Saturday, December 13
Shadow
Da gangan Tinubu ya jefa ‘yan Najeriya cikin Yunwa, kuma irin yanda ake kulle dashi ko dansa Seyi sai baiwa shugaban hukumar zabe INEC ba zai ci zaben shekarar 2027 ba>>Inji Solomon Dalung

Da gangan Tinubu ya jefa ‘yan Najeriya cikin Yunwa, kuma irin yanda ake kulle dashi ko dansa Seyi sai baiwa shugaban hukumar zabe INEC ba zai ci zaben shekarar 2027 ba>>Inji Solomon Dalung

Duk Labarai
Tsohon Ministan matasa sa wasanni, Solomon Dalung ya bayyana cewa ko da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dansa Seyi zai baiwa shugaban hukumar zaben me zaman kanta INEC ba zai ci zaben shekarar 2027 ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Sunnews. Yace Tinubu ya ja dagar yaki da mutanen Najeriya saboda jefasu a halin yunwa da yayi wanda ba'a taba samun irin hakan ba a tarihin Najeriya. Dalung yace ko da tururuwar da ake ta shiga APC ba wai dan farin jinin shugaba Tinubu bane, ana yi ne saboda kare muradun siyasa da kuma tsoron kamu.
Kalli Bidiyo: Yanda Tsohon Mataimakin shugabab kasa, Atiku Abubakar ya taka rawa da matarsa Titi

Kalli Bidiyo: Yanda Tsohon Mataimakin shugabab kasa, Atiku Abubakar ya taka rawa da matarsa Titi

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taka rawa shi da matarsa, Titi Abubakar a yayin da take bikin cika shekaru 75 da haihuwa. Atiku yace shekararsu sama da 50 da aure inda ya jinjinawa matar tasa da cewa ta yi hakuri da halinsa. https://www.youtube.com/watch?v=8BT8ZiqApF4 Atiku yace duka iyayensu biyu basu son aurensu amma a haka suka yi auren da bokai biyu kawai da suka halarta.
An daure likitan Najeriya a gidan yari saboda sumbatar mara lafiya har sau biyu ba tare da son ranta ba

An daure likitan Najeriya a gidan yari saboda sumbatar mara lafiya har sau biyu ba tare da son ranta ba

Duk Labarai
Wani likita dan Najeriya dake aiki a kasar Ingila an daukeshi tsawon shekara daya saboda sumbatar wata mata marar lafiya dake karkashin kulawarsa. Likitan me suna Adewale Kudabo ya fara sumbatar marar lafiyar ne a lebenta yayin da take kwance bata iya motsi sannan ya sake sumbatar ya a karo na biyu. Lamarin ya farune a Asibitin York Hospital. Saidai likitan yace ba da wata manufa yayi hakan ba yana son nuna jin kai ne ga marar lafiyar kuma ba a lebenta ya sumbaceta ba, ya sumbaceta ne goshi. Marar lafiyar ta gayawa kotu cewa, sam bata ji dadin abinda ya mata ba ya sakata a fargaba da tsoro da damuwa. Lauyan wanda akw zargi yace sun amsa laifin wanda ake zargin amma suna neman sauki saboda wannan ne karin farko da ya aikata wannan laifi. Mai shari'a Alex Menary yace ya gam...
Shugaba Tinubu ya taya Tsohon Shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar murnar cika shekaru 83

Shugaba Tinubu ya taya Tsohon Shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar murnar cika shekaru 83

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar me ritaya murnar cika shekaru 83 da haihuwa. A sanarwar da ya sanyawa hannu ranar Lahadi, Shugaba Tinubu ya bayyana Abdulsalam Abubakar a matsayin mutum me dattako wanda ke son zaman lafiya. Yace yayi rayuwa me kyau wadda tasa ma'aikatan gwamnati da yawa ke son yin koyi dashi.
Da Duminsa: Akwai yiyuwar majalisar tarayya zata taimakawa Tinubu ya ci gaba da mulki iya tsawon rayuwarsa

Da Duminsa: Akwai yiyuwar majalisar tarayya zata taimakawa Tinubu ya ci gaba da mulki iya tsawon rayuwarsa

Duk Labarai
Tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya yi zargin cewa wataran za'a tashi kawai majalisar Dattijai ta mayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shugabab dindindin har iya tsawon rayuwarsa. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a jaridar Sunnews. Solomon Dalung yace 'yan majalisar saboda tsabar biyayyar da suke wa shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu idan suka ganshi sai ka ga kamar irin jikoki sun ga kakansu. Yace irin biyayyar da suke masa ta yi yawa zata sa a rika yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya karan tsaye ba tare sa bin doka ba wajan gudanar da gwamnati.
Ƴan Ta’addar Daji Sun Sako Wasu Daga Cikin Waɗanda Sukayi Garkuwa Dasu A Ɗanmusa Bayan Anyi Zaman Sulhu Jiya Asaba

Ƴan Ta’addar Daji Sun Sako Wasu Daga Cikin Waɗanda Sukayi Garkuwa Dasu A Ɗanmusa Bayan Anyi Zaman Sulhu Jiya Asaba

Duk Labarai
Biyo bayan zaman sulhu da sasanci da ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar Katsina ƴan bindigar sun sako mutanen da suke garkuwa dasu Goma Sha Shidda tare da bada wasu bindigogi dake hannun su. A ƙoƙarin su na ganin an samu zaman lafiya shuwagabannin sojoji dake jagorancin rundunar jami'an tsaron Operation Fasan Yamma haɗin guiwa da sauran masu ruwa da tsaki sun jagorancin zaman Sasanci a ƙaramar hukumar Dan Musa. Inda ƙasurguman ƴan bindiga da suka haɗa da Kamulu Buzaru, Manore, Nagwaggo, Lalbi, Alhaji Sani, Dogo Baidu, Dogo Nahalle, da Abdulkadir Black suka aje makaman su bisa raɗin kansu tare da sako waɗanda suka yi garkuwa dasu a ranar 14 June 2025. Ƴan bindigar sun bayyana cewa sun miƙa wuya kuma dagaske suke akan wannan sasancin, inda makaman da suka bada aka miƙa s...
Bidiyo: Ni Bazawarace, Kuma ‘Yan mata yanzu idan ba wadda Allah ya tsare ba su da zawarawan duk daya ne>>Samha M. Inuwa

Bidiyo: Ni Bazawarace, Kuma ‘Yan mata yanzu idan ba wadda Allah ya tsare ba su da zawarawan duk daya ne>>Samha M. Inuwa

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa ta bayyana cewa, ta taba aure, ta bayyana hakanne a hirar da Hadiza Gabon ta yi da ita a shirinta me suna Gabon Show. Samha ta bayyana cewa, 'yan matan da zawaranwan wannan zamanin duk daya ne sai wadda Allah ya tsare. https://www.tiktok.com/@abdullahee40/video/7515437929221688583?_t=ZM-8xEYvkOCejI&_r=1 Samha ta kuma bayyana cewa, ita tana son diyarta ta gajeta dan ta san rayuwa me kyau ta ke yi.
Babban Sakatare a jihar Gombe da wasu mutane 4 sun rasu bayan dawo da wutar lantarki me karfi

Babban Sakatare a jihar Gombe da wasu mutane 4 sun rasu bayan dawo da wutar lantarki me karfi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dawo da wutar Lantarki me karfi ta yi sanadiyyar Rasuwar mutane 5 a unguwar Tudun Wada Pantami jihar Gombe. Cikin wadanda suka rasu akwai babban sakatare a jihar, Abdullahi Kulani. Lamarin ya farune da duku-dukun ranar Asabar inda aka kawo wutar Lantarki da karfi. Hakanan Bayan wadanda suka rasu din akwai mutane 13 da suka jikkata a lamarin. Kakakin 'yansandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace bayan tashin wutar sun je gurin da lamarin ya...
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce bai amince a kashe Shugaban Iran ba

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce bai amince a kashe Shugaban Iran ba

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, bai amince da aniyar kasar Israyla ta kashe shugaban juyin Juyahlin kasar Iran Atayollah Khumaini ba. Israyla tana son ta kashe Shugaban Iran dinne saboda a lissafinta idan ta kasheshi shine za'a kawo karshen shirin Mallakar makamin kare dangi na kasar. Saidai shi Trump a cewarsa, bai yadda da wannan mataki ba inda yace sulhu yafi baiwa muhimmanci.