Maganin rage kiba wanda bashi da illa a hankali ake samun sa, mafi yawan abubuwan rage kiba na dare daya suna illa sosai.
Ga hanyoyin da ake bu wajan rage kiba ba tare da shan magani ba:
A rage cin kayan zaki wanda basu da fiber.
A rage shan lemun kwalba, Biredi, cincin,biskit da sauransu, a yawaita cin Wake, Alkama, kwai, kifi da nama wanda bashi da illa.
A Motsa jiki:
Motsa jiki na da matukar muhimmanci idan ana son rage kiba. Ba wai sai mutum yayi abinda zai kure kansa ba, ko da tafiya da sauri-sauri ta isa, ana iya yinta na tsawon mintuna 30 zuwa 60 a kullun dan samun sakamako me kyau.
A daina cin abubuwan da kamfani ya sarrafa irin na leda kwalba da roba.
Anan ana maganar irinsu madarar gwagwani,Waken Gwangwani, Alewa, Biskit, da sauran duk wasu abubuwan da ba'a g...