Monday, December 15
Shadow
Kasar Saint Lucia ta girmama shugaba Tinubu

Kasar Saint Lucia ta girmama shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kasar Saint Lucia ta girmama shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da lambar girmamawa mafi girma a kasar. Hakan ya farune yayin da shugaba Tinubu ke ziyarar aiki a kasar kuma an karramashi ne dan kokarinsa wajan kyautata zumunta tsakanin kasashen biyu. Ba kasafai kasar Saint Lucia ke baiwa kowa wannan kyautar karramawar ba wanda hakan ke nuna muhimmancin da shugaba Tinubu ke dashi a wajansu.
Matatar man fetur ta Fatakwal ta dawo aiki

Matatar man fetur ta Fatakwal ta dawo aiki

Duk Labarai
An barke da murna a Eleme dake Birnin Fatakwal na jihar Rivers bayan ganin wutar matatar man fetur dake garin na ci balbal. Lamarin ya farune ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu na shekarar 2025, wasu rahotanni na cewa, ana gwajin matatar man fetur dinne. 'Yan kasuwar man fetur dake kusa da matatar sun ce alamace matatar man fetur din na daf da dawowa da aiki dan ana kwacin ta ne. Rahotanni sun ce fiye da dala Biliyan 1 ne gwamnatin tarayya ta kashe Akan gyaran matatar man fetur din tun daga shekarar 2021 zuwa yanzu.
Kalli Bidiyon yanda manomi ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta a jihar Kebbi

Kalli Bidiyon yanda manomi ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta a jihar Kebbi

Duk Labarai
Wani manomi a jihar Kebbi me suna Kabiru Kamba ya ce ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta amma bata mutu ba a gona. An binne jaririyar a gonarsa dake Kamba karamar hukumar Dandi dake jihar. Ya bayyana hakane ga tawagar hukumar yaki da cin zarafi ta jihar da ta kai masa ziyara gida. Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito cewa, tsohuwar babbar sakatariya a jihar, Hajiya Rafa’atu Hammani.ce ta jagoranci tawagar zuwa gidan Kabiru. Yace a ranar da lamarin ya faru ya je gona sai yaga kunya wadda bai san da ita ba kuma ta yi sama sosai Yace anan ya kira mutane suka tayashi suna tonawa sai suka ga jaririya. Yace sun sanar da 'yansandan kusa da gurin inda yace kuma ya dauki yarinyar zai rike kuma an yi sa'a ma matarsa ta haihu dan haka ba za'a sam...
An Samu Mace Ta Farko Da Ta Kai Matakin Farfesa A Bangaren Haɗa Magunguna A Arewacin Nijeriya

An Samu Mace Ta Farko Da Ta Kai Matakin Farfesa A Bangaren Haɗa Magunguna A Arewacin Nijeriya

Duk Labarai
An Samu Mace Ta Farko Da Ta Kai Matakin Farfesa A Bangaren Haɗa Magunguna A Arewacin Nijeriya. Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria Ta Ɗaga Likkafar Hajia Hadiza Usman Ma'aji Zuwa Matsayin Farfesa Akan Haɗa Magunguna Na Clinical Pharmacy, Wadda Ita Ce Mace Ta Farko A Arewacin Najeriya Da Ta Kai Wannan Matakin. Wace Irin Fata Za Ku Yi Mata? Daga Jamilu Dabawa
WATA SABUWA: Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah

WATA SABUWA: Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah

Duk Labarai
Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah. Cikakken rahoto na nan tafeA Dimokuraɗiyya
Peter Obi: Sau daya kacal zan yi mulki idan aka zabeni shugaban kasa>>Peter Obi

Peter Obi: Sau daya kacal zan yi mulki idan aka zabeni shugaban kasa>>Peter Obi

Duk Labarai
Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ya shirya yin wa’adin shekara huɗu kacal idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027. Obi, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir el-Rufai, na shirya kafa kawance domin ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027. Da yake magana a wata tattaunawa ta “Twitter Space” da Parallel Facts suka shirya a ranar Lahadi, Obi ya ce duk wani ɗan takara daga kudancin Najeriya da aka zaɓa shugaban ƙasa a 2027 dole ya kasance cikin shiri ya sauka daga mulki ranar 28 ga Mayu, 2031, bisa abin da ya kira “yarjejeniya marar rubutu” da kuma tsarin rabon mulki. Ya ƙara da cewa tsarin rab...
Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka tarwatsa taron jam’iyyar PDP a Abuja duk da musanta rufe ofishin jam’iyyar da suka yi

Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka tarwatsa taron jam’iyyar PDP a Abuja duk da musanta rufe ofishin jam’iyyar da suka yi

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana wanda ya nuna 'yansanda a wajan taron jam'iyyar PDP inda rahotanni suka ce sun tursasawa 'yan jam'iyyar ficewa daga taron. https://twitter.com/thecableng/status/1939708148878884974?t=GCP_zgMmmcYiHVEPqmoTtA&s=19 A baya dai hukumar 'yansandan ta musanta cewa, ta kulle ofishin jam'iyyar PDP din.
Allah Sarki Kalli Bidiyon yanda aka cire hoton Ganduje daga ofishin APC ana maye da hoton sabon shugaban jam’iyyar

Allah Sarki Kalli Bidiyon yanda aka cire hoton Ganduje daga ofishin APC ana maye da hoton sabon shugaban jam’iyyar

Duk Labarai
A yayin da aka nada shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC bayan saukar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi. An ga Bidiyon yanda aka cire hoton Ganduje daga ofishin shugaban jam'iyyar aka mayeshi da na sabon shugaban jam'iyyar. https://twitter.com/INYAMURI/status/1939643637438267642?t=Pr0LkVz9nZOIaHCfud-I6A&s=19 Duniya kenan kowa da zamaninsa.