Karanta Jadawalin sunayen Manya-Manyan ‘yan Adawar da suka hadu a waja taron jam’iyyar ADC ta su Atiku a jiya
A jiyane dai aka yi babban taro na hadakar 'yan adawa da suka bayyana jam'iyyar ADC a matsayin wadda zasu koma cikinta.
Ga jadawalin sunayen manyan 'yan Adawar da suka koma jam'iyyar ta ADC ko wanda suka halarci taron na jiya.
Akwai Atiku Abubakar; Peter Obi; Da Rauf Aregbesola.
Victor Umeh wanda shugaban jam'iyyar APGA ne sai tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Prince Uche Secondus, Mataimakin Peter Obi, Datti Baba-Ahmed.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC John Odigie-Oyegun, tsohon shugaban 'yansandan Najeriya, Mohammed Abubakar.
Tsaffin Gwamnoni a waja taron sun hada da Nasir El-Rufai (Kaduna), Rotimi Amaechi (Rivers), Gabriel Suswam (Benue), Abdulfattah Ahmed (Kwara), Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto), Oserheimen Osunbor (Edo), Celestine Omehia (Rivers), Liyel Imoke (Cross River), ...







