Ba zamu dawo da tallafin man fetur ba>>Inji Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ba zata dawo da biyan Tallafin man fetur ba.
Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga.
Bayo yace suna sane da kiraye-kirayen da ake game da cire tallafin man fetur da kuma maganar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar yayi na cewa zai dawo da tallafin man fetur.
Yace amma duk da wannan matsi ba zasu dawo da tallafin man fetur din ba.
Dalili shine idan aka dawo da biyan tallafin man fetur din, ci gaban da aka samu a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zasu ruguje.








