Monday, December 15
Shadow
Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo

Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo

Duk Labarai
Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo. Rundunar ƴansandan jihar Imo ta rage wa wani ɗansanda mai muƙamin Sajan, Anayo Ekezie mukamin sa saboda cin zarafin wani dattijo. Wani faifan bidiyo na yadda wasu ƴansanda ke cin zarafin wani mutum a kan hanyar Owerri zuwa Aba ya bazu a kwanakin baya. Kakakin rundunar ƴansanda ta jihar, Henry Okoye, a jiya Laraba, ya tabbatar da cewa an gano ‘yansandan tare da tsare su. Ya ce an samu ƴansandan uku da lamarin ya shafa, inda ya kara da cewa an rage wa Ekezie mukami zuwa Kofur, yayin da aka ja wa sauran biyun kunne.
Shugaban Hukumar Alhazai (NAHCON) Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan tare da rakiyar wasu daga cikin manyan jami’an hukumar, sun sauƙa a filin jirgin sama na Port Harcourt domin shirin tashin jirgin farko na Alhazan bana da za a yi gobe a Owerri, fadar gwamnatin jihar Imo

Shugaban Hukumar Alhazai (NAHCON) Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan tare da rakiyar wasu daga cikin manyan jami’an hukumar, sun sauƙa a filin jirgin sama na Port Harcourt domin shirin tashin jirgin farko na Alhazan bana da za a yi gobe a Owerri, fadar gwamnatin jihar Imo. NAHCON Information.
Nan da shekarar 2045 zan rabar da gaba dayan kudina, ban so in mutu a matsayin me kudi>>Inji Me Kudin Duniya, Bill Gates

Nan da shekarar 2045 zan rabar da gaba dayan kudina, ban so in mutu a matsayin me kudi>>Inji Me Kudin Duniya, Bill Gates

Duk Labarai
Hamshakin me kudin Duniya, Bill Gates ya bayyana cewa, nan da shekaru 20, watau 2045 zai Rabar da gaba dayan kudinsa. Bill Gates ya bayyana hakane a shafin Gidauniyarsa ta Bill and Melinda Gates wadda suka kafa a shekarar 2000. Daga baya Wallen Buffet ya shiga tafiyar. Ya bayyana hakane yayin bikin cikar gidauniyar shekaru 25 da kafuwa. Hakanan a shekaru 25, Bill Gates ya bayar da Tallafin da ya kai na dalar Amurka Biliyan 100 kyauta. Yace nan da shekaru 20 din zai nunka yawan kudin da yake bayarwa tallafi har sai kudin sa sun kare gaba daya, bai bayyana cewa zai barwa 'ya'yansa ko sisi ba. Bill Gates wanda shine me kamfanin Microsoft yace zaftare tallafin da kasashe masu kudi suka yi wanda a baya suke baiwa kasashe matalauta abin damuwa ne. Yace baya so idan ya mutu a ri...
Nifa ba da son raina na dawo Najeriya ba, garkuwa dani aka yi>>Inji Nnamdi Kanu

Nifa ba da son raina na dawo Najeriya ba, garkuwa dani aka yi>>Inji Nnamdi Kanu

Duk Labarai
Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya bayyana cewa ba da son ransa ya dawo Najeriya, garkuwa dashi aka yi. Ya bayyana hakane a yayin zaman kotu dake sauraren kararsa. Yace kuma shi ya kafa kungiyar ESN ne dan su baiwa iyayensu dake shiga daji kariya ba dan su kaiwa kowa hari ba. Da aka tambayeshi game da hare-haren da aka kai kan jami'an tsaro da sauran hukumomin Gwamnati, Nnamdi Kanu yace bai san da wannan ba dan shi baya tayar da Fitina.
Bidiyo: Shugaba Tinubu ya isa jihar Anambra

Bidiyo: Shugaba Tinubu ya isa jihar Anambra

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa jihar Anambra inda yake ziyarar aiki a yau, Alhamis. Shugaban iya isa filin sauka da tashin jiragen sama na Chinua Achebe dake jihar inda ya samu tarbar gwamnan jihar, Charles Soludo da 'yan majalisar jihar da sauran dattawan jihar. Shugaba Tinubu kuma ya samu ya tsaya an masa taken Najeriya inda sojoji suka yi harbi sama dan girmamashi. Bayannan kuma, Shugaba Tinubu ya shiga motar da aka tanada dan shi tare da Gwamnan jihar inda zai zarce dan fara kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta gudanar.
Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Duk Labarai
Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Waɗanda suka sauya shekar sun haɗa da Honorable Salisu Yusuf Majigiri na mazaɓar Mashi/Dutsi, Honorable Aliyu Iliyasu na mazaɓar Batsari/Safana/Danmusa, Honorable Abdullahi Balarabe Dabai na mazaɓar Bakori/Danja. Dukkan su sun bayyana rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP a matsayin dalilin sauya shekar ta su.
Akpabio ya kai Sanata Natasha Akpoti kara kotu kan takardar Hakuri da shagube data yi masa, Yace yana son Kotu ta sa Natasha ta goge Wasikar a shafinta na sada zumunta sannan ta bashi Hakuri

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya maka Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a kotu, yana zargin ta da wallafa kalaman ɓatanci a cikin wata wasikar bada haƙuri da aka danganta da ita — Wasikar da ke ɗauke da wata magana mai cin mutunci da ke cewa “ta yi kuskuren tunanin cewa kujerarta a Majalisa ta samu ta hanyar zaɓe, ba ta hanyar jima’i ba.” Rahotanni sun bayyana cewa wannan ƙara ta samo asali ne daga wata wallafa da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda aka danganta da Sanata Natasha, inda ta nemi gafara daga Shugaban Majalisar bisa wasu maganganu da ake cewa ta furta a baya. A cikin wannan wasikar, an ambaci cewa ta “yi kuskuren ɗauka cewa ta samu kujera ne ta hanyar sahihin zaɓe.” Lauyoyin Akpabio sun ce wannan magana ta wallafa ra’ayi mai matuƙar cin mutunci da b...