Ku Daina Ɗaukar Abin Da Gwamnoninku Suke Muku Kamar Alfarma Ce, Ko Taimakonku Suke, Haƙƙinku Ne, Cewar Barista Ɗantani
Fitattaccen lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya, Barista Hamza Nuhu Ɗantani, ya ja hankalin al'umma da su daina kallo ko ɗaukan abubuwan da ƴan siyasa ko shugabanni suke musu a matsayin taimako ko wata alfarma domin ba da kuɗinsu suke yin ayyukan ba.
Barista Ɗantani wanda ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito, ya fara ne da cewa, "Ba fa noma ko wani aiki suka yi aka biya su suke muku aiki da kuɗin ba! Ba Kuɗinsu ba ne! Ba Dukiyarsu Ba ce! Ba Guminsu ba ne! Su da kansu suka fito suka roƙe ku don ku zaɓe su! Suka dinga manna hotunansu (Posters), suna ta ihu suna shiga lungu da saƙo suna barar ƙuri’unku don kawai su riƙe amanar Dukiyarku!". Inji shi.
Barista Ɗantani, ya ci gaba da cewa, "Ku sani Haƙƙinku ne, ba fa kuɗinsu ba ne, ba du...







