Tuesday, December 16
Shadow
Wallahi Da Yawan Mahajjatanmu Ba Su San Yadda Ake Dawafi Ba Duk Suna Kashe Makudan Kudade Su Zo Hajji, Wallahi Mun Sauka A Filin Jirgi A Jidda Wani Bafulatani Ya Ga Hoton Wata Balarabiya Kyakkyawa Sai Yake Tambaya Wannan Ita Ce ‘Nana Aisha’?, Inda Sheik Gadon Kaya

Wallahi Da Yawan Mahajjatanmu Ba Su San Yadda Ake Dawafi Ba Duk Suna Kashe Makudan Kudade Su Zo Hajji, Wallahi Mun Sauka A Filin Jirgi A Jidda Wani Bafulatani Ya Ga Hoton Wata Balarabiya Kyakkyawa Sai Yake Tambaya Wannan Ita Ce ‘Nana Aisha’?, Inda Sheik Gadon Kaya

Duk Labarai
Wallahi Da Yawan Mahajjatanmu Ba Su San Yadda Ake Dawafi Ba Duk Suna Kashe Makudan Kudade Su Zo Hajji, Wallahi Mun Sauka A Filin Jirgi A Jidda Wani Bafulatani Ya Ga Hoton Wata Balarabiya Kyakkyawa Sai Yake Tambaya Wannan Ita Ce 'Nana Aisha'?, Inda Sheik Gadon Kaya
Kalli Bidiyo: Rawar da Ganduje yayi a lokacin da Rarara ke wakeshi ta dauki hankula

Kalli Bidiyo: Rawar da Ganduje yayi a lokacin da Rarara ke wakeshi ta dauki hankula

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya chashe a yayin da shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya wakeshi. Lamarin ya farune a wajan babban taron jam'iyyar APC na kasa daya gudana a fadar shugaban kasar dake Abuja. https://www.tiktok.com/@usyzamani/video/7507294051272559928?_t=ZM-8wapg4onEam&_r=1 Da yawa dai sun bayyana mamakin ganin rawar ta Ganduje.
Mutane 2 sun nutse a ruwa suka ràsù a Kano yayin da suke bin sahun wani da suke bi bashi

Mutane 2 sun nutse a ruwa suka ràsù a Kano yayin da suke bin sahun wani da suke bi bashi

Duk Labarai
Wasu mutane 2 a Kano sun rasu bayan da suka nutse a ruwa yayin da suke bin sahun wani da suke bi bashi. Lamarin ya farune a titin Ring Road dake Dorayi Babba. Kakakin hukumar kwanakwana ta jihar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin. Yace wani me suna Garba Sani ne ya kirasu ya sanar dasu lamarin da misalij karfe 9:36 a.m. Yace sun dakko mutanen 2 masu suna Saifullahi Muhammad, 27, da Halifa Abdullahi, 29 daga ruwan da suka fada. Yace suna bin wani mutum ne da suke bi bashi daga Kofar ruwa yayin da ibtila'in ya afka musu. Yace an kaisu asibitin Murtala Inda likita ya tabbatar da sun rasu, yace sun mika gawarwakin zuwa ga Inspector Halifa Muhammad.
Ku Dai ku ci gaba da min fatan Alheri: Ni kuma ina bakin kokarina wajan Gyara kasarnan>>Shugaba Tinubu

Ku Dai ku ci gaba da min fatan Alheri: Ni kuma ina bakin kokarina wajan Gyara kasarnan>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi kira ga 'yan Najeriya kada su yanke tsammani, su ci gaba da mai fatan Alheri game da ayyukan da yake yi. Ya bayyana hakane a wajan taron jam'iyyar APC na kasa da ya gudana a fadarsa. Yace yana fatan ganin karin 'yan Jam'iyyar Adawa suna shiga jami'iyyar ta APC. Shugaban ya kuma gode da amincewar da aka bashi na shugabantar Najeriya.
Na sake fada cewa bani da lokacin da zan roki Allah ya bani miji>>Matashiya ta sake nanatawa

Na sake fada cewa bani da lokacin da zan roki Allah ya bani miji>>Matashiya ta sake nanatawa

Duk Labarai
Matashiyarnan da Bidiyota ya watsu sosai saboda maganar da ta yi na cewa, bata da lokacin da zata roki Alah ya bata miji, ta sake maimaita maganar. Matashiyar tace ta sake maimaitawa duk abinda zai faru ya faru bata sa lokacin da zata roki Allah ya bata miji, duk wanda ya bata shikenan. https://www.tiktok.com/@boh_360_hub/video/7507012060476198150?_t=ZM-8wagsLnQHyP&_r=1 Tace koma dai menene ba za'a daina zaginta ba.
‘Allah Ya isa duk wanda ya ce APC nake yi wa aiki’ – Inji Shugaban PDP Damagum

‘Allah Ya isa duk wanda ya ce APC nake yi wa aiki’ – Inji Shugaban PDP Damagum

Duk Labarai
Shugaban babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, Ambasada Umar Iliya Damagun, ya musanta zargin da wasu ke yi masa cewa yana yi wa jam'iyya mai mulkin kasar, APC aiki ne shi ya sa rikicin PDP din ya ki ci ya ki cinyewa. A hirarsa da BBC Ambasada Damagun ya ce shi kam tsakaninsa da masu zargin cewa shi dan-amshin-shata ne na jam'iyyar APC, baa bin da za ice sai, ''Allah Ya isa.'' Ya ce : ''Allah ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan Kazafi, kuma Allah Zai yi mana shari'a in da zan shiga jam'iyyar APC da tun lokacin Buhari da na shiga. ''Kuma ina da tarihi tun da na shiga jam'iyyar PDP a 1999 ban taba sauya sheka ba. Dole wanda ba ya so na zai nemi yanda zai yaba min zargi don ya samu biyan bukatarsa. Na ce ma na je na yi mitin da Tinubu, a Ingila, wannan duk masu yin wan...
Hatsarin ababen hawa ya kàshè mutum 1,593 a Najeriya cikin wata uku

Hatsarin ababen hawa ya kàshè mutum 1,593 a Najeriya cikin wata uku

Duk Labarai
Hukumar Kiyaye Aukuwar Haɗurra ta Najeriya, (FRSC) ta ce kimanin mutum 1,593 ne suka mutu sakamakon haɗurra a cikin wata ukun farko na shekarar 2025. Cikin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna samun ƙaruwar munanan haɗurran da suka haddasa rasa rayuka da raunuka. Hukumar ta bayar da rahoton cewa an samu haɗurra 2,650 a faɗin Najeriya daga watan Janairu zuwa Maris. To sai dai bisa ga alƙaluman an samu raguwar yawan haɗuran idan aka kwatanta da daidai wannan loacin a 2024. Haɗurran ababen hawa na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da asarar rayuka a Najeriya, wani abu da masana ke alaƙantawa da rashin kyawun titunan ƙasar, da kuma tuƙin ganganci daga ɓangaren direbobi.
Mutanen jihar Kebbi sun ce Shugaba Tinubu ne zabin su a 2027

Mutanen jihar Kebbi sun ce Shugaba Tinubu ne zabin su a 2027

Duk Labarai
Jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi sun bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin zabinsu a shekarar 2027 sannan Gwamna Nasiru Idris a matsayin zabinsu na dan takarar gwamna a jihar. Sun cimma wannan matsaya ne bayan zaman da suka yi na musamman da ya faru a Birnin Kebbi na masu ruwa da tsaki a jam'iyyar. Daya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, Abdullahi Idris Zuru ya tabbatar da hakan. Hakana zaman yayi maraba da tsaffin sanatocin jihar karkashin jam'iyyar PDP da suka koma APC wadanda sune Senator Muhammad Adamu Aliero (Kebbi Central), Dr. Yahaya Abdullahi (Kebbi North), da Senator Garba Musa Maidoki (Kebbi South)
‘Yan Najeriya dubu 50 sun yi gudun Hijira zuwa kasar Ingila a shekarar 2024

‘Yan Najeriya dubu 50 sun yi gudun Hijira zuwa kasar Ingila a shekarar 2024

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Ingila na cewa 'yan Najeriya 52,000 ne suka yi gudun Hijira zuwa kasar Ingila a shekarar 2024. Rahoton yace 'yan Najeriya na kan gaba waja yin gudun Hijira zuwa kasar Ingila a tsakanin kasashe wanda ba turawa ba. Hakan na zuwane duk da yake yawan masu yin gudun Hijira zuwa kasar ta Ingila ya ragu da kaso 50 cikin 100. Yawanci 'yan Najeriyar na tafiya ne saboda nema aiki da karatu da sauransu.