BA RABO DA GWANI BA: Yau Shekara 15 Da Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa Ummaru Musa Yar’adua
Daga Comr Nura Siniya
Shugaba ƙasa na farko mafi kwazo a mulkin farar hula da akayi a tarihin Najeriya mai tausayi mai ƙishin talaka mai tsantsini da dukiyar talaka da son ganin al'umma taci gaba.
Abinda ya ƙara bani sha'awa da marigayi Yar'adua shi ne lokacin da yake neman a zabe shi bai fito yayi ma ƴan Nijeriya alƙawuran ƙarya ba wanda yasan bazai iya cikawa ba. sai dai ya fito da tsarin 7-point Agenda ta yadda ya ƙudurci sauya fasalin Najeriya don ganin talaka ya samu sauƙin rayuwa da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa
'Yar'adua ya zo da manufofi masu kyawan gaske inda ya fara inganta albashin ma'aikatan gwamnati da albashin jami'an tsaro da ƙara inganta alawus na matasa masu ɓautar ƙasa NYSC da suka kammala karatun jami'a tare da kawo ƙarshen rikicin tsagerun yankin Naija Delta ta...








