litattafai 75. Saidai wasu rahotannin sun ce 'ya'yansa 100 kuma ba'a tantance iya yawan litattafan da ya rubuta ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa: A shafin twitter zaku same mu a @hut...

Wuridin kudi nan take

Addu'a
Musulunci ya amincewa mutum ya roki Allah Arzikin Duniya da ya hada da Kudi, Mata ta gari, da sauransu. Tirmizi ya ruwaito daga Sabit, Anas yace, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi waslalam yace "Kowannenku na da damar ya roki Allah dukkan abinda yake so, hadda rokon Allah madaurin takalmi idan ya katse. Albani ya inganta wannan hadisi. Wannan na nuni da cewa komai mutum zai roka ya roki Allah, saidai a nemi Albarka a cikin rayuwar Duniya da dukiyar da kuma Lahira zai fi. Hakanan manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam, ya taba tambayar Abuzar(RA) cewa, Abu Zar me kake tunani game da mutumin da yake da tarin Duniya, zaka kirashi me Arziki? Abu Zar(RA) ya amsa da cewa, tabbas zan kirashi da me Arziki ya Rasulullah. Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam ya sake tambayar ...

Addu’ar biyan bukata cikin gaggawa

Addu'a
Ga kuma kari: Wanda ya farka cikin dare, sai yace: "Lailaha illallah, Wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa ala kullu shai'in qadir, walhamdulillah, wasubhanallahi, walailahaillallahu, wallahu akbar, wala haula wala quwwata illa billah" Sannan yace Allahummagfirli, ko yayi kowace irin Addu'a, Annabi, Sallallahu Alaihi Wasallam yace Allah zai karba masa. Hakanan idan yayi Alwala yayi Sallah to za'a karbi sallarsa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa: A shafin twitter zaku same mu a @hutudole A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Abincin dake sa kiba, Karin kiba cikin sauri

Magunguna
Kuna neman kiba da kuma kara nauyi ta hanyat da bata da ill? A nan zamu zayyano muku kalar abincin da idan kuna ci zaku kara kiba kuma jikinku yayi kyau. Abincin dake sa kiba Ruwan kwakwa: Ruwan kwakwa kofi daya a kullun zai sa mutum yayi kiba kuma ya sami nauyin jiki. Yagwat(Yogurt): Shan Yagwat me kyau na sa kiba da kuma gyara jiki. Fruit salad: Hada kayan marmari waje daya a yi juice dinsu yana sanya a samu kiba me kyau. Ice cream. Pizza Doughnuts Potato chips Chocolate Soyayyen dankalin turawa. Burger Fried rice Kaji Kwai Talo-talo Madara Wake Madarar waken suya Karin kiba cikin sauri Idan kuma ana neman karin kiba cikin sauri to ga abincin da za'a rika ci. Saidai a kiyaye shan magani, saboda yawanci wuna da illa. Karin k...