Ba gaskiya bane cewa Sojoji dubu goma sun tsere daga aiki>>Inji Hukumar sojojin Najeriya
Hukumar sojojin Najeriya ta karyata cewa, Sojoji dubu goma sun tsere daga aiki.
Wasu rahotanni a kafafen sada zumunta sun bayyana cewa, Saboda sojoji dubu 10 sun tsere daga aikin soja duk wanda ya kai sama da shekaru 18 dole zai shiga aikin soja.
Saidai hukumar sojojin sun bayyana cewa wannan labarin karya ne.
A baya dai Hukumar sojojin ta sanar da daukar sabbin sojoji 24,000.
https://twitter.com/HQNigerianArmy/status/1991787697976000989?t=xPFnCke9fTejeYkzVK3vdQ&s=19








