Monday, December 15
Shadow
Kaɗan Kenan Daga Cikin Kyaututtukan Raguna Da Shanu Da Masoya Suka Yiwa Ango Rarara Da Amaryasa A’isha Humaira.

Kaɗan Kenan Daga Cikin Kyaututtukan Raguna Da Shanu Da Masoya Suka Yiwa Ango Rarara Da Amaryasa A’isha Humaira.

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Kaɗan Kenan Daga Cikin Kyaututtukan Raguna Da Shanu Da Masoya Suka Yiwa Ango Rarara Da Amaryasa A'isha Humaira.
Da Gwamnan Bauchi ya mike tsaye yace zai mare ni, na duba naga ko warewa muka yi bai iya dukana shiyasa nima na mike tsaye na nuna mai tsawona>>Inji Ministan Harkokin kasashen Waje Yusuf Tuggar

Da Gwamnan Bauchi ya mike tsaye yace zai mare ni, na duba naga ko warewa muka yi bai iya dukana shiyasa nima na mike tsaye na nuna mai tsawona>>Inji Ministan Harkokin kasashen Waje Yusuf Tuggar

Duk Labarai
A karon farko cikin makonni da dama, Ministan Harkokin Wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana wa BBC dalilin rigimar da suka yi tsakaninsa da Gwamnan jiharsa ta Bauchi da kuma mataimakin Gwamnan. Tun a baya wasu rahotanni sun ce an samu hatsaniya ne tsakanin Ministan da Gwamna Bala Mohammed, Kauran Bauchi inda har mataimakin gwamnan ya yi yunkurin marin Ministan. Lamarin dai ya faru ne ranar Juma'a 19 ga watan Afirilun nan, lokacin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ke wata ziyara a jihar ta Bauchi. A tattaunawarsa da BBC, Ministan ya yi karin haske kan abin da ya haddasa rashin jituwa tsakaninsu har ta kai su ga sa-in-sa. Ministan ya ce ba kamar yadda wasu ke yadawa ba cewa da mataimakin gwamna suka yi hatsaniya, da ainahin shi gwamnan ne abin y...
Kalli Bidiyon yanda shugaban jarabawar JAMB ya fashe da kuka saboda kuskuren hukumar yasa dalibai da yawa sun fadi jarabawar

Kalli Bidiyon yanda shugaban jarabawar JAMB ya fashe da kuka saboda kuskuren hukumar yasa dalibai da yawa sun fadi jarabawar

Duk Labarai
An gano cewa, Kuskuren hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami'a ta JAMB yasa dalibai da yawa sun fadi jarabawar. Akalla Dalibai Miliyan 1.5 ne suka ci kasa da makin da ake bukata a jarabawar ta bana wadda ake ganin sun yi yawa. A yayin taron manema labarai dan bayyana dalilin da yasa aka samu wannan tangarda, shugaban hukumar ta JAMB, Professor Ishaq Oloyede ya fashe da kuka. https://twitter.com/ARISEtv/status/1922676757787766804?t=LRtY04XWaym5mjx3aoC7Ug&s=19 Ya dai bayar da hakuri sannan kuma ya sha Alwashin sakewa dalibai da yawa jarabawar. Yankin da aka samu wannan matsaloli na jihar Legas ne da kudu maso kudu.
Kalli Bidiyo: Dangote na daya daga cikin wadanda suka gaisa da shugaban Amurka, Donald Trump a kasar Qatar

Kalli Bidiyo: Dangote na daya daga cikin wadanda suka gaisa da shugaban Amurka, Donald Trump a kasar Qatar

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote na daya daga cikin wadanda suka gaisa da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yin ziyarar da ya kai kasar Qatar. Shugaba Trump ya kao ziyara kasar Qatar bayan kammala ziyara a kasar Amurka. https://twitter.com/thecableng/status/1922724222867996726?t=ELlWm2kvK9sQIMxkMnfH5g&s=19 Kasar Qatar dai ta baiwa shugaba Trump kyautar jirgin sama Kirar Boeing.
DATTIJUWA TA SAUKE KUR’ANI: Allah Ya Sa A Amfana Da Abinda Aka Karanta Baaba!

DATTIJUWA TA SAUKE KUR’ANI: Allah Ya Sa A Amfana Da Abinda Aka Karanta Baaba!

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} DATTIJUWA TA SAUKE KUR'ANI: Allah Ya Sa A Amfana Da Abinda Aka Karanta Baaba!
Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci

Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci

Duk Labarai
Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci. Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dage ranar yanke hukunci kan shahararriyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, har zuwa ranar 20 ga watan Mayu, bayan da masu gabatar da kara su ka nemi izini don gyara tuhumar da a ke yi mata. Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa hukumar EFCC ce ta gurfanar da Murja da tuhuma daya tak kan zargin cin zarafin Naira. An ga Murja a wani faifen bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta tana watsar da kudi har Naira 400,000 tare da rawa a lokacin wani biki da aka gudanar a otal din Tahir Guest Palace a watan Disamba na shekarar 2024. Tuni dai wanda ake tuhumar ta amsa laifin da ake zarginta da shi. A zaman kotun na ranar Talata da aka tsara domin yanke hukunci, lauyan EFCC...
Ɗalibai 379,997 za su sake zana UTME ta bana bayan da JAMB ta tabbatar da an samu tangarɗar na’ura

Ɗalibai 379,997 za su sake zana UTME ta bana bayan da JAMB ta tabbatar da an samu tangarɗar na’ura

Duk Labarai
Ɗalibai 379,997 za su sake zana UTME ta bana bayan da JAMB ta tabbatar da an samu tangarɗar na'ura. Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta amince da kuskuren na'ura da ya kawo cikas ga sahihancin sakamakon jarabawar da aka yi ta bana a cibiyoyi 157 a fadin kasar nan. Shugaban hukumar ta JAMB, Ishaq Oloyede, yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Laraba, ya ce sakamakon ɗalibai 379,997 abin ya shafa. Ya ce hukumar ta gano matsalolin a cibiyar a Legas da Owerri, wanda hakan ya sa aka kasa dora amsoshin ɗaliban da abin ya shafa a kwanaki ukun farko na jarabawar. Oloyede ya ce ba gano matsalar da daya daga cikin kamfanonin da ke bada na'urar yin jarrabawar ya haifar ba kafin a fitar da sakamakon. Ya ce cibiyoyi 65 a Legas ɗalibai...
Mun shaida tsare-tsaren shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu na aiki yanda ya kamata, sun kawowa Najeriya ci gaba>>Inji Kasar Ingila

Mun shaida tsare-tsaren shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu na aiki yanda ya kamata, sun kawowa Najeriya ci gaba>>Inji Kasar Ingila

Duk Labarai
Gwamnatin Birtaniya ta ce matakan da shugaban Najeriya bola Ahmed Tinubu ke ɗauka a ɓangaren tattalin arzikin ƙasar kwalliya na biyan kuɗin sabulu. Birtaniyan ta ce matakan da aka ɗauka musamman wajen farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar, da na kuɗin shiga na daga cikin dalilan da suka aka samu ƙaruwar damar zuba jari a ƙasar. Jakadan Birtaniya a Najeriya Dr. Richard Montgomery ne ya sanar da hakan a yayin wani taro na aiwatar da shirin bunƙasa tattalin arzikin Najeirya da Birtaniya, ta fuskar kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen biyu, da ya gudana a Abuja babban birnin na Najeriya. Gwamnatin Birtaniyar ta ce la’akari da rahoton da Bankin Duniya a baya-bayan nan kan harkokin zuba jari a Najeriya ya nuna cewar darajar kuɗin ƙasar naira na farfaɗowa. Haka kuma rahoton ya ce ana sam...