HAJJIN 2025: Yariman Saudiyya ya yi kira da kakkausar murya da a dakatar da kìsàn kìyàshì da ake wa Fàlàsɗìnàwà
Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya kira ga al’ummar duniya da a dauki matakin dakatar da hare-haren da ake kai wa Gaza yana mai jaddada cewa akwai buƙatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin ta hanyar bin ka’idojin na duniya.
Yariman Saudiyya ne ya yi wannan kira ga al’ummar duniya domin kawo karshen fadan da ake yi a Gaza.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa ( NAN) ya rawaito sarki Salman na bayyana haka cikin saƙon da ya gabatar na taron shekara a lokacin a Muna a ranar Asabar.
Ya jaddada cewa daukar mataki domin kare rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da kuma samar da yanayi na zaman lafiya da walwalar ga Falasɗinawa muhimmin abu ne.
Ya ce, “wannan roƙi na nuna yadda kasar Saudiyya ta himmatu wajen kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa da...








