Monday, December 15
Shadow
Kasar Nijar ta koro ‘yan Najeriya 294 gida

Kasar Nijar ta koro ‘yan Najeriya 294 gida

Duk Labarai
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta ce ta sake karɓar 'yan ƙasar 294 a ranar Litinin da aka kwaso daga maƙwabciyarta Jamhuriyar Nijar. Wata sanarwa daga hukumar ta ce jirgi biyu ne ya kwaso mutanen daga garin Agadez na Nijar zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ne da ke Kano bayan sun maƙale a can. Ta ce jirgin farko ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:30 ɗauke da mutum 148, na biyun kuma ya sauka da mutum 146 da misalin ƙarfe 4:29 na yamma. Bayanai sun nuna akasarin mutanen kan maƙale ne bayan yin zango a Agadez yayin da suke kan hanyarsu ta kaiwa ƙasashen Aljeriya ko Libya ko kuma nahiyar Turai. Ƙungiyoyin bayar da agaji na ƙasashen duniya ne ke taimakawa tare da hadin gwiwar gwamnati wajen mayar da su gida a jirgi.
Dalla-Dalla Ji Dalilin da ya sa Ganduje bai je tarɓar Tinubu ba a Kano

Dalla-Dalla Ji Dalilin da ya sa Ganduje bai je tarɓar Tinubu ba a Kano

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje bai je tarɓar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba a Kano ranar Juma’a saboda balaguron da ya yi zuwa birnin Landan, a cewar makusancinsa Muhammad Garba. Ganduje wanda ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a watan Yuni ya shirya tafiyar ne kwana biyar kacal da saukarsa daga muƙamin, kamar yadda Muhammad Garba ya bayyana cikin wata sanarwa a yau Asabar. Tinubu ya je Kano ne domin yin ta’aziyyar attajiri Aminu Ɗantata da ya rasu a ƙarshen watan Yuni, kuma rashin ganin Ganduje a wurin ya jawo cecekuce tsakanin magoya baya da ‘yan’adawa a jihar. “Ba kamar abin da ake yaɗawa ba cewa da gangan ya ƙi zuwa ko kuma ba shi da lafiya, Ganduje ya je Landan ne saboda tafiyar da aka shirya da daɗewa tun kafin ziyarar,” in ji sanarwar. ...
Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Duk Labarai
Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar ta'aziyya ofishin jakdancin Najeriya da ke birnin Monrovia domin jajanta rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Yayin ziyarar tasa a ranar Laraba, Mista Boakai ya sanya hannu kan rajistar makoki a ofishin bayan ya samu tarɓa daga jakadan Najeriya R.O Mohammed. Alaƙar Najeriya da Laberiya na da tarihi sosai. A shekarun 1990, Najeriya ta tura sojojinta domin kawo ƙarsen yaƙin basasar ƙasar.
Rundunar ‘yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar ‘yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Peter Obi, ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2023. An shirya tattakin ne domin yin bikin murnar cika shekara 64 da haihuwar Mista Obi. Mai magana da yawun rundunar DSP Mansir Hassan ya ce bayanai sun nuna cewa akwai wasu "miyagu da ke shirin fakewa da gangamin domin haddasa fitina" a jihar. DSP ya ce rundunar ta dakatar da duk wani taron jama'a mai kama da na siyasa har sai "lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓe a hukumance kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa Inec ta tsara". A cewar sanarwar: "Yayin da ake gudanar da zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyu a ranar da magoya bayan Obi suka tsara gangamin, rundunar 'yansandan Kaduna na ganin hakan zai haddasa rikici a wu...
Kalli Bidiyo: Bayan rashin Buhari, Alaramma Ahmad Sulaiman ya masa Addu’ar Samun Rahama wajan Allah

Kalli Bidiyo: Bayan rashin Buhari, Alaramma Ahmad Sulaiman ya masa Addu’ar Samun Rahama wajan Allah

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"transform":1,"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Babban Alaramma, Ahmad Sulaiman ya yiwa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari addu'ar neman gafara. Ko da a baya kamin ya ci zabe, Alaramma Ahmad Sulaiman ya yiwa tsohon shugaban kasar addu'o'in Nasara. https://www.tiktok.com/@sobman_fans_pantami/video/7527815001994743046?_t=ZM-8y9fwFat3ZA&_r=1
Kalli Bidiyo: Burina shine idan Allah ya min cikawa a kaini Daura a Binne kusa da kabarin Masoyina Buhari>>Inji Wannan matashiyar

Kalli Bidiyo: Burina shine idan Allah ya min cikawa a kaini Daura a Binne kusa da kabarin Masoyina Buhari>>Inji Wannan matashiyar

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"transform":1,"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Wata matashiya masoyiyar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari ta bayyana cewa ita burin ta shine idan ta rasu a kaita a binne kusa da kabarin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Daura. Ta bayyana cewa, Gaskiyarsa da sauran nagartarsa ce tasa take sonshi. https://www.tiktok.com/@salzee23/video/7527811179436084487?_t=ZM-8y9exmW3tNY&_r=1
Kalli Bidiyon yanda aka lakadawa wata data yi murnar rashin Shugaba Buhari na jaki sannan aka kaita Ofishin ‘yansanda

Kalli Bidiyon yanda aka lakadawa wata data yi murnar rashin Shugaba Buhari na jaki sannan aka kaita Ofishin ‘yansanda

Duk Labarai
Rahotanni nata yawo cewa, an kama Sister Zeerah shahararriyar 'yar Tiktok kuma 'yar Shi'a da ta yi murna da mutuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Bidiyo dake ta yawo na cewa, wata ce ta hadu da ita suka yi fada akan murnar mutuwar Buhari da ta yi sannan aka kaita ofishin 'yansanda. Kwana biyu ba'a ga ta hau Tiktok ba amma daga baya ta dawo. https://www.tiktok.com/@sdikko3/video/7528380316214496568?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7528380316214496568&source=h5_m&timestamp=1752917225&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm...
Kalli Subhanallahi Ana ta yada Bidiyon kirkira na AI dake nuna wai shugaba Buhari yayi mummunan karshe, Saidai mutane nata Allah wadai da fadar cewa hukuncin bawa na ga mahaliccinsa

Kalli Subhanallahi Ana ta yada Bidiyon kirkira na AI dake nuna wai shugaba Buhari yayi mummunan karshe, Saidai mutane nata Allah wadai da fadar cewa hukuncin bawa na ga mahaliccinsa

Duk Labarai
Wasu makiyan tsohon shugaba kasa, Marigayi Muhammadu Buhari na ta yada Bidiyon dake nuna cewa wai yana wuta. Bidiyon na nuna tsohon shugaban kasar yana tafiya zuwa cikin wuta ne. Saidai da yawa sun yi Allah wadai da hakan inda suke cewa, hakan bai dace ba dan hisabin bawa na ga mahaliccinsa babu wanda ya sani. Kalli Bidiyon anan https://www.tiktok.com/@don_freex/video/7527762758939495736?_t=ZM-8y9cFoF4A7E&_r=1