Saturday, December 13
Shadow
Babu Abinda matasan Najeriya suka iya sai Korafi da zagin Shuwagabanni>>Inji Sanata Ireti Kingibe

Babu Abinda matasan Najeriya suka iya sai Korafi da zagin Shuwagabanni>>Inji Sanata Ireti Kingibe

Duk Labarai
Sanata Ireti Kingibe ta koka da cewa, Babu abinda matasan Najeriya suka iya sai korafi da zagin shuwagabannin. Tace idan aka yi abu wani lokacin sai matasan su ce zasu yi zanga-zanga amma basa iyawa. Tace wannan kasa taku ce, baku da wata kamarta, dan haka ya kamata ku tashi tsaye ku gyarata. Tace amma yawanci ko Talakawa sun je kusa da masu mulki, yawanci suna neman abinda zai amfanesu ba ba wanda zai amfani Al'umma ba.

Ƴan Sa Kai 11 Sun Ràsà Rayukansu a Sokoto Bayan Artabu da Ƴan Bìndìgà

Duk Labarai
Ƴan Sa Kai 11 Sun Rasa Rayukansu a Sokoto Bayan Artabu da Ƴan Bindiga ‎‎Aƙalla ‘yan sa-kai 11 ne aka tabbatar sun mutu, wasu da dama kuma ba'a san inda suke ba, bayan wani mummunan artabu da suka yi da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a karamar hukumar Tangaza da ke Jihar Sokoto.‎‎Rikicin ya fara ne tun ranar Juma’a, inda aka samu rahoton mutuwar mutane biyu, amma daga bisani aka ƙara gano gawawwaki tara a dajin Lakurawa. Har yanzu ana ci gaba da neman wasu da ba a san inda suke ba, tare da taimakon sojoji da jami’an tsaro daga Binji da Racca.‎‎Shaidun gani da ido sun bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan da ‘yan sa-kai suka hana wani hari a kauyen Magonho, lamarin da ya janyo musayar wuta mai tsanani.‎‎Ƴan bindigar, wadanda yawansu ya kai 40, sun zo ne akan babura guda 20 dauke da ma...
Yunwa da talauci, fatara, rashin tsaro sun addabi mutanen arewa Amma ana yunwa Tinubu Waka Yana anashuwa, Yana holewa. Babu Kimi. Akwai ranar kin dillanci>>Inji Mahadi Shehu

Yunwa da talauci, fatara, rashin tsaro sun addabi mutanen arewa Amma ana yunwa Tinubu Waka Yana anashuwa, Yana holewa. Babu Kimi. Akwai ranar kin dillanci>>Inji Mahadi Shehu

Duk Labarai
Yunwa da talauci, fatara, rashin tsaro sun addabi mutanen arewa Amma ana yunwa Tinubu Waka Yana anashuwa, Yana holewa. Babu Kimi. Akwai ranar kin dillanci. https://twitter.com/shehu_mahdi/status/1918965226831028383?t=QHuXUJuRhgcAO6N_1YVNTg&s=19 Da yawa dai sun bayyana takaici da mamaki irin na Mahadi Shehu.
Shekarar mu daya cur bamu ci nama ko kifi ba, babu abinci me gida jiki babu kulawar Lafiya>>Inji Masu Laifi dake daure a gidan gyara hali

Shekarar mu daya cur bamu ci nama ko kifi ba, babu abinci me gida jiki babu kulawar Lafiya>>Inji Masu Laifi dake daure a gidan gyara hali

Duk Labarai
Masu Laifi dake daure a gidan gyara hali na garin Jos a jihar Filato sun koka da cewa, yanayin da suke ciki ya munana. A wani rahoto da kafar Sahara reporters ta wallafa, mai laifin sunce shekara daya kenan rabonsu da cin nama ko kifi, sai wake wanda babu wani abun gina jiki a cikinsa. Hakanan sun koka da cewa, idan basu da lafiya babu kulawa kuma ana azabtar dashi ga nuna kabilanci. A wani hoto da aka wallafa, an ga kalar abincin da ake baiwa masu laifin wanda ya hada da wake da garin rogo da miyar Kuka.
Gwamnatin Tarayya ta sha Alwashin kammala aikin gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi nan da shekarar 2026

Gwamnatin Tarayya ta sha Alwashin kammala aikin gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi nan da shekarar 2026

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana aniyar gwamnatinsa na kammala gina titin jirgin kasa daga Kano, zuwa Jigawa zuwa Katsina zuwa Maradi. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya bayyana haka a yayin da ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar ta Katsina da gwamnatin Jihar ta aiwatar. Shugaban kasar yace idan aka kammala wannan aiki zai taimaka wajan saukaka tafiyar mutane da safarar kaya wanda yace hakan zai rage amfani da Titi. Hakanan shugaban kasar yace sun bayar da aikin gyaran titunan da suka hada Marabar Kankara -Dutsinma -Katsina da kuma wadanda suka hada garuruwan Zaria -Hunkuyi -Dabai da kuma wadanda suka hada garuruwan. Hakanan shugaban kasar yace suna aiki akan titin Kano zuwa Katsina.
Kalli Bidiyo yayin da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ke tambayar Anya Baffa Bichi na da hankali kuwa kan maganar da yayi ta cewa ana baiwa Kwankwaso Biliyan biyu

Kalli Bidiyo yayin da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ke tambayar Anya Baffa Bichi na da hankali kuwa kan maganar da yayi ta cewa ana baiwa Kwankwaso Biliyan biyu

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Anya Baffa Bichi na da hankali kuwa? Yayi wannan tambayar ne game da ikirarin Baffa na cewa ana turawa Kwankwaso Naira Biliyan 2 duk wata. https://twitter.com/HonAbdullahiM12/status/1919049059119014034?t=cOh5tIQ0hOwP_0-gIyNDoQ&s=19 Wannan magana dai ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sadarwa
Da Duminsa: Shugaba Tinubu zai gana da kamfanonin wutar Lantarki dan magance matsalar bashin da kamfanonin wutar ke bi

Da Duminsa: Shugaba Tinubu zai gana da kamfanonin wutar Lantarki dan magance matsalar bashin da kamfanonin wutar ke bi

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gana da kamfanonin wutar lantarki dan magance matsalar bashin da kamfanonin wutar ke bi. Ana sa ran Shugaban zai gana da kamfanonin ne inda za'a biya wani sashe na bashin da suke bi sannan sauran bashin za'a biyashi a hankali nan da watanni 6. Hakan na zuwane bayan ganawar kamfanonin wutar da ministan wuta, Adebayo Adelabu. Me magana da yawun Ministan, Bolaji Tunji ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan a wata sanarwa da ya fitar. Kamfanonin wutar na fuskantar matsalar karancin kudi wanda kuma suke bin bashin Naira Tiriliyan 4.
Kalli Bidiyo:Yanda wani Dan kasada ya tsallaka Titi yayin da tawagar motocin shugaba Tinubu ke wucewa

Kalli Bidiyo:Yanda wani Dan kasada ya tsallaka Titi yayin da tawagar motocin shugaba Tinubu ke wucewa

Duk Labarai
Wannan wani dan kasada ne da ya baiwa mutane mamaki inda aka ganshi yana tsallaka Titi yayin da tawagar motocin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke wucewa. Lamarin ya baiwa mutane mamaki inda akai ta masa Allah wadai. https://twitter.com/abdullahayofel/status/1918913317881491890?t=Wca6Hk9N0w2YDDllnbS4lA&s=19 Wasu dai sun ce kamar baya son rayuwarsa ne.
Wani ɗan asalin jihar kano, mazaunin Faransa ya kafa sabon tarihi a fannin kimiyya

Wani ɗan asalin jihar kano, mazaunin Faransa ya kafa sabon tarihi a fannin kimiyya

Duk Labarai
Wani ɗan asalin jihar kano, mazaunin Faransa ya kafa sabon tarihi a fannin kimiyya. Dr. Mubark Mahmud PhD, mai bincike kan muhalli ya ƙirƙiri sabuwar hanyar auna tsawon bishiya wanda duniyar kimiyya ta karba ta kuma raɗa wa binciken suna "Mahmud Method". An saka a manhajar M-Tree da jami'o'i a Faransa ke amfani da ita wajen auna tsayi da kauri na bishiyoyi. Tuni dai aka ƙaddamar a jami'ar da ya ke karatu, université Paris-Saclay a ranar 30 ga watan Afrilu. Tuni dai aka wallafa wannan bincike a wata mujallar noma mai suna Smart Agricultural Technology Kuma za a saka shi a manhajojin koyarwa a makarantu da cibiyoyi da dama. Hakazalika an baiyana cewa akwai shirin za a bunƙasa binciken ta hanyar saka shi a ƙirkirarriyar fasaha wato Artificial Intelligence, AI.