Wani Rahoto daga kafar Statisense yace wai jihohin Arewa ne suka fi shan giya.
Rahoton yace jihohin Arewa maso yamma ne akan gaba.
Sai jihohin Arewa ta tsakiya na biye musu baya.
Sai Jihohin Arewa maso gabas.
Sai jihohin Yarbawa na Kudu maso yamma.
Sai jihohin Kudu maso kudu.
Sai Jihohin Kudu maso yamma.
HEAVY ALCOHOL CONSUMERS — 2024
Zone — Male | Female in 1,000 population:North West — 624 | 30 *North Central — 140 | 56North East — 66 | 298South West — 40 | 46South South — 24 | 63South East — 15 | 25
NB : asterisk means insufficient sample size
#Statisense(NDHS 2024)
Rahotanni daga Abuja sun bayyana cewa wani jirgin sojojin saman Amurka daya taso daga kasar ta Amurka me suna, A US Air Force C-37B ya sauka a Abuja.
Jirgin ya saukane a daren jiya.
Bayan Awanni 4 Jirgin ya kuma tashi zuwa kasar Ghana.
Brant Philip me kawo rahoto akan harkar tsaro a Afrika ne ya ruwaito wannan labari.
https://twitter.com/BrantPhilip_/status/1997243829930561958?t=7g_arf0RZhpWPaLJqC8kHA&s=19
Wannan matashiyar 'yanmurar ta bayyana aniyarta ta Qona Qur'ani.
Tace itace zata zama ta farko a jihohin Inyamurai da zata Qona Qur'anin.
https://twitter.com/Onyinye________/status/1997016140409721064?t=RUI4xRwG6lkDXSKpiccW6Q&s=19
Wannan Bidiyon dan majalisa daga jihar Katsina ne watau, Honorable Abubakar Yahaya wanda aka ga yana chanja tayar motarsa da kansa bayan da ta yi fachi.
Da yawa sun yaba da rashin girman kansa.
https://twitter.com/The_Umdazz/status/1997215926983315869?t=FtSlA4wKGyKnuXinkA_BQA&s=19
Gwamnan jihar Edo, Monday, Okpebholo yayi zargin cewa wani dan siyasa ne dake son cin zabe yake sawa ana garkuwa da mutane a Najeriya dan bata sunan Gwamnati.
Yace haka sukawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kuma sun samu nasara a wancan lokacin.
Saidai bai bayyana sunan dan siyasar da yake zargi ba.
https://twitter.com/ChuksEricE/status/1997230638651347070?t=GKelUTSR6TMChwMlL4O2Aw&s=19
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Amurka ta fara kawo makamai da zata yi amfani dasu wajan hare-haren da zata kai kan kungiyoyin 'yan tà'àddà a Najeriya.
Masani kan harkar tsaro, Brant Philip ne ya bayyana haka inda yaje jiragen yaki dauke da makaman sun rika sauka a sansanin da Amurkar ta kafa a kasar Ghana wanda daga canne zata rika kawo harin.
Yace Amurkar ta shafe sati 2 kullun tana aiko jirgi mara matuki dan tattara bayanan sirri akan kungiyoyin na ÌŚWÀP da Bòkò Hàràm da sauransu.
https://twitter.com/BrantPhilip_/status/1996848825999241722?t=1J9KQgRJ2ouMkJBiIMq_Iw&s=19
Kwamitin shugaban kasa dake kula da canja dokar Haraji ya bayyana shahararrun masu amfani da kafafen sada zumunta su 20 da za'a yi amfani dasu wajan tallata sabuwar dokar Haraji Gwamnatin.
An fitar da wadannan sunayene daga cikin guda sama da dubu 8 da aka mika sunayensu.
Financial Jennifer, Onlinebanker, Don Aza, Mary Efombruh, Baba Ogbon Awon Agba International, Perpetual Badejo, Personalfinancegirl, Tomi Akinwale, Emeka Ayogu, da Aderonke Avava.
Sauran sune Odunola Ewetola, Christiana Balogun, Mosbrief, Chidozie Chikwe, Zainulabideen Abdulazeez, Chinemerem Oguegbe, Oyagha Michael, Ayomide Ogunlade, Ayọ̀dèjì Fálétò, and Vera Korie.
Saidai a lurar da hutudole yayi dan Arewa ko daya a cikinsu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aika da sunan matacce a cikin sunayen wadanda yake son baiwa mukamin jakadanci zuwa majalisa.
Wanda shugaban ya aika shine Sen. Adamu Garba Talba wanda tun a 14 ga watan Yuli da ya gabata ya rasu.
Dan Asalin Jihar Yobene.