Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yayi murnar samun jika.
Ya wallafa hotunan bikin suna da aka yi na jikar tasa.
inda yayi mata Addu'a.
Rahotanni sun bayyana cewa, 'Yansanda a babban birnin tarayya, Abuja sun kama dan fafutuka kuma me rajin kare hakin bil'dama, Omoyele Sowore.
An kamashi ne a yayin da yake fitowa daga cikin babbar kotun tarayya dake Abuja inda akewa Nnamdi Kanu shari'a.
Rahoton yace 'Yansandan sun saka Sowore a gaba yayin da yake fitowa daga Kotun inda suka ce su wuce office.
Bayan da aka yi tirka-tirka Sowore dai ya yadda an tafi dashi.
Wani na kusa da Sowore yace dama can 'yansandan sun gayyaceshi amma Azarbabin sune yasa suka zo kamashi.
Gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya baiwa mutanen jiharsa shawarar su tashi tsaye su kare kansu.
Yace matsalar garkuwa da mutane dan neman kudin fansa a jihar ya kai matakin yaki inda yace dole sai an tashi tsaye.
Gwamnan yace, ba zai biya kudin fansa ba kuma babu maganar sulhu da 'yan Bindigar yace idan aka rika basu kudi, zasu mayar da abin kasuwanci.
Gwamna Bago yace kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowane dan kasa damar kare kansa da Dukiyarsa.
Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy ya fara zaman gidan yarin da aka yanke masa na tsawon shekaru 5.
An sameshi da laifi ne na karbar kudin yakin neman zabe ba ta hanyar data dace ba.
Wannan dauri da aka masa shine irinsa na farko a tsakanin shuwagabannin kasar ta faransa a cikin shekarun bayabayannan.
Kalli Bidiyon anan
https://www.youtube.com/watch?v=IEWMOqQs2pU?si=wl8g-yvmNRBuwenW
Rikicin cikin gida ya kunno kai a kungiyar Izala.
Malam Ibrahim Matayassara ne ya fito ya ce yana jawo hankali ga Farfesa Sheikh Sani Rijiyar Lemu da cewa ya rika girmama malamai na zamaninsa ya daina tunanin shine ya fi owa ilimi.
Sannan Yace shi fadakarwa ce yayi ga Sheikh Rijiyar Lemu ba rashin kunya ba.
https://www.tiktok.com/@isah_bello_assalafy_garo/video/7563743936150310164?_t=ZS-90m2FmtZd9l&_r=1
Saidai lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu malamai suka fito suka yi Allah wadai da wadannan kalamai nasa
https://www.tiktok.com/@sheikmurtala01/video/7564029374526196999?_t=ZS-90m1xKLFhJo&_r=1
Bidiyo ya bayyana inda aka ga yanda akawa Maiwushirya da 'YarGuda Gwaji a Asibiti a ci gaba da shirin aurensu.
https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7564102158837091604?_t=ZS-90m17FI9oP3&_r=1
Hakanan an ga sun je ofishin shugaban Hisbah na Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa inda ya fati matakan da za'abi a kai ga auren.
Kotu dai tace nan da kwana 90 za'a daura auren.
Bidiyon abin kunyar da ya faru a jihar Ogun na ta yawo a kafafen sadarwa inda aka ga 'yan Najeriya na rokon 'yan kwallon kafar kasar Africa ta Kudu abinci.
'Yan kwallon wanda suka je filin kwallo na MKO Abiola dake Abeokuta dan wasa da Remo Stars sun rika jefawa 'yan Najeriyar sauran abincin da suka ci suka rage.
Da yawa dai sun yi Allah wadai da mutanen.
Kalli Bidiyon anan
https://www.youtube.com/watch?v=cq1Y4xEJEDo?si=MlWRJFlqZGtx8RYH
Tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo me ritaya tare da dansa, Brigadier General Adeboye Obasanjo kenan a wannan hoton.
Hoton ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda akai ta sam barka
Tauraruwar Tiktok, Habiba Dorayi ta fito ta bayar da hakuri game da Bidiyon ta na batsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta.
Habiba a Bidiyon data wallafa a shafinta na Tiktok tace hukumar tace fina-finan Kano ta nusar da ita cewa abinda ta yi bai dace ba.
Tace dan haka tana baiwa duk masoyanta hakuri kuma hakan ba zai sake faruwa ba.