Tuesday, January 13
Shadow
Biyo bayan nuna goyon baya ga Trump da goyon bayan Shi ya kawo Khàrì Najeriya, Fitsararriyar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj ta rasa mabiya Miliyan 4 a shafinta na sada zumunta

Biyo bayan nuna goyon baya ga Trump da goyon bayan Shi ya kawo Khàrì Najeriya, Fitsararriyar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj ta rasa mabiya Miliyan 4 a shafinta na sada zumunta

Duk Labarai
Tauraruwar mawakiyar Amirka, Nicki Minaj ta rasa mabiya Miliyan 4 a shafinta na Instagram. Hakan ya faru ne bayan data nuna goyon baya ga shugaban Amirkar, Donald Trump. Sannan tace tana goyon bayan harin da zai kawo Najeriya. Yanzh haka dai an kaddamar da kiraye-kirayen a koreta daga Amurka ta koma kasarta, ta Asali watau Trinidad.
Najeriya ta ci Tunisia 3-2

Najeriya ta ci Tunisia 3-2

Duk Labarai
A ci gaba da gasar cin kofin Aftika na AFCON, Najeriya ta ci Kasar Tunisia kwallaye 3-2 Najeriya ta sakawa Tunisia kwallaye 3 ta hannun Ndidi, Osimhen da Lookman. Saidai ana daf da tashi, Tunisia ta farke kwallaye 2 inda a haka aka tashi wasan. Hakan yasa Najeriya ta tsallake zuwa mataki na gaba.
Kalli Bidiyon:Momi Gombe ta yi magana kan zargin da ake cewa itace ta haihu

Kalli Bidiyon:Momi Gombe ta yi magana kan zargin da ake cewa itace ta haihu

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Momi Gombe ta fito ta yi magana a karin farko kan zargin da ake mata cewa itace ta haihu a masana'antar Kannywood. Momi a wani Bidiyo da Oscar442 ya wallafa an ji yana tbayarta cewa mutane nata kiransa cewa wai ta haihu. Ta tambayeshi cikin Raha wane suna za'a sakawa jaririn. Daga baya dai tace 'yan Biyu ne ta haifa https://www.tiktok.com/@sunusioscar_442/video/7588556808130809109?_t=ZS-92aAVZdJuOf&_r=1
Biyo bayan shawarar da Dr. Ahmad Gumi ya bayar, Gwamnatin tarayya tace ta fara magana da kasar Turkiyya dan su taimakawa Najeriya magance matsalar tsaro

Biyo bayan shawarar da Dr. Ahmad Gumi ya bayar, Gwamnatin tarayya tace ta fara magana da kasar Turkiyya dan su taimakawa Najeriya magance matsalar tsaro

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, sun tuntubi kasar Turkiyya dan ta taimakawa Najeriya wajan magance matsalar tsaro. Ya bayyana hakane yayin ganawa da kungiyar Kiristoci ta CAN a ziyarar data kai masa a fadarsa dake Abuja. Shugaban yace akwai bukatar Kiristoci su taya Najeriya da Addu'a dan kawo karshen matsalar. Ya kuma kara da cewa, sun siyi Jiragen yaki 3 daga kasar Amurka amma ba zasu zo da wuri ba. Hakan na zuwane bayan da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya baiwa Gwamnatin tarayya shawarar ta yi watsi da kasar Amurka ta koma neman taimakon tsaro daga kasashen China, Pakistan da Turkiyya.
Kalli Bidiyon: Malam Aminu Saira na shan Suka saboda sakin Fim din Labarina duk da rasuwar Fulani

Kalli Bidiyon: Malam Aminu Saira na shan Suka saboda sakin Fim din Labarina duk da rasuwar Fulani

Duk Labarai
Me shirya fim din Labarina, Malam Aminu Saira na shan suka saboda sakin Fim din Labarina na wannan makon duk da rasuwar daya daga cikin jaruman fim din watau Fulani. Da yawa sun yi Allah wadai da hakan inda suke cewa dan girmama rasuwarta ya kamata ace an dakatar da nuna fim din na wannan satin. https://www.tiktok.com/@captainhabeeb/video/7588468852590218517?_t=ZS-92ZsHawwGY5&_r=1 Wasu ma sun yi zargin cewa, ko jana'izar ta su aminu Saira basu Halarta ba. kalli Bidiyon anan https://twitter.com/fatimaaaah__/status/2004678236492771820?t=Q3VMIdy9GKybta09X9PnoA&s=19