Sunday, December 21
Shadow
Hukumar ‘yansandan Najeriya ta yi magana kan dansandan da aka ga matasa na Dùqànsà saboda zargin yayi sàtà

Hukumar ‘yansandan Najeriya ta yi magana kan dansandan da aka ga matasa na Dùqànsà saboda zargin yayi sàtà

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya ta yi magana kan dansandan da aka ga ana dukan sa akan titin Legas bisa zargin sata. Me magana da yawun 'yansandan jihar Legas, Abimbola Adebisi ne ya bayyana cewa suna bincike kan lamarin. Bidiyon ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga dansandan jina-jina matasa na dukansa suna kiransa ds Barawo.
Mun gana da Kiristoci da ke zaune a sansanin ‘yan gudun Hijira ba zamu kyale Fulani da suka sakasu a wannan halin ba dole mu dauki mataki akansu>>Inji ‘yan majalisar kasar Amurka da suka kawo ziyara Najeriya

' Yan majalisar kasar Amurka da suka kawo ziyara Najeriya wanda Riley Moore ya musu jagora sun ce sun gana da Kiristoci da aka yiwa cin zarafi a jihar Benue. Sun ce sun gan su a matsayi na rashin tabbas wanda suka zargi Fulani da jefasu a ciki. Riley yace ba zasu zuba ido suna ganin irin wannan abuba, dole zasu dauki mataki. Yace ya ji labarai masu tayar da hankali da 'yan Gudun Hijirar suka gaya masa wadanda ba zai taba mantawa dasu ba.
Kaso 35 cikin 100 na ruwan Najeriya ne kadai sojojin ruwa suke iya tsarewa, sauran Kamfanoni masu zaman kansu aka dauka aka baiwa kwangilar aikin>>Inji Sowore

Kaso 35 cikin 100 na ruwan Najeriya ne kadai sojojin ruwa suke iya tsarewa, sauran Kamfanoni masu zaman kansu aka dauka aka baiwa kwangilar aikin>>Inji Sowore

Duk Labarai
Dan Gwagwarmaya kuma dan siyasa, Mawallafin Jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, Sojojin Ruwan Najeriya kaso 35 cikin 100 ne kawai na ruwan Najeriya suke iya tsarewa. Ya bayyana cewa, sauran wasu kamfanoni ne masu zaman kansu aka baiwa suke kula da tsaron ruwan kasar. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi inda yake magana akan gazawar jami'an tsaron Najeriya. https://twitter.com/OzorNdiOzor/status/1998731226077692252?t=uOX7B2O65QJm4gFoSh5x4g&s=19
Kalli Bidiyon: An kawo mana ‘yan Ìskàn yara da basu da kishi, Next season duk sai mun koresu>>Ali Jita ya magantu kan halin da Real Madrid ke ciki

Kalli Bidiyon: An kawo mana ‘yan Ìskàn yara da basu da kishi, Next season duk sai mun koresu>>Ali Jita ya magantu kan halin da Real Madrid ke ciki

Duk Labarai
Tauraron mawakin Hausa, Ali Jita ya bayyana cewa Yanzu Real Madrid yara ne aka tara marasa kishi. Ya bayyana cewa Allah jika su Ronaldo, Bezema ba dan sun mutu ba. Yace nan da Next Season, watau kakar wasa me zuwa sai sun kori 'yan wasan. https://www.tiktok.com/@realalijita/video/7582305495566929170?_t=ZS-927sn3cYLdQ&_r=1
Idan dai shugaba Tinubu da gaske yake kan maganar janyewa manyan mutane ‘yansanda masu basu tsaro to ya fara da dansa, Seyi Tinubu >>Inji Bulama Bukarti

Idan dai shugaba Tinubu da gaske yake kan maganar janyewa manyan mutane ‘yansanda masu basu tsaro to ya fara da dansa, Seyi Tinubu >>Inji Bulama Bukarti

Duk Labarai
Lauya kuma dan Gwagwarmaya Bulama Bukarti ya bayyana cewa idan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da gaske yake kan maganar janyewa manyan mutane 'yansandan dake basu Kariya to ya fara da janyewa dansa, Seyi Tinubu. Ya bayyana hakanne a matsayin karin haske kan maganar da farfesa, Wole Soyinka yi akan sojojin dake baiwa da shugaban kasar kariya inda yace sun yi yawa. Bukarti yace maganar farfesa Wole Soyinka maganace akan gyaran tsarin tsaro da ya lalace inda yayi kira ga Gwamnatin Tinubu kada ta ji haushin maganar. https://twitter.com/bulamabukarti/status/1998836451136422096?t=JHt1QCW7a4saM6tfLw-kIQ&s=19
Kalli Bidiyon yanda matasa suka lakadawa wani Dansanda na Jàkì saboda zargin yayi sàtà

Kalli Bidiyon yanda matasa suka lakadawa wani Dansanda na Jàkì saboda zargin yayi sàtà

Duk Labarai
Wasu matasa a Legas sun lakadawa wani dansandan Najeriya dukan kawo wuka bisa zargin yayi sata An ga dansandan jina-jina inda matasan ke daukarsa Bidiyon suna kiransa da Ole, watau Barawo kenan da yarbanci. Sannan an ga wani abokin aikina na kokarin tseratar dashi. https://twitter.com/General_Somto/status/1998817572041732284?t=PeDgjrGuYfKxcAyhAG8h_A&s=19
Kalli Bidiyon da Hotunan katafaren gidan da Malam Aminu Saira Daraktan Labarina ya gina

Kalli Bidiyon da Hotunan katafaren gidan da Malam Aminu Saira Daraktan Labarina ya gina

Duk Labarai
Wadannan hotunan gidan Daraktan fim din Labarina Watau Malam Aminu Saira ya gina kenan. Da yawa sun rika masa fatan Alheri. Gidan dai ba'a dade da kammalashi ba. https://www.tiktok.com/@mailafiyasairamovies/video/7581905158234213650?_t=ZS-927DshsFYrR&_r=1 https://www.tiktok.com/@abdullahihussai18/video/7581988431861943572?_t=ZS-927DlJ5eBOa&_r=1 https://www.tiktok.com/@abdullahihussai18/video/7581952096686116116?_t=ZS-927CqPqOx2v&_r=1
Kalli Bidiyon: An jiyo Peter Obi na cewa Musulman Najeriya mabarata ne, kuma bara wani sashe ne na Musulunci

Kalli Bidiyon: An jiyo Peter Obi na cewa Musulman Najeriya mabarata ne, kuma bara wani sashe ne na Musulunci

Duk Labarai
Wani Bidiyon dan takarar shugaban kasa a zaben shakerar 2023 a jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya bayyana inda aka jishi yana cewa Almajiranci da bara na musulmai be Sannan ya alakanta addinin Musulunci da bara Saidai yace Almajirai da suke yawo a tituna zasu iya zama ma'aikata a kamfanoni. Saidai wadannan kalamai sun jawo masa suka sosai a kafafen sadarwa. https://www.tiktok.com/@the_nigerianist/video/7581865063154273554?_t=ZS-927AMNopeoi&_r=1 https://twitter.com/HighChiefOkoro/status/1998776191470227481?t=bi0NiPvyM20SyAUFuDFVNQ&s=19
Shuwagabannin Najeriya ne suka samar da matsalar tsaron da ake fama ita kuma duk randa suka ga dama sune zasu magance ta>>Inji Sheikh Zakzaky

Shuwagabannin Najeriya ne suka samar da matsalar tsaron da ake fama ita kuma duk randa suka ga dama sune zasu magance ta>>Inji Sheikh Zakzaky

Duk Labarai
Malamin Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayyana cewa, Gwamnati ce ta kawo matsalar tsaro Najeriya kuma itace zata magance matsalar idan ta ga dana. Ya bayyana hakane yayin wata Hira da 'yan Jarida suka yi dashi. Yace ta yaya fulani dake daji suna kiwon dabbobi suka samu Bindigu da motocin sulke irin na soji? https://twitter.com/dammiedammie35/status/1998798879412859303?t=MZbwGkuoUg1pK7TjG4C8FA&s=19
Ko a Mafarki ban taba Tunin za’a janye min ‘yansandan dake bani tsaro ba>>Sanata Ningi

Ko a Mafarki ban taba Tunin za’a janye min ‘yansandan dake bani tsaro ba>>Sanata Ningi

Duk Labarai
Sanata Ahmad Ningi ya bayyana cewa, Bai taba Tunanin cewa wata rana za'a wayi gari a janyewa Sanatoci jami'an tsaron 'yansanda dake basu kariya ba. Yace abin takaici shine ga mawaka, 'ya'yan 'yan siyasa, da sauran wadanda basu kamata ba har yanzu 'yansanda na take musu baya. Yace indai an janye musu masu take musu baya, to kamata yayi suma Gwamnoni da Ministoci da shugaban kasa duk a janye musu masu take musu baya. https://twitter.com/dammiedammie35/status/1998777385500410294?t=BmhI3Cz7YiAIekZI-kHqTA&s=19