Tuesday, December 16
Shadow
Gajartace tawa El-Rufai yawa shiyasa ya ke ta soki burutsu>>Inji Shugaba Tinubu

Gajartace tawa El-Rufai yawa shiyasa ya ke ta soki burutsu>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, gajarta ce tawa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yawa shiyasa yake ta soki burutsu. Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga. El-Rufai a wata hira da aka yi dashi yace a wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da suka gudanar sun gano cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai ci zaben shekarar 2027 ba. Saidai Onanuga yace babbar matsalar El-Rufai shine shi a ko da yaushe yana son ya nuna yafi sauran mutane. Yace El-Rufai bashi da biyayya inda yawa mutane da yawa a baya ciki hadda wansa wanda tsohon soja ne. Yace kuma makaryaci ne sosai wanda ke yin abubuwa yawanci dan kawai amfanin kansa.
A karin farko musulmi ya ci zaben fidda gwani na tsayawa takarar magajin garin Birnin New York na kasar Amurka

A karin farko musulmi ya ci zaben fidda gwani na tsayawa takarar magajin garin Birnin New York na kasar Amurka

Duk Labarai
A karin farko a tarihi, Musulmi me suna Zohran Mamdani ya lashe zaben fidda gwani na tsayawa takarar magajin garin birnin New York City dake kasar Amurka. Zohran ya lashe zabenne a karkashin jam'iyyar Democrats inda ya doke tsohon gwamnan Jihar ta New York, Andrew Cuomo. Zohran dan shekaru 33 ne kuma dan majalisa ne a Queens dake New York din. A yanzu dai zai jira zuwa watan Nuwamba inda za'a gudanar da ainahin zaben dan ganin wanene zai zama magajin garin na Birnin New York City. Saidai tuni yahudawan dake birnin suka ce zasu fice daga birnin sanoda nuna kiyayya ga Zohran. Kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa, Zohran yace idan ya zama magajin garin New York City, toh lallai duk sanda Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu ya shiga birnin zai kamashi.
Karanta jadawalin sabbin Jihohi 31 da majalisar tarayya ke son korkirowa a Najeriya

Karanta jadawalin sabbin Jihohi 31 da majalisar tarayya ke son korkirowa a Najeriya

Duk Labarai
North-Central: Benue Ala (from Benue) Okun, Okura, Confluence (from Kogi) Apa-Agba, Apa (from Benue) Federal Capital Territory (to be a standalone 37th state)North-East: Amana (from Adamawa) Katagum (from Bauchi) Savannah (from Borno) Muri (from Taraba) North-West: New Kaduna, Gurara (from Kaduna) Tiga, Ghari (from Kano) Kainji (from Kebbi) South-East: Etiti (proposed 6th SE state) Adada (from Enugu) Urashi, Orlu, Aba (from South-East region) South-South: Ogoja (from Cross River) Warri (from Delta) Bori (from Rivers) Obolo (from Rivers/Akwa Ibom) South-West: Toru-Ebe (from Delta, Edo, Ondo) Ibadan (from Oyo) Lagoon (from Lagos) Ijebu, Oke-Ogun (from Ogun) Ife-Ijesha (from Oyo and Osun)
Sanata Neda Imasuen ya bar jam’iyyar Labour party zuwa APC

Sanata Neda Imasuen ya bar jam’iyyar Labour party zuwa APC

Duk Labarai
Sanata Neda Imasuen daga jihar Edo ya bar jam'iyyar Labour Party inda ya koma jam'iyyar APC inda yace rikicin cikin gida ya mamaye jam'iyyar ta APC. Ya bayyana ficewarsa daga Labour party zuwa APC a zaman majalisar Dattijai na ranar Laraba. Kakakin majalisar, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan inda ya karanto takardar da sanata Nedu ya aikawa majalisar. Yace kamin yanke wannan shawara sai da ya tuntubi da yawa daga cikin abokan shawararsa da mutanen mazabarsa da sauransu.
Duk malamin cocin da ya kai mukamin Priest dole ne ya hakura da jìma’ì saboda tsoron Allah>>Fafaroma ya jaddada dokar cocin Katolika

Duk malamin cocin da ya kai mukamin Priest dole ne ya hakura da jìma’ì saboda tsoron Allah>>Fafaroma ya jaddada dokar cocin Katolika

Duk Labarai
Fafaroma Leo XVI ya jaddada cewa dolene duk wanda ya kai mukamin Priest ya hakura da yin jima'i a rayuwarsa saboda tsoron Allah. Ya bayyana hakane a ranar Laraba inda yace Bishops su tashi tsaye dan hukunta masu karya wannan doka da kuma cin zarafin mata da yara. Yayi bayanin ne ga Bishops guda 400 da suka fito daga kasashe 38 na Duniya. A lokuta da dama dai ana samun jagororin cocin suna lalata da yara ko cin zarafin matan dake halartar cocinsu.
Kalli Bidiyo: Ƴan sanda sun kama mutum 26 da ake zargi da hannu a harin Jihar Benue

Kalli Bidiyo: Ƴan sanda sun kama mutum 26 da ake zargi da hannu a harin Jihar Benue

Duk Labarai
Sufeto Janar na ‘ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa an kama mutum 26 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi a al’ummar Yelwata da ke ƙaramar hukumar Guma a Jihar Benue, ranar 13 ga Yuni, 2025. Egbetokun ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 47 a cikin harin, yayin da wasu 27 kuma suka jikkata kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito. Rundunar ‘yan sanda ta ce an kuma kashe wasu biyu daga cikin ‘yan harin a ranar da lamarin ya faru. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1937832392464441518?t=girIfCT6i0I0_OrwQt0kgA&s=19 Egbetokun ya ce an tura jami’an tsaro domin bin diddigin lamarin, kuma daga baya an kama wasu manyan masu hannu biyu-biyu a kisan wanda hakan ya kai ga kama karin mutum bakwai.
Me sayar da motoci ya koka bayan da wani ya sayi Motar Naira Miliyan 45 kuma ya biya kudin tun shekarar 2023 amma bai je ya dauki motar tasa ba

Me sayar da motoci ya koka bayan da wani ya sayi Motar Naira Miliyan 45 kuma ya biya kudin tun shekarar 2023 amma bai je ya dauki motar tasa ba

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani me sayar da motoci ya koka saboda wani ya sayi motar Naira Miliyan 45 a hannunshi kuma ya biya kudin tun shekarar 2023 amma bai je ya karbi motarba. da yawa aun jinjinawa me sayar da motocin inda suka ce ba kowane zai iya abinda yayi ba.
Shugaba Tinubu zai kafa rundunar tsaro ta musamman a garin Zuru na jihar Kebbi

Shugaba Tinubu zai kafa rundunar tsaro ta musamman a garin Zuru na jihar Kebbi

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kafa rundunar tsaro ta musamman a garin Zuru na jihar Kebbi. Gwamnan jihar, Nasir Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai kauyukan karamar hukumar Danko da Wasagu inda 'yan Bindiga suka kashe mutane 30. Yace za'a kafa rundunar tsaronne dan inganta tsaro a jihar dama yankin baki daya. Gwamnan yace yanzu haka ya yi kokarin an kai jami'an tsaro da makamai inda lamarin ya faru.
Kamfanin Multichoice dake da tauraron dan adam na DSTV ya rage farashi daga dubu 20 zuwa dubu 10 bayan da ya tafka asarar kudade saboda mutane sun daina kallo

Kamfanin Multichoice dake da tauraron dan adam na DSTV ya rage farashi daga dubu 20 zuwa dubu 10 bayan da ya tafka asarar kudade saboda mutane sun daina kallo

Duk Labarai
Kamfanin Multichoice dake da tauraron dan Adam na DSTV sun sanar da rage farashin da ake biya dan kallo duk wata daga Naira dubu 20 zuwa Naira Dubu 10. Hakan na zuwane bayan da kamfanin ya tafka asarar miliyoyin kudade saboda da yawan 'yan Najeriya sun daina saka kudi dan kallon. Saidai abin jira a gani shine ko hakan zai sa mutane a yanzu su dawo su ci gaba da biyan kudi dan kallon DSTV din?