Tuesday, December 23
Shadow
Shugaba Tinubu ya zo na 3 a cikin shuwagabannin kasashen Duniya da suka fi rashawa da cin hanci

Shugaba Tinubu ya zo na 3 a cikin shuwagabannin kasashen Duniya da suka fi rashawa da cin hanci

Duk Labarai
An bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban kasa na 3 mafi rashawa da cin hanci a Duniya. Wata Kungiya me sunan Organized Crime and Corruption Reporting Project (OCCRP) ce ta bayyana hakan. Kungiyar tace ta nemi a mika mata sunayen mutane da 'yan Jarida da shuwagabannin Duniya dan tantance wannan batu. Shugaban Kenya, William Ruto ne ya zo na daya sai shugaban kasar Indonesia,Joko Widodo ne ya zo na biyu shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya zo na 3.
Na talauce bani da kudi, kuma na sauka daga shugabancin Najeriya da mutunci na saboda ban karbi cin hanci gurin kowa ba>>Tsohon Shugaban kasa, Buhari

Na talauce bani da kudi, kuma na sauka daga shugabancin Najeriya da mutunci na saboda ban karbi cin hanci gurin kowa ba>>Tsohon Shugaban kasa, Buhari

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya talauce bashi da kudi. Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Garba Shehu inda ya kara da cewa kuma ya sauka daga mulki da mutuncinsa saboda bai karbi cin hanci daga girin kowa ba. Garba Shehu ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai a yayin da yake kaddamar da wani littafi kan irin abinda ya fuskanta lokacin yana aiki da shugaban kasa. Garba yace dalilin da yasa shugaba Buhari baya hira da 'yan jaridu sh...
Dan an kawo mana hari, sojoji tserewa suke>>Wani Basaken kauye ya koka

Dan an kawo mana hari, sojoji tserewa suke>>Wani Basaken kauye ya koka

Duk Labarai
Basaraken kauyen Yashikira dake karamar hukumar Baruten, a jihar Kwara, Amb (Dr) Alhaji Umar Sariki Usman, ya bayyana cewa da an kai kusu hari sai sojoji su tsere su barsu. Basaraken ya nuna damuwa kan yanda sojojin da aka kai musu basa iya basu kariya. Ya bayyana cewa, duk da alkawarin gwamnati na kai karin jami'an tsaro amma har yanzu ba'a kai ba. Yace 'yan bangansu da basu da makamai masu kyau sune suke fuskantar 'yan Bindigar. Yace sojojin da aka kai musu basu da kwarewar aiki kuma basu da kayan aiki masu kyau.
Da Duminsa: An sake daga jana’izar Aminu Dantata

Da Duminsa: An sake daga jana’izar Aminu Dantata

Duk Labarai
Bayanai daga makusantan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata sun nuna cewa an ɗage jana'izar marigayin da aka shirya gudanarwa bayan sallar La'asar a ranar Talata. Yanzu an mayar da jana'izar zuwa bayan Magariba a haramin birnin Madina. Dama dai Mustapha Junaid, mataimaki na musamman ga marigayin ya shaida wa BBC cewa tuni gawar Alhaji Aminu ta isa birnin na Madina. "Alhamdu lillah an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina kuma yanzu haka za a je Shakzura inda a nan ne za a ƙarasa shirya shi kafin daga bisani a kai shi haramin Madina domin gudanar da sallah kamar yadda hukumomin Saudiyya suka amince." In ji Mustapha Junaid. A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.