Saturday, December 13
Shadow
Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna ‘Katsina babu ƙorafi’ ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa

Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna ‘Katsina babu ƙorafi’ ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa

Duk Labarai
Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna 'Katsina babu ƙorafi' ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa. Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa yace a matsayinsa na gwamna, bai da masaniya dangane da kafa wani allo da ke nuna cewa Al'ummar Jihar ba su da ƙorafi bisa ga salon Mulkin shugaba Tinubu ba. Hasalima Gwamnan yace, sun gabatar ma shugaba Tinubu ƙwararan ƙorafe-ƙorafe har guda 3 da ke buƙatar a magance masu, wanda suka haɗa da Matsalar tsaro, kammala wuta mai amfani da hasken Rana, da kuma fadada filin sauka da tashin jirage na Umar Musa Yar'adua da ke Katsina. Bayan haka ya ja hankalin masu suka da su riƙa tantance labarin da suka gani a kafafen sada zumunta domin tabbatar da asalin labarin, kafin sukar wanda baya da masaniya a kai. Daga Lukman Aliyu
Tashin Hankali: Wata Amarya ta yiwa Ango yankan rago a Kano kwana 9 da aurensu

Tashin Hankali: Wata Amarya ta yiwa Ango yankan rago a Kano kwana 9 da aurensu

Duk Labarai
Tashin Hankali: Wata Amarya ta yiwa Ango yankan rago a Kano kwana 9 da aurensu. Rahotannin da ke shigo wa Jaridar Arewa yanzu haka sun tabbatar da cewa ana zargin wata amarya da yiwa Angonta yankan rago a daren jiya Litinin, a jihar Kano. Lamarin ya faru a unguwar Farawa da ke cikin birnin Kano. Bayanai sun tabbatar da cewa Amaryar ta fara shayar da shi guba ne a Lemu, daga bisani ta yi masa yankan rago kamar yadda ta Dala FM ta ruwaito. Hakazalika wani rahoton ya ce an yi masu auren zumunci ne a ranar 27 ga watan Afrilu, wanda yau kimanin kwana 9 kenan. Zuwa yanzu jami'an tsaron yan sanda sun samu nasarar kama Amaryar domin bincike. Jaridar Arewa
Likitocin Abuja za su tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata

Likitocin Abuja za su tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata

Duk Labarai
Kungiyar ƙananan likitoci a Najeriya reshen Abuja babban birnin ƙasar ta sanar da fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga yau Talata, bayan korar ma’aikatan lafiya 127 da hukumar kula da ma’aikatan birnin na FCT ta yi. An yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan wani taron gaggawa da kungiyar likitocin ta gudanar a asibitin Asokoro ranar Litinin, kamar yadda kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito. Shugaban ƙungiyar likitocin, Dr. George Ebong, ya bayyana korar a matsayin maras tushe da kuma "rashin imani", yana mai buƙatar gaggauta dawo da ma’aikatan bakin aiki tare da biyansu albashin watan Afrilu. Dr. Ebong ya kuma buƙaci shugaban hukumar kula da ma’aikatan Abuja, Emeka Ezeh, da ya yi murabus daga mukaminsa. Ya yi gargaɗin cewa idan Ministan Abuja Nyesom Wi...
An gurfanar da wata mata Harira Muhammad a gaban babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Post Office a jihar Kano, bisa zargin ta da auren maza biyu a lokaci guda

An gurfanar da wata mata Harira Muhammad a gaban babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Post Office a jihar Kano, bisa zargin ta da auren maza biyu a lokaci guda

Duk Labarai
Ita dai Hariri ta kwashe tsawon watanni 6 basa zaune waje ɗaya da mijinta na farko Sagiru Shuaibu Tudun Murtala, sai dai ya ce ranar da ya ziyarci gidanta, ya tarar da ita kwance a gadonsu na aure da wani, lamarin da ya sa ya sanar da makwabta abin da ke faruwa. A lokacin da ta ke kare kanta game da zargin da mijinta na farko ya yi, Hariri ta musanta cewa akwai igiyar aure tsakaninta da shi, amma sai dai da alkalin kotun mai shari'a Khadi Munzali Tanko Soron-Dinki ya umarce ta data yi rantsuwa da Al-Qur'ani sai ta janye kalamanta. Shi kuwa a nasa ɓangaren, Bello Abdullahi Ƴankaba mijin Harira na biyu, ya shaida wa kotun cewa ya aureta ne a hannun kawunta Abdullahi Umar kan sadaki naira dubu ɗari. Bayan kammala jin dukkanin ɓangarorin, mai shari'a Khadi Munzali Tanko...
BABBAR MAGANA: Daga Kai Sadaki Shi Da Abokinsa Suka Aure Yaya Da Kanwa

BABBAR MAGANA: Daga Kai Sadaki Shi Da Abokinsa Suka Aure Yaya Da Kanwa

Duk Labarai
BABBAR MAGANA: Daga Kai Sadaki Shi Da Abokinsa Suka Aure Yaya Da Kanwa. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Daya daga cikin Angwayen, Umar Khalipha ne ya tabbatar da hakan.
Ana rade-radin an fara zartar da shari’ar Musulunci a jihohin Yarbawa inda har aka yankewa wannan mutumin hannu saboda sata, mutumin yayi karin bayani

Ana rade-radin an fara zartar da shari’ar Musulunci a jihohin Yarbawa inda har aka yankewa wannan mutumin hannu saboda sata, mutumin yayi karin bayani

Duk Labarai
A cikin kwanakinnan Hotunan wani mutum da guntulallen hannu ya bayyana a kafafen sadarwa inda ake ikirarin cewa an yanke masa hannu ne bisa laifin sata a jihar Kwara inda aka fara zartas da shari'ar Musulunci. Saidai a hirar mutumin me suna Lanlege Samuel Adewale da kafar yada labarai ta Leadership yace 'yan Bindiga masu garkuwa da mutanene suka masa wannan aika-aika. Yace daya daga cikin masu garkuwa da mutanenne ya kai masa sara a wuya shine ya kai hannunsa ya tare shin hannunsa na hagu ya fita. Ya bayyana hakanne bayaj da 'yansanda suka kubutar dashi da dan uwansa daga hannun masu garkuwa da mutanen. Da yake bayar da labarin yanda aka yi garkuwa dashi, yace ranar Lahadi suna tafiya akan mashin a Ogbe dake karamar hukumar Yagba West ta jihar Kogi sai 'yan Bindigar su ...
Neman Shawara: Kanwata ta ci Amanata inda ta Kwanta da Mijina, ya zanyi da ita?

Neman Shawara: Kanwata ta ci Amanata inda ta Kwanta da Mijina, ya zanyi da ita?

Duk Labarai
Wata mata me suna Akinyi Hellen na neman shawarar yanda zata yi da kanwarta uwa daya uba daya data kwanta da mijinta. Tace iyayensu tun suna yara suka rabu dan haka ta dauki kannenta dan ta rikesu. Tace ita ta saka kanwartata a makaranta har ta gama amma daga baya sai ta fara kwanciya da mijinta, tace ta tsani aure saboda tasan maza shedanune. Tace kanwartata kuma sai tambayar mijinta kudi tace akai-akai. Tace bata da wani wanda zata yi shawara dashi shiyasa ta wallafa a shafinta na Facebook take neman shawara.
Ban ga Amfanin Zumudin Hadakatar ‘yan Adawar da El-Rufai yake yi ba, kamata yayi a bar Shugaba Tinubu ya nutsu yawa ‘yan Najeriya aiki kar a raba masa hankali>>Inji Buba Galadima

Ban ga Amfanin Zumudin Hadakatar ‘yan Adawar da El-Rufai yake yi ba, kamata yayi a bar Shugaba Tinubu ya nutsu yawa ‘yan Najeriya aiki kar a raba masa hankali>>Inji Buba Galadima

Duk Labarai
Jigo a jam'iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, yayi wuri ace an fara hadakar 'yan Adawa dan zaben shekarar 2027. Galadima ya bayyana hakane a hirar da Jaridar Punchng suka yi dashi inda yace Zumudin El-Rufai yayi yawa, yace ko da yake ba dan siyasa ban shiyasa amma yasa ba inda zashi. Yace kamata yayi a bari shugaba Tinubu ya nutsu mayar da hankali wajan yiwa 'yan Najeriya aiki. Yace shi a yanzu ba zai ce komai akan mulkin Tinubu ba sai ya cika shekara biyu cif yana mulki kamin su duba suka yayi kokari ko akasin haka.
Duk wanda yace ban yi komai ba tun bayan hawa Mulkin Najeriya Makahone kuma Kurmane>>Shugaba Tinubu

Duk wanda yace ban yi komai ba tun bayan hawa Mulkin Najeriya Makahone kuma Kurmane>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, duk wanda ke ikirarin bai aikata komai ba bayan hawa mulki to Makahone kuma kurma ne. Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Daniel Bwala. Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a TVC News inda yace shugaba Tinubu ya kara yawan kudaden da Najeriya ke ajiye dasu a bankin Amurka inda kuma ya biya tarin bashin da tsohuwar gwamnatin da ya gada ta bar masa. Ya kara da cewa kuma Shugaba Tinubu ya kara yawan kudaden da yake aikawa jihohi, yace kamin zuwan Tinubu jihohi 27 sun Talauce basa iya biyan Albashi. Yace amma a yau babu jihar da ta Talauce ko ta kasa biyan Albashi. Yace ba biyan Albashi ba kadai yanzu Jihohi na gudanar da ayyukan ci gaba inda yace kwanannan suka je jihar Katsina, kuma Gwamnan jihar ya ...