Tuesday, December 16
Shadow
Bidiyo: Mansurah Isah ta bayyana yanda ta tsira daga hannun ‘yan damfara

Bidiyo: Mansurah Isah ta bayyana yanda ta tsira daga hannun ‘yan damfara

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana yanda ta tsira daga hannun 'yan Damfara. Mansurah tace wani yaro ya je gidanta inda ya rubuta sunanta a jikinsa da sunan cewa, wai yana sonta, yana son ta taimaka masa. Saidai tace ta kai maganar wajan 'yansanda inda aka mayar da yaron Bauchi saboda yace daga kauyen Bauchi ya fito, tace ta yi yunkurin tallafawa yaron inda tace a tambayo kudin makarantar Bokonsa da Arabi. Tace amma sai akance wai makarantar Arabi ana biyan Naira dubu 70 duk wata ita kuma Boko ana biyan Dubu 150 duk wata. Mansurah tace data ga abin nasu damfara ne sai kawai ta ce a bar maganar ta daina kulasu. Tace kwatsam sai gashi kuma ta ga yaron wai ya rubuta sunan Lilin Baba a jikinsa. Mansurah tace Allah ya ceceta. Kalli Bidiyon ta: https://...
David Mark zai shagabanci jam’iyyar ADC ta hadakar ‘yan adawa

David Mark zai shagabanci jam’iyyar ADC ta hadakar ‘yan adawa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon kakakin Majalisar Dattijai, Sanata David Mark ne ake sa ran zai jagoranci Jam'iyyar hadaka ta 'yan Adawa watau ADC. Ana tsammanin nan gaba kadanne hadakar 'yan adawar zasu bayyana ADC a matsayin jam'iyyar da zasu yi amfani da ita wajan kalubalantar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 kuma David Mark ne zai zama shugaban jam'iyyar na rikon kwarya. Rahoton yace hadakar 'yan adawar ta hada da Atiku Abubakar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Rotimi Amaechi, da Peter Obi. Jaridar Punchng tace David Mark ya amince ya zama shugaba jam'iyyar ta ADC. Rahoton yace hadakar 'yan adawar na neman wanda zai zama sakataren jam'iyyar tasu bayan da Rauf Aregbesola, da Senator Ben Obi suka ki amincewa da tayin zama sakataren jam'iyyar. Ana ts...
Har Yanzu Akume Ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cewar Fadar Shugaban Ƙasa

Har Yanzu Akume Ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cewar Fadar Shugaban Ƙasa

Duk Labarai
Har Yanzu Akume Ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cewar Fadar Shugaban Ƙasa. Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu wani canji da aka yi game da matsayin Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF). A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin bayani da dabarun yada labarai, ya fitar a yau Asabar, an bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda a halin yanzu yake Saint Lucia bai yi wani sabon nadin mukami ba. Sanarwar ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da labarai cewa an sauke Sanata Akume daga mukaminsa, tana mai cewa wannan labari ƙarya ne da aka kirkira don cimma wata manufa. Fadar Shugaban Ƙasar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da irin wadannan jita-jita da basu da t...
Gwamnatin Tarayya zata samar da sabbin ofisoshin ‘yansanda masu kayan aiki sosai

Gwamnatin Tarayya zata samar da sabbin ofisoshin ‘yansanda masu kayan aiki sosai

Duk Labarai
Newly deployed Nigerian Formed Police Unit (FPU) personnel under the African Union Mission in Somalia (AMISOM) arrive at Aden Abdulleh International Airport, Mogadishu, Somalia on January 6, 2016. AMISOM Photo / Ilyas Ahmed Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin samar da ofisoshin 'yansanda masu isassun kayan aiki a fadin Najeriya. Gwamnatin ta sanar da cewa za'a yi hadaka ne tsakanin ma'aikatun Gwamnati da hukumar kula da 'yansanda. Rahoton yace za'a samar da ofisoshin da za'a zubawa kayan aiki na zamani.
Kungiyar dattawan Arewa sun nemi shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaron Arewa

Kungiyar dattawan Arewa sun nemi shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaron Arewa

Duk Labarai
Kungiyar dattawan Arewa ta NEF sun nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ayyana dokar ta baci akan matsalar tsaron Arewa. Kungiyar dattawan sun kuma yi Allah wadai da kisan sojoji 20 a kananan hukumomin Bangi, Mariga dake Jihar Naija. A sanarwar da kakakin kungiyar, Prof Abubakar Jiddere ya fitar, yace kisan sojojin alamace ta rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Yace irin wannan hari alamace ta kaddamar da yaki akan Najeriya da 'yan ta'addar suka yi.
Talauci da rashin tsaro na iya barazana ga zaɓen 2027 – Rahoto

Talauci da rashin tsaro na iya barazana ga zaɓen 2027 – Rahoto

Duk Labarai
Ƙungiyar fafutikar kare haƙƙin ɗan'adam da tabbatar da dimokuraɗiyya ta YIAGA Africa ta ce babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027 na fuskantar barazana saboda ƙaruwar talauci da rashin tsaro a ƙasar. YIAGA ta bayyana haka ne a Abuja a lokacin da take gabatar da rahoton bincikenta, inda daraktan ƙungiyar, Samson Itodo ya ce talaucin da ya wa ƴanƙasar katutu zai iya jawo ƙaruwar sayen ƙuri'a a zaɓen, musamman ta hanyar amfani da abinci domin sayen ƙuri'a. Ya ce, "wannan zaɓen akwai alamar a yi amfani da kuɗi sama da zaɓukan baya. Yanayin talauci da yunwar da ƴanƙasar ke ciki zai sa a samu sauƙin sauya tunanin masu zaɓe," in ji shi, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito. Rahoton ya ƙara da cewa maimakon matsin tattalin arzikin da ƙasar ke ciki ya sa mutane su fusata su ...
Tsohuwar Ajiya, Ji Amsar da marigayi Aminu Dantata ya bayar da aka nemi ya tsaya takarar shugaban kasa

Tsohuwar Ajiya, Ji Amsar da marigayi Aminu Dantata ya bayar da aka nemi ya tsaya takarar shugaban kasa

Duk Labarai
Duk da cewa Aminu Ɗantata ya fi shahara a fannin kasuwanci da kuma tallafa wa jama'a, ya kuma taɓa harkokin siyasa tun daga shekarun 1963. Ya taɓa zama ɗanmajalisar wakilai a tsohuwar jihar Kaduna na wa'adi ɗaya lokacin Jamhuriya ta Farko daga 1963 zuwa 1966. Bayan kifar da gwamnatin farar hula ta lokacin ne kuma ya koma Kano, inda gwamnan mulkin soja Audu Bako ya naɗa shi kwamashinan harkokin kasuwanci a 1968. Ɗantata ya ce yayin da ake shirin shiga Jamhuriya ta Biyu, sai wasu mutane da dama suka fara neman ya tsaya takarar shugaban ƙasa. Wasu kuma sun nemi ya tsaya takarar gwamnan Kano, cikinsu har da tsohon ɗan gwagwarmaya kuma ɗansiyasa Mallam Aminu Kano. Sai dai bai amince da kiran nasu ba. "Dalilin da ya sa na ƙi yarda shi ne, a matsayina na ɗankasuwa ina ganin Allah y...
Ni Na Yì Aikì Aka Kori Ganduje Daga Shugabancin APC, Da Taĺò-Ťàĺo Ma Na So Na Mayàŕ Da Shì Aka Ba Ni Hakuri, Inji Wani Malami Dan Jihar Borno

Ni Na Yì Aikì Aka Kori Ganduje Daga Shugabancin APC, Da Taĺò-Ťàĺo Ma Na So Na Mayàŕ Da Shì Aka Ba Ni Hakuri, Inji Wani Malami Dan Jihar Borno

Duk Labarai
Ni Na Yì Aikì Aka Kori Ganduje Daga Shugabancin APC, Da Taĺò-Ťàĺo Ma Na So Na Mayàŕ Da Shì Aka Ba Ni Hakuri, Inji Wani Malami Dan Jihar Borno. Wannan Malami dan asalin jihar Borno ya ce ya so mayar da tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje tàlò-tàĺì amma aka ba shi hakuri. Malamin ya ce duk wanda ya ce zai taba Kashim Shattima to lallai za su saka kafar wando daya da shi. Hakazalika, malamin ya gargadi mataimakin shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Barau Jibril da ya shiga taitayinsa, idan kuma ba haka ba zai mayar da shi Ràķùmin daji. Daga S-bin Abdallah Sokoto