Saturday, December 13
Shadow
Gwamnonin Arewa na taro kan matsalar tsaro a Kaduna

Gwamnonin Arewa na taro kan matsalar tsaro a Kaduna

Duk Labarai
Gwamnonin arewa da kuma sarakunan gargajiya na gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin. Taron wanda ke gudana a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, zai kuma tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al'amura da suke damun yankin. Gwamnonin jihohin Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da kuma Zamfara na cikin waɗanda ke halartar taron. A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli da Etsu na Nupe da Sarkin Zamfara da Sarkin Bauchi da Sarkin Ilorin da Sarkin Keffi da sauransu.
Haziƙin Matashi Ya Kammala Digirinsa Da Sakamako Mafi Kyau A Bangaren Kimiyya A Jami’ar Aliko Dangote Dake Wudil

Haziƙin Matashi Ya Kammala Digirinsa Da Sakamako Mafi Kyau A Bangaren Kimiyya A Jami’ar Aliko Dangote Dake Wudil

Duk Labarai
Haziƙin Matashi Ya Kammala Digirinsa Da Sakamako Mafi Kyau A Bangaren Kimiyya A Jami'ar Aliko Dangote Dake Wudil Muhammad Abubakar Ɗan Haya kenan dalibin da ya zama gwarzo a bangon karatu na shekarar 21/22, inda ya fita da sakamako mafi daraja a fannin kimiyya (Engineering) jami'ar Aliko Dangote dake Wudil. Abubakar ɗan Haya, ya fito daga ƙaramar hukumar Birnin-Kudu dake jihar Jigawa. Daga Abubakar Shehu Dokoki
Hajj 2025: Maniyyata fiye da 2000 sun tashi zuwa ƙasa mai tsarki

Hajj 2025: Maniyyata fiye da 2000 sun tashi zuwa ƙasa mai tsarki

Duk Labarai
Hukumar alhazan Najeriya ta ce ya zuwa ranar misalin ƙarfe 8:02 ta yi jigilar maniyyata 2,006 zuwa ƙasa mai tsarki. Hukumar ta bayyana a shafinta na X cewa jirgin MaxAir ya tashi daga birnin Bauchi zuwa Madina, inda ya kwashi maniyyata 384 da kuma jami'i guda ɗaya. Wannan dai shi ne cikamakin jirgi na biyar da suka yi jigilar maniyyatan daga ranar da aka ƙaddamar da jigilar wato ranar Juma'a.
Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne – Kwankwaso

Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne – Kwankwaso

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya soki ƴan siyasar da ke sauya sheƙa bayan sun gama cin moriyar jam'iyyar, abin da ya bayyana da babban kuskure a siyasance. Sanata Kwankwaso wanda ya bayyana hakan a Kano lokacin da yake karɓar wasu ƴan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa NNPP daga ƙaramar hukumar Takai, a gidansa da ke Miller road a birnin Kano. A baya-bayan nan ne dai raɗe-raɗi suka yi ta yawo cewa Kwankwason zai koma jam'iyya mai mulki ta APC. Rabi'u Kwankwaso ya ƙara jaddada irin juriya da haɗin kai da ke tafiyar Kwankwasiyya duk kuwa da cewa an ta ƙoƙarin ganin an kawar da hankalin mabiya.
Gwamnatin Borno ta haramta sayar da man fetur a Bama

Gwamnatin Borno ta haramta sayar da man fetur a Bama

Duk Labarai
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayar da umarnin haramta sayar da man fetur a karamar hukumar Bama na jihar, ciki har da garin Banki. Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne ayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta. Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani ɓangare ne na tsare-tsaren da gwamnatin jihar ke na daƙile ayyukan ƴan ta-da ƙayar baya. "Na bayar da umarnin haramta sayar da da man fetur a garuruwan Bama da Banki da kuma wasu sassa na karamar hukumar Bama nan take," in ji gwamna Zulum. Ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana saɓa umarnin zai fuskanci hukunci mai tsanani. "Babu wanda doka za ta kyale, sannan babu shafaffe...
An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin India da Pakistan

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin India da Pakistan

Duk Labarai
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Indiya da Pakistan sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta nan take. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce: "Bayan tattaunawa ta tsawon dare da Amurka ta shiga tsakani, ina farin cikin sanar da cewa Indiya da Pakistan sun amince da tsagaita wuta nan take. "Ina yi wa duka ƙasashen murna saboda amfani da hankali wajen amincewa da tsagaita wuta," in ji Trump.
Kalli Bidiyo: Gafarar Allah da Rahamarsa ba wasa bane: Sai ka aikata zunubi yace a rubuta maka lada, ko ka aikata zunubu ya mantar da mala’ikun ba zasu rubuta ba>>Sheikh Maqari

Kalli Bidiyo: Gafarar Allah da Rahamarsa ba wasa bane: Sai ka aikata zunubi yace a rubuta maka lada, ko ka aikata zunubu ya mantar da mala’ikun ba zasu rubuta ba>>Sheikh Maqari

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama Sheikh Ibrahim Maqari ya bayyana cewa, Rahamar Allah yawa gareta. Yace idan Allah yaso, sai mutum ya aikata Laifi a rubuta lada ko kuma ya aikata laifi a mantar da mala'ikun ba zasu rubuta zunubinba. Yace ko kuma idan mutum ya aikata Zunubi sai a aiko babbar gafara da zata shafe Zunubin da ya aikata. https://www.tiktok.com/@masoyinannabi509gmailcom/video/7502567487347739959?_t=ZM-8wF0fqcw2K7&_r=1 Da yawa sun yi Kabbarar Allahu Akbar.
Manyan Arewa kudi aka basu suka siyar daku shiyasa suke gayawa shugaban kasa, Arewa ba korafi, Subul da baka ne aka yi a Katsina maganar ta fito fili amma dama can haka suke gayawa shugaban kasa, saboda an biyasu, Inji Sheikh Nura Khalid

Manyan Arewa kudi aka basu suka siyar daku shiyasa suke gayawa shugaban kasa, Arewa ba korafi, Subul da baka ne aka yi a Katsina maganar ta fito fili amma dama can haka suke gayawa shugaban kasa, saboda an biyasu, Inji Sheikh Nura Khalid

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid wanda aka fi sani da Digital Imam ya bayyana cewa, Manyan Arewa kudi aka basu shiyasa basa iya fitowa su gayawa shugaban kasa gaskiya suke ce masa Arewa ba korafi. Kalmar Arewa ba Korafi ta fito ne daga jihar Katsina wadda ke fama da matsalar 'yan Bindiga a lokacin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai ziyara jihar, an ga wani babban allo dauke da kalmar Katsina ba Korafi. Lamarin ya jawo cece-kuce inda akai ta sukar musamman manyan masu mulki na Jihar, har sai da ta kai ga gwamnan jihar ya fito ya nesanta kansa da wannan allo. Saidai Sheikh Nura Khalid ya bayyana cewa, Subul da baka ne aa yi amma haka suke gayawa shugaban kasar.